← Book details Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 172

Sashe 73

Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ki daina kuka ai komai zai zo da sauki tun da na fadawa Jarma�

Nana ta rumgume Hajiya tana jin wani irin son ta a ranta, domin ta tabbatar da Ammy ce ba zata mata haka ba. Apartment din Hajiya direban ya faka motar, sai Hajiya ta fito rike da hannun Nana ta nufi cikin gidan da ita, har cikin dakinta ta kai ta kwantar.

“Kwanta a nan ki huta�

Ba musu Nana ta kwanta a gurin, Hajiya kuma ta karasa ciki ta aje jakarta ta fice daga dakin rike da wayarta. Tashi Nana tai zaune ta kunna Power button din wayar sai ta samu wayar a pattern da katon hoton AA a din daya cika screen din wayar, wani irin tausayinsa ne ya kara sauka a ranta, ji tai kamar bata da natsuwa idan bata san halin da AA yake ciki ba, hakan yasa ta mike tsaye ta bi bayan Hajiya.

Hajiya ta na fitowa daga dakin, ta shiga second room dinta ta rufe ta kira number Jarma, wannan karon bugu daya ya dauka.

“Jarma�

“Hajiya�

“Jarma a nemo inda yaron nan yake, maganar bokan ta tabbata sunanshi Sardauna�

“Hajiya ai ni abun ya bani mamaki, ace har kin san shi�

“Ni ma sai yanzu nake saninsa, amman ni na siye macijin da hannuna, domin ni na dauke shi aiki ba tare da sani ba, kuma ba tare da na yi bincike ba, ina cikin tashin hankali Jarma ka nemo yaron nan�

“Dole zan saka a nemo shi ai, ba ke dai ce a matsala ba har da ni�

Jarma ya amsa daga dayan bangare.

“Kuma idan an samo shi, ka fada min da wuri, a juyar da case dinsa daga sata zuwa kisan kai, a tura shi gidan kaso, ko nawa ake ashewa zan kashe, ka shigo da safe zamu yi, domin dole ne mu koma gurin mutanen nan kar abubuwan su kara mana yawa, ina murna Nana ta fara dan hali sai kuma abu ya juye min haka�

“Gaskiya kam ya kamata mu koma garin nan daga can ma sai su sanar da mu wacece Fadime ita ma kar ta ribance mu�

“Haka ya kamata, muna ta sanyin jiki abubuwa suna faruwa da mu, ya kamata mu yi maganin komai tun a yanzu�

“Wai daman Nana ta fara dan hali Hajiya�

“Hmm Jarma kenan, ai har abunda ya fi sata sai Nana ta yi, ba ni da buri sai na ganin kukan Ammy kuma sai ta yi shi indai ina raye, yanzu dai ka nemo yaron kuma ka san wanda aka hannatawa case din, gobe ka zo ka karbi kudi ayi komai tun da wuri, abun ai ya zo mana da sauki tun da har haka ta faru�

“Shikenan Hajiya zan shigo gobe inshallah�

“Yayi kyau sai anjima�

Ta fada tana sauke wayar, tare da sauke wata doguwar ajiyar zuciya.

“Dole ne na shirya jibi nai tafiyar nan, idan ba haka ba ban san me zai sake faruwa ba, ya kamata na tari Fadimen ita kuma tun kamin ta tare ni�

Line Hajiya Talatu ta nemo ta aika mata kira, ringing daya ta dauka kamar daman can jiran kiran take.

“Hello Talatu�

“Hajiya ina cikin tashin hankali, Waziri ya dage sai ya hada auren nan�

Ta amsa da muryar kuka wanda hakan ke nuna ta ci kukan har ta gode Allah.

“Nima ina cikin nawa tashin hankali, amman dai ki shigo gobe sai mu yi magana, be kamata mu kyale yarinya akaita ga halaka ba�

“Shiyasa nake son tun wuri mu tafi garin nan tun da aikinsu kamar yankan wuka ne, su wargaza komai tun abu be yi nisa ba�

“Hmm ke dai ki shigo gobe kawai�

“Tau Allah ya kai�

Hajiya ta sauke wayar tana jijjina lamarin bokayen nan sai yanzu ta kara tabbatar ba da wasa suke aiki ba, kuma dama ta dade tana son irinsu masu aiki kamar yankan wuka. A yanzu ne take jin ya zame mata dole ta je garin ko dan maganin matsalolinta.

**
Shirun da Nana ta ji ne ya tabbatar mata da Hajiya ta gama wayar da take, sai ta daga daga jikin kofar wasu sabbin hawaye masu zafi na sauko mata. Why Hajiya zata juyar da case din to kisan kai bayan tace zata taimake ta? Mi Sardauna yai mata? Anya ya cancanci haka? Da sauri ta ta bar kofar ta dauki hanyar da zata sadata da part dinsu hawaye na sauko mata kamar ba gobe, daman ta bi bayan Hajiya ne da zimmar ta sake rokonta sai ta tararda kofar dakin a rufe tana kokarin turawa ta ji sautin muryarta na tashi kadan-kadan hakan yasa ta kai kunnenta domin ta ji abun da Hajiya take fada, domin azatonta zata ji ko Jarma ya gano inda suke ne ko kuma wani abu sai gashi ta ji mummunan abu da bata taba mafarkin ji ba, kuma ba tai zato daga Hajiya ba.

“Miyasa ma nai satar to? Why?�

Ta tambaya cikin kuka tana jin haushin kanta. Ganin bata da mai taimakonta a yanzu wanda zai fito da Sardauna, bata isa ta tunkari Ammy da wannan maganar ba, daman daga Hajiya sai Zainab ne suke mata gata a gidan, sai kuma Shattima, sai dai ba zata iya fada masa ba, gudun kar Ammy taji ko Baba Waziri. Silently ta isa bangarensu ta shige dakinta ba tare da kowa ya sani ba. Maida kofar dakin tai ta rufe ta jingina da kofar ta fashe da sabon kuka tana kallon hoton AA dake gaban wayarsa. Haka ta shafe awa uku zaune a gurin tana aikin kuka abun da bata taba ba, idanuwanta da fuskarta suka kumbura, tun tana jin kuzarin kuka har ta nemi kuzarin ta rasa. Can ta mike tsaye ta cire tufafin jikinta ta dauki tufafin bachi ta saka ta shiga bandaki ta wanke fuskarta, sannan ta fito ta hau saman gadon ta kwanta ba dan tana jin zata iya bachin ba sai dan jin jikinta da take da rashin kwari. Misalin 10 da yan mintuna kiran Anti Rabi ya shigo wayar AA dake hannun Nana.
Second Mother shine rubuce a wayar dauke ta emoji din heart. Kasa daukar kiran tai sai kawai tai rejecting call din ta kashe wayar gaba daya.

“Innalillahi�

Ta furta, she can't remember when last ta furta wannan kalmar ma. Bata taba jin ta a tashin hankali irin yau ba, abun da ta ji Hajiya Babba na fada ya fi daga mata hankali fiye da halin data jefa AA. Sauka tai saman gadon ta bude kofar dakinta ta fito falo, babu kowa a falon an kashe kayan kallo wanda hakan ke nuna Ammy tana bangaren Mai Martaba ko kuma tana shirin tafiya ne. Dakinta Nana ta dosa tana taba kofar ta ji ta a bude sai ta tura ta shiga, duk wani tsoron kar Ammy ta ji da take da gudun fadanta ko dukan Baba Waziri sai ta ne meshi ta rasa, bata da buri a yanzu da ya wuce AA ya zama free. Daga bakin kofar ta tsaya tana kallon Ammy dake tsaye jikin wardrobe dinta tana daukar wasu kaya, ta jikin madubin wardrobe Ammy ta hango Nana sai ta juyo tana wani kallo fuska ba yabo ba fallasa.

“Ya akai?�

Nana ta kalleta hawaye na sauko mata, sai kuma ta nufi inda take ta karasa har kusa da ita.

“Ammy... �

Sai kuma tai shiru hawayen na sauko mata.

“Ammy na san ni da ke don't get along, amman dan Allah ki taimaka min�

“Minene?�

“A gurin bikin da naje dazun na su Amal na saci sarkar gold ta kawar Amal, nasan be dace nai sata ba right? Na sani amman ban san miyasa nai ba, direbana sai ya karbi sarkar yaje ya maida shine suka ce shine ya dauka kuma Wallahi ba shi ba ne ni ce, shine suka kira masa police aka tafi da shi, dan Allah ki taimaka Ammy a fito da shi pls�

Ammy ta saki kayan hannunta sun zube kasa, tana yi ma Nana wani irin kallo kamar na tsoro kamar na mamaki, a take idonta ya cika da kwalla. Tassss ta dauke Nana da wani irin mahaukacin mari, cikin wani irin zafin nama da bata taba sanin tana da shi sai yau.

“Sa... Sa... Sa... Sata Nana?�

Ta furta daker hawaye na sauko mata, Nana kam tun da Ammy ta tsinka mata mari tai bata da sauri tana ma Ammy wani kallo tsoro domin ji take kamar babu fuska a jikinta.

“Na san be dace nai ba Ammy na sani....�

Ta furta a rikice tana girgiza ma Ammy kai. Sai kuma ta juya da gudu da fice daga dakin, Ammy ta bita da kallo baki sake, wani abu ta ji yana mata yawo a zuciya yana neman numfashinta, da sauri ta rike murfin wardrobe din ta jingina ta zauna a kasa tana numfashi daker.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un�

Ta furta daker tana ta kokuwa da numfashinta.

FADIME POV.

Hannu biyu Wasim ya saka ya dauki Fadime ya ya nufi kofar fita, zaratan mazajen da suke fadar tsaye suka nufishi sai Sarkin ya daga musu alamar su kyaleshi. Zainab na ganin hakan ta bi bayansu yadda yake tafiya da gudu sai ka dauka biyo shi akai Fadime kam sai tari take hankalinta ya dade da barin jikinta. Duk inda ya nasa kafarsa Zainab sai ta nasa tata, har suka isa wani karamin gida mai dauke da dakuna uku, dakin farko ya shiga wanda shi ya fi ko wane daki girma. Yana shiga ya kwantar da Fadime gaban makahon bokan ya soma magana da shi da yarensu.

“Kaka ka taimaka mata ta daina tarin nan kar ta samu matsala�

Bokan ya mika hannunsa ya taba fuskar Fadime.

“Wasim miyasa ka aikata haka?�
Chapter 73 · 0% Book details