← Book details Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 172

Sashe 4

Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wata babbar kofa ya nufa mai kyau da kyalle kamar an am mata ado da zinari, ya kai farin hannunsa ya tura kofar ya shiga, sai ya tsinci kansa a wani matsakaicin corridor mai kama da karamin falo an cika ko'ina da na gurin da manyan fulawoyin na kasko da jan carpet.
Mikewa yai straight zuwa katon stairs din da ke gabansa, gabansa kawai yake kallo har ya haye sama, kofar farko ya fara turawa tun kan ta karasa budewa ya jiyo kukan dansa, hakan yasa shi hanzarin cira kafa ya shiga cikin falon mai kama da da wata karamar fadar turawa, a wannan falon kam komai na cikinsa blue ne idan ka cire farin fentin mai kawata ko'ina na gidan, ta bangare daya kuma wani gini ne akai a cikin gurin mai kamar swimming pool sai dai wannan anyi shi da dan yi tsayi, an masa kwalliya da kwaryar da kuma rudayi sai dawusu a samansu yana furzo ruwa gwanin sha'awa, a iya cikin gilashin ruwan ke tsawa ko kadan basa digowa kasa balle har su sauka.
  Falo ne mai dauke da set din kujeru uku kujerun farko kanana ne an jerasu kamar kujerun dinning wato a zagaye, sai dan karamin tebur a tsakiya da kuma wani karamin carpet blue, na biyun su kuma manyan turkish ne masu daukar hankali, sai  wasu daga can karshen falon su ma blue kamar dai sauran an zagaye gefen da su, su ma kuma suna da karamin carpet da center table.
A gaban falon kuma wani katon kirsten tv stand ne fari mai gloss fronts da haske blue, left and right na tv stand din matsakaicin show glass ne mai haske a ciki blue color an masa kwaliya da turaruka na alfarma masu kyau da tsada gwanin burgewa.
Ga wani katon plasma da aka kawata tv stand da shi kamar matanen ciki za su fito waje.
A dayan gefen kuma wani karamin madubi ne na aka manna mai dauke da gurin wanke hannu, yamma da falon kuma matattarar cin abinci ce mai zamam kanta wacce aka ware mata kofarta dabam kusa da wani katon freezer mai kofa biyu, a dinning area din ma akwai madaidaicin plasma wanda zai bawa duk wanda yake zaune a dinning din damar kallo.
Kofar da Umar ya shigo ce kawai gini a cikin falon sauran duka glass ne gwanin burgewa.
  A dayan bangaren kusa da dinning akwai wata karamar kofar glass, shiga cikinta na sadarda mutum da wani kebantaccen guri mai dauke da set din karamin dinning har biyar an rarrabasu an jera ko wane set dabam da wani.

Ta backyard din mutum zai iya hango wanda ke tafe da kuma abunda ke gudana a harabar Masarautar sai dai ba zai bawa mutum damar hango bangaren mai Martaba ba, dama da shi kuma wanda ke tsaye a gurin zai iya hangon garden din dake bangaren Momy, shi ma kuma ganin mai shiga ko mai fitowa ne kawai mutum ke da damar yi ba wai komai da komai na cikin ba kasancewar garden din na da manyan itatuwa da katon Swimming pool a gafe na dutse.....

Nana na ganinsa ta mike tsaye rike da Labib da tana jijjigashi ta nufi gurinsa. Cike da kulawa da tausayi da kuma kaunar dansa ya sa hannu biyu ya karbe sa.

“What happened?�

“Ba wanda zai fada maka ga abunda ya faru fa, ina dakin kawai yai kyalowa�

“No karya kike na fada muku a daina barinsu su kadai�

Bata sake unkurin cewa komai ba ta koma ta zauna tana kallonsa.
A kafadarsa ya dorashi yana jijjigashi tare da karanta masa ayatul kursiyu ya tofa masa sannan ya nufi hanyar dake kusa da dinning da kansa ya bude kofar ya shiga, yana shafa bayan Labib a hankali yana kallon abunda ke gudana a kasa.

Ta kofar farko Hajiya Karama ya fito ta nufo inda yake tsaye.

“Har ka iso, ya jikin na shi?�

“Da sauki�

Ya amsa mata domin ya daina kukan da yake.

“Me ke damunshi�

“Ban sani ba�

“Kawo shi�

Ta karbe shi tana jijjigashi cike da kulawa domin ita ma kanta tana kaunar yaran.

“Nana tace kyallowa yai, na fada musu a daina bar min yara su kadai, if not zan dauke su daga gidan nan�

Ya fada yana juyawa ya kalli wata harabar dabam kana ya aje numfashin da sautin da ke nuna ba da wasa yake ba, biyoshi tai tana girgiza kai.

“Nono Ammy ba zata jidadi ba, am samu mai kula da dakinsu fa, na ce a barta ta kula da su Iya tace bata yarda da ita ba�

“Wacece?�

Ya juyo yana tambaya.

“Wata ce ba zata wuce 16-17 years ba�

“Miyasa ba ta yarda da ita ba?�

“I don't know ko maybe saboda ta yi kankanta ne�

Kare mata kallo yai ya dauke kai

“Ji dress dinki, na sha fada miki ki daina irin shigar nan�

Ya karasa yana takawa a hankali zuwa gurin karfen dake gabansa. Sai ta kalli jikinta.

“What's wrong with my dress?�

Be amsa ta ba ya juya ya fice daga gurin ya barta rike da Labib din a kafadarta.
Murmushi tai tana kara kallon kanta, dogon wando ne da wata riga mai guntun hannu wacce ta tsaya iya kwankwasonta, ba laifi kayan sun matse ta sai dai ba irin matsuwa can can sosai ba, a gurinta hakan normal ne ko ba komai tana jindadin yadda hankalin maza yake tashi idan sun yi arba da irin halittar da Allah yai mata, hakan na mata dadi sosai wai sai dai a gani a hade yawu babu yadda za'ayi da ita.
Bin bayansa tai ta kofar da ya shiga tana cigaba da murmushi, a kujerar da ke kusa da kofar ta zauna ta sa dayan hannunta tana gyara yar karamar jar hular da ke kanta.

“Yayi shiru?�

Nana ta tambaya tana nufo inda Zainab din take zaune.

“Yeah i think yayi bachi�

Ta taba jikinsa sai ta ji shi da dan zafi za tai magana Zainab ta mike tsaye tana kallon Doc Deen wanda ya shigo rike da dan karamin akwatin magani, fuskarsa sanye da farin gilashi.

“Sannu da zuwa Doctor�

“Hajiya Karama�

Ya amsa mata yana murmushi tare da kallon Shattima wanda ke tsaye jikin window ya rumgume hannayensa ta baya yana kallon harabar gidan.
Har Doc ya zauna Zainab ta mika masa Labib ya fara duba shi Shattima be juyo ba.

“Miya same shi?�

“Ba komai haka kawai yai ihu�

Nana ta amsa shi tana zaunawa kusa da Doc kamar ita ce zata duba yaron, Doc Deen yayi murmushi yana kallonta.

“Ko na baki ki duba shi?�

Dariya tai mai sauti ta make kafada tana girgiza masa kai. Zainab ta yi murmushi ta nufi gurin da Shattima yake tsaye ta tsaya ta jera tare da shi tana kallon dokin da yake kallo wanda ake yi wa ado irin na sarakuna.

“Yaushe ka dawo?�

“Jiya....�

Ya amsa mata a takaice duk kuwa da kasancewar yana a cikin yanayin da baya son magana, amman ba zai iya kin amsa ta ba, babu abunda Zainab zata bukata ya kasa mata, bayan girman da tai a kusa da shi ta bude ido, kusan ta fi shakuwa da shi fiye da kowa, tana jin maganarsa kamar yadda shi ma yake saurarenta yana girmamata a ciki har da sunan mahaifiyarsa da ta ci, wanda hakan yasa ake mata lakabi da Hajiya Karama, gashi tana da sirri idan ya fada mata A babu mai ji sai idan shi ya umarce ta data fada, babu abunda za tai ba da saninsa ba, babu abunda take boye masa ita da shi abokai ne kuma shakikai.

“Wannan shi ne karo na biyu da ka sauka wani guri ba Masarautar nan ba, and i don't think hakan zai mana dadi�

A hankali ya busar da iskar bakinsa ya zuba hannyensa aljihu yana cigaba da kallon dokin ta cikin gilashin falon ya ce.

“Abubuwan gidan nan basa min dadi�

“Yeah amman some time muna bukatar shawararka, ko bukatar wani abu kusan kai ne Sarki a gidanan tun da Mai Martaba bashi da Lafiya, be kamata ace kana nisa da gida ba, and the way you act Ammy ba zata jidadi ba�

Murmushin gafen baki yai ya kalleta.

“Zan gyara Hajiya Karama�

“Good�

Ta fada with smile on her face, sannan ita ma ta saka hannunta aljihu tana wasa da dayar kafarta, shiru ne ya biyo baya kamin ta kalleshi

“This time around ina son nai wani abun da zai bawa kowa mamaki as a photographer i want to do something differently like..... �

Sai kuma ta kasa karasawa ta ware hannayenta kamar mai tunanin abunda zata fada. Kallonta yai kadan ya dauke kai.

“Well i think ki shiga kauye, ki duba wata culture ko yare ki duba wasu addinai na wasu da suke wanda ya sha banban da wanda ake gani sai ki dauka�

Ta wara idonta tana murmushin jindadi.

“Wow shiyasa bana son kai nisa da ni, a duk lokacin da na nemi shawara sai ka sama min mafita�

Murmushi yai mata kamin ya juyo da sauri jin muryar Muhseen.

“Wow wow wow..... Longest time Dude�

Tsakanin shi da Muhseen aka rasa wanda ya fi wani sauri, a tsakiyar falon suka hadu suka rumgume junansu ko wanensu fuskarsa dauke da dariya da farincikin arba da dan'uwansa.
Nana ta taso da sauri ta rumgume Muhseen.

“Ya Muhseen oyoyo�

“Hey Little One�

Zainab ma side hug tai masa tana welcoming dinsa, sai da ya kai wa Doc Yazeed hannu suka gaisa sannan ya zauna kusa da Zainab.

“Hajiya Karama how far?�

“Fine ya Abuja?�

“Kalau�

“Ina Aliyu and Mama Fulani?�

“Yana nan kalau Mama kuma tana kasa tare da Mai Martaba�

Shattima ya karbi Labib dake bachi a hannun Doc Deen yana fadin.

“Doc me ke sa su yawan zaburar nan ne wai?�

“To Wallahi ba zan iya fada ba, adai rika yi ana hada musu da addu'a especially idan za su kwanta bachi ko idan sun farka, and a daina barinsu a duhu ko barinsu su kadai�

Yana fadar hakan ya mike tsaye ya rufe akwatinsa yana musu sallama, sai Nana ta mike tsaye ta bi bayansa suka fita falon tare, yana saukowa stairs din ta ce.
Chapter 4 · 0% Book details