← Book details Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 121 OF 172

Sashe 121

Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ammy kenan, ai Shattima ko be auri Maijidda ba, dole zai auri wata, na zaba masa Maijidda ne saboda na san a halin da ake yanzu yana wahala ace ga wanda yake so, kuma Inshallah babu fashi duk wani shirye shirye da ya kamata na fara shi, kuma yau zan yi magana da mahaifiyarta Inshallah�

Shattima yayi shiru yana saurari kamin ya dago kai da zimmar yin magana sai Ammy ta hana shi da ido, hakan yasa shi yin shiru har sai da Baba Waziri yai ma Ammy sallama ya fita, sannna Ammy ta kalli Shattima cikin damuwa ta ce.

“Abun da kake be kamata ba, na san ba lallai ne ace kana son Maijidda ba, amman ko dan darajar Waziri da irin yadda yake maka tsaye a komai ya kamata ace ka amince, idan tsoro a ranka ka cireshi, indai har da gaske iya ce take cinye maka mata, zan tabbatar kuma zan yi magana da Hajiya Talatu da kaina�

“Ki yi magana da ita kuma? To ai za ki jefa rayuwar Fadime ne a hadari, aa gaskiya kar a cutar da ita, tana fama da makanta a kara mata wani�

“Sai na fada maka zuwa zan yi na fada mata cewar wata ce ta zo ta fada min? Kamar baka san wacece ni ba? Kowa ya ji haka a ba zai dauki abun da gaske ba�

“No Ammy bana son yarinyar ta shiga matsala, karki yi magana da Hajiya Talatu, ni nasan abun da zan yi�

Yana fadar hakan ya tashi cikin rashin jindadi, ya fice daga daki. Ammy da bishi da kallo har ya fice sannan ta dauki wayarta ta kira jekadiya.

“Ki shigo ina nemanki�

Ta aje wayar ba tare da ta jira abun da Jekadiyar zata fada ba. Cikin yan dakiku Jekadiya ta shigo dakin da saurin ta bayan ta yi knocking Ammy ta mata izinin shiga.

“Ranki ya dade gani�

“Jekadiya ina son ki samo min hantiti, da tsakin kuka, sai bushenshen kashi, ki hade su guri daya, idan an samu ki fada min, sai na aika kiran Iya, idan zata shigo nake son ki turara shi a falo�

“To ranki ya dade za a nemo da yarda Allah�

Ammy ta dauko 3k ta mika mata, duk da ta san hantitin ne kawai abun da zta nemo domin tsakin kuka bushesshe da ƙashi ba abu ne mai wahalar samu ba.

SIRLEEM POV.

Shi ya fara shiga yai alwala ya fito sannan ya rika hannunta ya shiga ta ita bandakin, kusan rabin alwalar duk shi yai mata sannan ya sakota gaba suka fito da kansa ya shimfida katuwar carpet ya shiga gaba ita kuma ta tsaya daga baya tana yafe da mayafin da aka kawo ta da shi ta kabbarta tana binsa a baya, raka'a biyu yai ya sallame sannnan ya dora da addu'a kana ya juyo ya kama kanta ya karanta addu'a, sai ya ji wani irin natsuwa da nishadi yana sauko masa, duk da kasancewar yana a halin da shi kansa ya san ba son Falmata yake ba, sai dai yana tausayinta kuma kuma yana jin idan har ya aurenta yayi dacen mace mai hakuri da tarbiya kuma zai taimaki rayuwarta.

Sai ya ji wani girma da dattijanta ta kama shi, look at him wai shi ne mai aure a yanzu kuma matarsa ce a gabansa abu kamar a mafarki. Naman da ya siyo ya dauko ya aje gabanta ya fara cira yana kai mata a karamin bakinta, sai ta kasa karba saboda kunya da nauyinsa da ya kamata, tashi yai ya koma kusa da ita ya zauna ya jata kusa da shi sosai ya kwantar da kanta a kirjinsa, sannan ya kai mata naman a baki, a hankali take taunawa tana jin wani irin kunyarsa ya cika mata ido, bata wani ci da yawa ba tace masa ta koshi, sai ya zuba lemun ya bata ta sha shi ma kadan, sannan ya hada komai ya maida gefe.

“Teema...�

“Na'am�

Ta amsa ba tare da ta kalleshi ba, hannunsa ya kai ya kama hannunta ya soma mata magana a natse.

“Na san kin saba da kalubalen rayuwa, kin saba shiga abubuwa kala kala, ina son ki san rayuwar yanzu da kika shiga da ta baya ba daya ba ne, ada can ke budurwa ce yanzu kuma matar aure, matar auren ma matar Sirleem, mutumen da ya aureki a boye, na fada miki wannan ne saboda kin san cewa akwai kalubale a gareki nan gaba, ban ce zaki shiga wani tasku na rayuwa ba, amman na san kamin ki sha da dadi a gurin Hajiya zai kin fara karbar azaba, so ina son ki daure saboda mahaifiyata ce, ni kaina a yanzu ta hana yin waka, ba abu ne mai sauki a gareni ba, amman a haka na tattara komai na aje, saboda na bi umarninta, na san idan ta sani ranta zai bace sosai, shiya saka ko dangin mahaifina ban labartawa ko wa ba, domin na san maganar zata koma a kunnenta, saboda akwai shakuwa da fahimtar juna a tsakaninsu dole za a samu wanda zai labarta mata, ba daga Hajiya kadai ba har dangin mahaifina na san ba lallai ne su karbe ki da wuri ba, kuma ba lallai ne su nuna miki so kamar sauran matan yan'uwa ba, saboda banbanci matsayi da kuma yanayin yadda na auro ki, ina son ki saka a zuciyarki cewar kina da kima da daraja mai yawa a gurin mijinki, kuma duk wani abu da zai bata miki rai zan yi kokarin kiyayewa domin a yanzu farinciki kike bukata, ina son na fada miki wani abu wanda be zama lallai yai miki dadi ba, idan har Hajiya ta cilasta cewar sai na auri Nana ko wata, ba zan bijirewa umarninta ba, sai dai hakan ba yana nufin na wulakanta ki ba...�

Yana soma fadar hakan sai jikin Falmata yai sanyi, tabbas ta baro wata wahalar zata fuskanci wata, ta san a yadda take ba kowa ba idan Hajiya ta ji ya aureta sai ta sha wahala da wulakancin a duk familynsa, bayan ta laka mata sata a lokacin da babu hadin komai a tsakaninsu balle yanzu da danta ya aureta, a take ta nemi farincikin auren Sirleem din ta rasa, zuciyarta na raya mata kara wacan da wahalar da wannan da zata fuskanta.

“Ba ina fada miki wannan ba ne saboda hankalinki ya tashi, ina tunatar da ke ne abun da ke gaba wanda be zama lallai ya zo kusa ba, wata kila sai nan da shekaru�

Ya fada yana murza tsiraran yatsun hannunta a hankali yana kallon fuskarta.

“Karki min kuka fa come here�

Ya kara janta jikinsa ya kwantar yana shafa kanta zuwa wuyanta.

“Ko da wasa wata ta tambaye ki waye mijinki karki fada mata�

Ta gyada kai, sai ya sumbanci kanta.

“Good girl�

Ya rada mata saitin kunne sannan ya tsotsa kunnen kadan, wani irin yarrrrr ta ji har cikin kanta tsigar jikinta ta tashi. Sai yai murmushi jin yadda take rike hannunsa da yake kokarin saka mata yatsan a baki, hakan ya bashi damar kama lips dinta yana wasa da shi, dayan hannunsa kuma rike da hannunta sai murza yatsunta yake.

“Fada min yanzu idan step mother din ki ta ji cewar ni kika aura za ta yi?�

“Ba zata jidadi ba, domin bata son na samu cigaba ko kadan�

“Hmmm�

Ya fada yana zira yatsansa ta cikin rigarta ta sama, tana jin haka sai komai nata ya tsaya cak ciki har da numfashinta. A hankali yana kara zira hannun yana goge mata fuskarsa a kanta, sannan ya saka dayan hannunsa ya sauke zip din rigarta, saurin barin jikinsa tai jikinta na ta rawa, na rawa na tsoro ba rawa irin na bakom al'amari ya ziyarce ka.

“Zan ...zan kwanta�

Daker ya daga ido ya kalleta da idonsa dake ta lumshi har wani ruwa ya fara taruwa ciki.

“Yeah ni ma bachin nake ji ai�

Ya mike tsaye ya kama hannunta.

“Zo mu wanke baki sai mu kwanta�

Kamin tace komai yaja hannunta zuwa bathroom din, sai da ya fara wanke mata nata bakin da brush sannan ya wanke na shi suka fito. Sakin hannunta yai ya cire rigar shaddar dake jikinsa, sai tai saurin yin kasa da kanta tana jin wani irin kunya ya kamata gabanta ya shiga faduwa da karfi, murmushi yai.

“Ni bana bachi da riga, komai sanyi sai dai na lullube�

Ita dai bata ce komai ba kanta na kasa, gaba daya kwarjinsa ya kara kamata, yadda ya cire rigar nan sai ta ji ya mata girma sosai kamar ba shi ba. Ya nufi wardobe ya bude ya dauko kamin wando.

“Juya karko fara tsorona kuma�

Ta juya da sauri kamar daman abun da take jira kenan, sai yai murmushi ya cire wandon shaddar ya saka boxer sannan ya dauko wani karamin boxer na maza da vest dinsa ya nufo inda take.

“Saka wannan, gobe zan siyo miki na ki kayan bachin�

Ta juyo sai kuma tai saurin rufe ido ganin har lokacin babu riga a jikinsa, zuwa yai ya kashe wutan dakin ya dawo kusa da ita ta fara cire mata rigar da kansa, amaimakon ya saka mata wata sai ya tsayar da hannayensa a kirjinta yana aikin da ya dade yana jiran zuwan ranar shi, jin abun da yafi karfin kwakwaltar yasa ta fara kokarin zame jikinta.

“Sirleem�

“Shiiiiiiii�

Ya dauke ta cak ya kwantar saman gadon sannan shi ma ya hau ya daga ta ya kwantar a kirjinsa ya lumshe ido yana jin yadda kirjinta ke taba na shi, a hankali yake maida numfashi yana shafa bayanta.

“Ban saka rigar ba�

Ta fada tana jin kamar ta fashe da kuka, abun ka da wanda be saba ba, sai wani abu take jin na rashin dadi da kuma kunya.

“Ki fara koyon bachi babu riga daga yau, wannan al'adata ce�

Ya fada cikin rada sannan ya mirginota ya kwantar ya rage tsayensa ta hanyar yin kasa ita kuma tai sama, sai ya dora kansa a kirjinta ya lumshe ido.

“Hmmmmm i miss alot�

Ya fada cikin rada kamin ya kai hannunsa gurin Skirt dinta... Ganin d gaske yake yasa ta fara kokarin tashi da sauri tana jin kuka na rashin dalili yana zo mata.
Chapter 121 · 0% Book details