← Book details Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 164 OF 172

Sashe 164

Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta furta kadan kadan ta zauna bakin gadon tana ta mamaki yadda aka cika dakin da katon farin gado dan turkish da wardrobe kamar wata yar govno, hawa tai saman gado ta kwanta ta sauko ta nufi wardrobe ta shafa, tana jin motsinta sai tai saurin ta dawo bakin gado ta zauna ta kama jikinta ta marairace fuska kamar da gaske babu ruwanta. Bude kofar bandakin yai ya fito rike da babbar rigarsa ya dorata saman gadon sannan ya nufi wardrobe ya bude ya dauko mata hijab. Sai ta karba ta saka gaba ya tsaya ta tsaya daga bayansa kadan kamar yadda ya nuna mata sannan suka soma gabatar da sallah akan katon center carpet din da yake dakin, bayansu sallama yai musu addu'a sannan ya juyo ya kama kanta ta rike ya karanta mata addu'ar da annabi ya koyar da mu.

“Alhamdulillah wannan Allah da mu ka yi godiya ce ga Allah akan irin ni'imar da yai mana, ya hada mu ta sigar da ba mu yi zato ba, kuma ya daidaita mu ya shirya tsakaninku har muka kawo yau da aka daura aurenmu�

Ta gyada masa kai alamar gamsuwa.

“Na yi mana addu'a kuma ina fatar ke ma kin yi mana�

“Eh na yi�

Yayi murmushi.

“Me kika ce?�

“Na ce Allah ya tsare mu daga dukan shari kuma ya ba mu yan biyu, kuma ya mana albarka�

“Yan biyu kike so kenan?�

Ta yi kasa da kai tana jin kunya, to mi ya rage tun da ta yi aure a yanzu ai ba ta da burin da ya wuce haihuwa, ita ma ta zama uwa kamar kowa.

“Samun yan biyu ba sauki fa�

Ya fada yana kallon fuskarta.

“Ni dai ina so haka nan suna burgeni�

“Yanzu fada min yadda ake wankan haila�

Sai ta ji wata kunya ta rufe ta, wai ta fada masa ai da kunya kam ta ina zata fara.

“Fada min mana�

“Gaskiya ni dai ina jin kunya�

Ya kai hannunsa ya kama hannunta.

“Fatee na�

Ta kalleshi.

“Babu kunya tsakanin mata da miji, kuma babu boyewa juna sirri, sannan babu yi ma juna karya, ni mijinki ne sirrinki komai nawa a yanzu na ki ne, haka ke ma sirrina ce, ko da wasa karki kuskura ki fadawa wani cewar mijinki yayi miki kaza ko taba miki kaza ko yace miki kaza kinji ko?�

“To fada min�

Ta fada masa kamar yadda take kuma kamar yadda Inna ta koya mata, ta fada daidai sai dai abun da bata sani ba shi ne yadda ake wankan haila haka ake wankan janaba.

“To ai yadda ake wankan haila haka ake na janaba�

“To minene ita?�

A takaice yai mata bayani duk da ya san ba lallai ta fahimta da kyau, har sai ya nuna mata, ita kam gaba daya ta gama tsinkewa da shi ganin yadda ya zage dantse ya fada mata abubuwa babu ko kunya, tashi yai ya nufi gurin da aka aje musu ledodi, ya dauko ya kawo gabanta ya aje tana jin kamshin kaza ta fara hade yawu, sauka yai kasa ya shiga kitchen ya dauko plate da cup ya dawo dakin, da kansa ya zuba komai ya matsa kusa da amaryarsa ya kwanto da ita jikinsa ya dauki cinyar kazar ya kai mata a baki, kin bude bakin tai haka nan kawai ta samu kanta da jin kunya. Be ce mata komai ba ya kai naman bakinsa ya tauna ya saka hannunsa ya dago kanta ya hade bakinsa da nata ya tura mata naman, tana son namam kaza over amman sai ta samu kanta da kyamar ci wannan.

“Tauna ki hade�

Bata iya masa musu ba, ta tauna naman ta hade, aiko yana kai mata yankan a karo na biyu sai ta bude baki ta ci, haka yai feeding dinta ya bata madarar ta sha ta koshi, sannan ya tashi ya dauko mata mayan bachi.

“To ka tafi waje sai na canja�

“Aa ba inda zan je bari dai na kashe miki wuta�

“To zaka rufe idonka?�

“Eh�

Ya fada yana cire rigar shaddar dake jikinsa, tana ganin kirjinsa da farar fatarsa sai ta yi saurin rufe ido.

“Innalillahi�

Kamar wanda bata taba ganin namiji ba riga ba haka tai, duk ganin da tai ma Wasim a can baya ba riga ta manta da shi sai a yau, murmushi yai ya saka rigar bachinsa sannan ya canja wandon shaddar ma zuwa na bachi, ya nufi gurin da wutar dakin take ya kashe wutar dakin, jin motsinta a bayansa yasa ta bude ido.

“Ka ce zaka rufe idonka�

“Rufe idona yake�

Shiru tai tana jin yadda yake kokarin cire mata zip.

“Kai ni dai ka daina bana so, bana so Wallahi ko na fasa auren�

Murmushi yai duk da ya san bata ganinsa ya janye hannunsa ya nufi gadon ya zauna, sai da ta saka hannun tawulga ta ji ba ya gurin sannan ta cire rigar ta lalaba ta dauko ta bachi ta saka ta cire zanen lace dinta dauko wandon ta saka.

“Na saka ka kunna wutar�

Ya tashi ya isa ya kunna wutar ya tsaya yana kallon yadda ta janyo bargo tana kokarin shinfidawa kasa.

“Me zaki yi?�

“Zan kwanta a kasa�

“Ni kuma fa?�

“Ka kwanta a saman gadon�

“Saboda gani dan iska ko? A kawo min Amarya kamar ke kuma na kwana a saman gado ke a kasa�

“To bari na hau gadon sai ka kwanta a kasa�

Yayi murmushi ya kashe wutar ya nufo inda take tsaye ya saka hannayensa yana shafata.

“Ba wani abu zan miki ba, zaki kwanta ne kawai ni ma na kwanta�

“Rantse�

Kamar saukar aradu haka ya ji rantsuwar da ta bashi, sai yaji wata sabuwar kasala ta sako shi gaba.

“Idan baka rantse ba ba zan yarda ba�

Ta ture masa hannu.

“Wallahi amman a yau�

Ya rantse mata ne saboda bashi da niyar taba a yau, domin ya san halinta kuma ya san akwai gajiya a tare da ita kamar shi din dai. Daukarta yai ya kwantar saman gadon ya kwanta bayanta yana dan shafata a hankali.

“Baby ba a fada miki ki yi min biyayya ba? Ba a fada miki ki yi duk abun da nace ba?�

“An fada min�

“To ki daina min musu, okay�

“Tau�

A hankali yakr shafata, can kuma ya tashi zaune yai mata addu'ar bachi ya tofa mata yai ma kansa, sannan ya sake komawa ya kwanta. Ya kai bakinsa saitin kunnenta a fara karanta mata Bakaqa murya can kasa, yana shafa ta har bachi yai gaba da ita.

Be taba ta har safe, sai da rabin bachin nata a jikinsa tai yi, sai asuba ya tashe tai alwala shi kuma ya shiga yai wanka sannan yai alwala ya fito su kai sallah a tare, bayan sun gama suka sake komawa bachi, misalin 9am aka kawo musu abinci kala kala daga masarauta cikin manyan kuloli na alfarma, da kamsa yai feeding din matarsa sannan ya shiga da ita bandaki sai aka fara drama ita ala dole ba zai taba ta.

‘Da can kai kake min wankan ne, sai wani maida ni kake jaririya kana ce min baby�

Ta fada a ranta tana dan turo baki, sai yai murmushi ya kai bakinsa ya sumbanci bakinta.

“Sarauniyar shagwaba, idan ba ki sonba zan cilasta ki ba, amman ni za ki min�

Ta bude baki

“Babba da kai?�

“Very soon zaki bukaci haka�

Ya fada sannan ya sa kai ya fice ya barta a bathroom din, she a tsaye tana kallon bathroom din tana duba gashin kanta da lallenta kamin ta cire tufafin jikinta tai wanka.
Gidan ya wuni da mutane kala daga bangaren Ammy da kuma Mai Martaba, sai kuma su Inna da suka zo mata sallama, a nan ta fara sabon kuka tana jin kamar ta fasa auren, har tana cewa Inna wai akwai dakuna a gidan idan zata zauna, Farinciki ganin inda Fadime take zaune ya manta Inna wani zancen kewarta ta shafe komai a ranta tana ta hamdalla ga Allah.
Ba ta wani dade a gidan ba ta tafi tare da direban da ya kawo ta, yan'uwanta da yan'uwan su Bappa da suka zo bikin kan a gidan suka wuni sai dare sannan sukai mata sallama. Ana sallah magariba Hajiya Mairo ta zo gidan ta kawo mata ragowar maganin matanta kuma ta fada mata yadda zata yi amfani da shi, Fadime bata ji kewar ta gaske ta kama ta ba sai da kowa ya watse aka barta a katon gidan ita kadai sannan ta fara kuka tana kewar su Inna da za su koma gobe.
Ana sallah isha'i Shattima ya shigo gidan, mai gadinsa ne ya shigo masa da ledodin dake hannunsa, ya aje a falo ya fice da sauri, Shattima ya dauki ledodin ya wuce sama, ya tura kofar dakin ya shiga, sai ya same ta kwance saman gadon tana kuka a hankali, aje lododin yai ya karasa inda take kwance ya sa hannunsa ya dago ta.

“Babyna ya akai?�

“Su Inna ne za su tafi gida gobe�

Rumgumeta yai a kirjinsa yana kissing din kanta.

“Haba Baby ba gani nan ba? Kuma idan an kwana biyun ai zamu je mu gaishesu, kuma za a kawo miki Hadimai a gida masu ta ya ki zama fa�

Ta dago kanta ta kalleta.

“Da gaske?�

Ya sumbanci bakinta ya shafa fuskarka.

“Yes Baby�

Sai ta maida kanta a kirjinsa tai lamo, yana shafa bayanta gemunsa a saman kanta.

“Kin yi sallah?�

“Eh na yi sallah�

“To taso muje ki ci abinci�

“Ammy ta aiko mana da rana da dare ma�

“Iyeee yar gatan Ammy, kuma ga kaza can na siyo miki muje ki ci�

Kamar jiya a yau ma shi ya ciyar da ita, banbanci jiya da yau, Jiya ya kyaleta yau kuma ba zai iya daga mata kafa. Azatonta irin bachin jiya da akai lami lafiya ba komai, har da wani kara shigewa jikinsa take domin ta ji dadin na jiya, kyaleta yai sai ta ta natsu bachi ya soma daukarta sannan ya kai hanunsa yana shafata.

“Yau ba zaka min karatu ba?�

“Kina so ne?�

“Eh ina jindadi�

Yayi murmushi.

“To zan miki wani sabon karatu da yafi wacan dadi�

“To�
Chapter 164 · 0% Book details