← Book details Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 169 OF 172

Sashe 169

Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ita ma kan ta daga masa tana cigaba da kuka da yaki ya tsaya mata. Sai da Sirleem ya tabbatar ta daina kukan sannan ya tashi ya basu guri sun yu maganganu da yawa masu taba zuciya da tuna baya, Falmata tana fadar yadda Mama take yawan maganarsa. A gidan ya ci abincin tare da Sirleem da Falmata abincin da kanwasar Falmata ta girka, duk da kasancewar baya cikin walwala saboda abun da ya faru sai dai kana ganin fuskarsa kasan yana cike da son yar'uwarsa ko'ina tai binta yake da kallo irin na kauna da mamakin yadda ta zama jininsa lokaci daya, sai a yanzu yake ganin yanayinta yana yin kama da na Mamarsa.

***
Rayuwa da ciki a gurin mace ba abu ne mai sauki ba, musamman cikin fari kuma ga mai kananan shekaru kamar Falmata, sai dai kasancewar mai juriya da hakuri ya bata damar iya daukar nauyin cikinta cikin ma Sirleem yana hana ta yin abubuwa da dama gudun kar ta wahala, domin har ya fita kula da rawar kafa dan abu kadan zai yace zata gajiyar masa da baby ko tana son ta ja masa babynsa ya wahala. Sai da tai da gaske sannan ya barta ta tafi bikin kawarta Khadija domin ko fita baya son tana yi wai ciki ya tsofa tana ta wahalar da abun ke cikin, idan ya fita komai ya gani sai ya siyo mata idan kuma yana gida kullum tana jikinsa shi kuma hannunsa ko kansa na kan cikinta, har mamakin yadda yake ta zumudin cikin take wata kila. Saboda be taba yi ba ko kuma saboda an kawo gunsa ne, domin wani rawar kafar dai bata taba gani ko jin irinsa ba sai da aka kawo gunsa, haka dai akai ta fama Allah ya kai ta shiga watan haihuwarta, a nan ta gane ashe abun ba sauki sai ga wanda Allah ya kawo wa, asibiti ta haihu tana dakin haihuwa tana nakuda Sirleem ya waje cikinsa na murdawa kamar shi zai haihuwa daman tun kamin nakuda ta kama ta ya fara nashi zazzabin da ciwon kai.
  Sai yamma ta haihuwa cikin nasarar Allah, take Sirleem ya fadi yai ma Allah sujuda yai godiya. Kamin dare hotunan baby sun cika Media kasancewar mijinta sanannen mutum ne.

FADIME POV.

Zuwa tai ta tsaya gabansa ta mika masa hannu.

“Miko min kofin can�

Ya dauke kai daga laptop din dake gabansa ya kalleta.

“Shi kofin?�

Ta turo baki gaba.

“Eh�

Sai yai murmushi ya kai hannu ya dauka ya mika mata, haka take masa ita ala dole tana da ciki ba zata duka ba, musamman idan ta san yana cikin gidan ko wanka za tai sai dai ta rage tsawo a hankali har ta kai kasa saboda cikinta kamar wata mai tsohon ciki, babu ranar da bata bude cikin tai ta kallo tana shafawa, har tana cewa wai bata ji motsinsa ba wai ko ba shi da lafiya ne ko kuma dan tana yawan cin abinci mai yawa ne, hakan yasa ta rage cin abinci mai nauyi kuma da yawa wai kar ta cutar da ciki, wani abun idan tana yi Shattima sai yai ta dariyarta yana mamakin yadda take wauta sosai. Ya fada ciki sai ya kai wata hudu yake fara motsi amman bata yarda ba, kullum sai ta masa complain.
Haka akai ta shan rainon cikin kamar akanta aka fara ciki a duniya ko numfashi ba ta yi da karfi, sai dai duk abun da take tana yi idan tana ita kadai ko kuma ita da Shattima, bata yi a gaban mutane musamman idan suka leka masarauta hakan yasa Shattima ya gane shagwabar har da shi ake yi ma. Daman kuma shi dan nema ne domin shi ya fara nuna mata tun farko ita kuma sai ta samu guri, haka zata tashe shi cikin dare ta ce zata ci abu, idan be nemo mata ba sai kuka kamar karamar yarinya, wani lokacin lallabata yake da sunan zai nemo mata sai ya samu tai shiru har bachi ya dauke ta, wani lokacin kuma fitowa yake da sunan zai fita ya nemo mata sai ya dawo falo ko dakinsa ya zauna sai ta yi bachi sannan ya koma ciki.
Ba ma kamar da cikin ya tsofa a lokacin ne yake son ta motsa jikin sai ta tsaya kai ta fata ta ce ba zata yi komai ba, sai fadar take cikin ya mata nauyi wani lokacin idan ta shiga bandaki fitsarin ma a tsaye take sakinsa, sai dai ta saka ruwa, domin idan ta duka zata ji kamar cikin zai fito mata ko kuma ta gagara tashi, hakan kuma baya hana ta fita cikin mutane da cikin saboda shegen son yawo, idan yace zai hana ta wata rigimar ce zai takalowa kansa. Yau ma ta kama weekend Shattima na gida amman hakan be hana ta shiryawa da sunan zuwa Walimar wata cousin dinsa da ake ba. Yana zaune falo ta sauko da shirinta karfin hali har su jaka. Shi dai kallonta kawai yake har ta sauko.

“Da gaske zuwa zaki yi?�

“Eh ni dai ina son zuwa�

Ta fada tana dan turo baki gaba, so kawai take yace mata ba zata je ba ta fara masa kuka tana cewa ba zata ji abinci ba saboda ta san yadda yake shiga damuwa idan bata ci ba. Murmushi yai ya mike tsaye ya nufi dakinsa, be dade ba ya fito ya shiga dakinta ya sauko inda take tsaye tana jiransa ya cire gyalen dake jikinta ya mika mata Hijab.

“Ki saka wannan zaki fi rufe jikinki�

“Ni nauyi yake min�

“Daure ki saka haka nan haba baby na dan Allah�

Ba dan ta so ba ta saka Hijab din sannan ya aje gyalen akan kujera ya rika hannunta suka fita daga falon, ya riga isa gurin motar ya bude mata ta shiga ta zauna sannan ya zagaya mazauninsa yai ma motar key.

“Allah ya taimake ni karki min raki gurin haihuwa�

“Wallahi sai na yi haka kawai waya ce kai ciki waya ce? Mutum cikin mutum kuma zai fito a ciki mutum ace ba zai yi raki ba? Lallai fa�

Yayi dariya.

“Kina da gaskiya fa, mutum cikin mutum ko?�

“Eh mana, kuma ni zan sake haihuwa ba ma daga wannan idan na haihu yar mace mai kyau�

“Kamar ni?�

Ta yi dariya.

“Ke da kika ce twins kike so? Ai mutum biyu ne zai fito a jikinki yarinya�

“Ni dai da na ji wani abu ka kaini asibiti�

“Aa asibiti? Ga asibiti a gida? Wa zai kula da ke kamar mijinki?�

“Ai kai ta yaranka za kai�

Ya kai hannu ya taba kumatunta.

“Kamin na ga yaran waye na fara gani?�

Ta mika masa bakinta sai ya maso da nasa tai masa kiss.

“Ni ka fara gani�

“I love you�

Ya dora hannunsa a kan katon cikinta yana murmushi.

“Kin san dai kina saurin jin yunwa ko? Ki daina zama baki ci ba yunwa tana damunki�

“To zo ka bude min�

Ya fita daga side dinsa ya zagaya dayan side din ya bude mata ta fito sannan ya rufe ya fita da kallo har ta shige cikin falon shi kuma ya shigo motarsa ya dawo gida, bayan yayi sallah azahar ya kwanta be farka ba sai 4 shi ma alarm din wayarsa ne ya vmuslim app ya farkar da shi,  bathroom ya shiga yai alwala ya fito ya sauko yana hamma ga mamakinsa sai ya ganta zaune saman kujera tana kallon plasma dake falon.

“Hajiya yaushe kika dawo?�

Juyowa tai ta kalleshi da idanuwanta da suka mata ja tsabar kuka.

“Tun dazun, kaje kana ta bachi wai ni kuma ina ta daukar nauyi, kai ba ruwanka tun da ba a jikinka ne ba�

Zaunawa yai kusa da ita, ya san kullum abun kuka take nema, but abun mamakin kar dai ace dan yana bachi take kuka, ya hana ta bachin ne ita?

“Shi ne kike kuka?�

“Eh mana, kuma mutane sai cewa suke a a ashe ciki ya tsufa mai ciki mai ciki suna ta ce min haka....�

Ta kara fashewa da kuka domin a yanzu babu abun da ta tsana kamar ace mata mai ciki, daman tana ta daurewa a can amman a gida dole ne tai kuka saboda abun ya mata ciwo, gashi kuma tana zuwa ta tararda Shattima yana bachi abun shi. At first dariya ce ta zo masa sai yai saurin gintseta ya ja jikinsa ya rumgume.

“Na san kina fama da abu, shiyasa na ce ki daina shiga mutane amman kin ki, da kina nan ai ni ma ba zan fara yi bachi ba, balle har su rika ce miki Mai ciki Mai ciki Mai ciki Mai ciki... �

Dagowa tai ta kalleshi.

“Cewa kake yi kai ma?�

“Aa ni ai ba zan fara ba, ina fadar yadda suke fada ne, Allah ya ba ni hakuri?�

“Ya baka?�

“Ya baki�

Yayi saurin gyarawa yana maidata kirjinsa sai dariya yake amman yaki bari ta gani.

“Fada min waya kawo ki?�

“Direban gidan�

“Ya kyauta, tashi ki yi sallah ni zan tafi masallaci�

“To�

Ta daga jikinsa shi kuma ya mike tsaye yana sumbantarta.

“Se na dawo�
Chapter 169 · 0% Book details