← Book details Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 120 OF 172

Sashe 120

Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Na kasa yarda komai gaskiya ne, na kasa yarda cewa kai na aura, na kasa yarda cewar nan din gidan aurena na ne, har yanzu ina jin kamar mafarki na ke, na yi zaton tsohon zan aura da gaske, na yi zaton rayuwa zata zo mi a wahale ne�

Ta lumshe ido hawaye a sauko mata.

“Ban cancanci zama matar babban mutum kamar kai ba, duk da na san ka yi ne saboda ka taimake ni...�

“Kin cancanci auren wanda ya fini ma Teema, kina tarbiya ga hakuri kowa wane namiji mai mutunci zai so yayi dace da ke a matsayin mata�

Ya kai hannu ya kama hannunta ya rike yana murza yatsunta a hankali.

“Kina da kananan shekaru amman kina da tunani da hakuri kamar babba, rayuwarki na burge ni, a yanzu ma kin yi zaton ni din tsoho ne amman a haka kika zabi zama da ni ki rumgumi kaddararki, hakan yasa na kara jin kin kwanta min a rai fiye da da�

Ya saka dayan hannunsa yana share mata hawaye.

“Kuka ya kare, bana son kina saka kanki a damuwa yanzu�

Ta bude idon still tana hawaye, shi da kanshi ya tayar da ita tsaye sannan ya suka ya dauke ta cak.

“Ashe ma amarya ta bata da nauyi�

Fashewa tai da kuka, har lokacin bata jin ta koma daidai ba. Sama ya haye da ita ta zaunar da ita akan katon gadonta ya sumbanci goshinta.

“Kina da alwala?�

“Aa�

Zai sake wata maganar wayarsa tai ringing, sai ya saka hannunsa aljihu ya ciro wayar ganin number Hajiya yasa gabansa faduwa.

“Hello Hajiya?�

“Sirleem kana ina?�

Ya dan yi jimm yana tunanin ko an labartawa mata wani abun ne, duk da ya san be fadawa abokansa ba balle wani ya fada har Hajiya ta ji, sai amininsa shi ma dan yana da tabbacin ba zai fada ba ne.

“Ina gidana, kaina ne yake dan ciwo a nan zan kwana�

Yana jin lokacin data sauke ajiyar zuciya sannan ta amsa masa da.

“Allah ya kara sauki, for now on bana son kana kwana a waje, kasan na saba fada maka wannan ba sau daya ba�

“Na sani Hajiya, amman ba abun da kike zargi ba ne�

Ya fada yana kashewa Falmata ido daya, Hajiya bata son yana kwana wajen masarautar ne saboda Mansura, a tunaninta idan ba ya kusa da ita to yana kusa da Mansura ne, duk kuwa da sanin cewar ba a Yola take ba, sai dai ta san wani lokacin tana zuwa Yola gurinsa, saboda Hajiya ta hana shi yin komai a Kaduna yanzu ba dan komai ba sai dan ya daina haduwa da Mansura.

“Shiga ki yi alwala bari na dauko mana kazar mu�

Ya fada yana jefar da wayar kan gado.

“Sirleem�

Ta kira shi sai ya juyo ya kalleta fuskarsa na ta annuri.

“Hajiya Nana take son ka aura, kuma Mansura ma tana sonka, kuma yanzu ka aure ni�

“Yeah...�

Ya furta sai kuma yai shiru ya dawo kusa da ita ya zauna.

“Maganar gaskiya, haduwar da nai da ke yasa na ji ba zan iya auren Mansura ba, saboda tana da bad habit, na yi iya abun da zan iya na raba da samari na kasa, na san tana so, amman tana mu'alama da wasu mazan, a iya tunanina idan na aureta ba zata daina ba ni kuma ba zan samu aminci da ita ba, and every good man yana son ya samu mata mai tarbiya kuma yar gidan mutunci kamar ke...�

Ta yi masa da kanta.

“Nana fa?�

Ya tabe baki tare da daga kafadunsa.

“Na taba fada miki cewar hadin Hajiya ne?�

Ta dago tare da daga masa kai.

“I don't think ina son Nana a raina, ina mata dai so ne irin na kanwa da yaya, amman bana soyayya ba, kawai dai na bi umarnin Hajiya ne, ita kanta Nana a yanzu idan aka tambaye ta za ta ce bata so na�

“Amman idan Hajiya ta ji, Ammy da Shattima da Mansura da Nana zan shiga uku...�

Ya dora yatsansa a kan bakinta.

“Shiiii you talk to much, ki manta da kowa a yanzu, duk wata matsala da rigima ni ne zan shiga ba ke ba�

Ya mike tsaye.

“Bari na dauko abu downstairs�

Yana juyawa sai Falmata ta mike tsaye ta rumgume shi da baya.

“Wata kila idan na rumgume ka zan yardar kai ne, kuma zan yarda ba mafarki na ke ba�

Ta fada tana lumshe wasu hawayen da bata san na minene ba su ka sauko mata. Murmushi yai ya juyo ya rumgumeta.

“Kin cancanci fiye da haka Teema na�

Sakinsa tai tunawa da abun da tai da kanta na rumgumarsa abun da bata taba ba, murmushi yai ya fice daga dakin.

***

Hajiya ta sauke wayar tana kallon kular tuwon dake gabanta.

“Me yace?

Jurry ta tambaya.

“Baya jindadi a waje zai kwana�

“Okay�

Ta dauki plate din abincin da ta gama ci tare da mikewa tsaye har zata fice sai kuma ta juyo tana fadin.

“Yauwa Hajiya, na manta wai Kausar tace min lokacin da taje kai su Hajiyar Zariya Gaisuwa a gurin Ammy ta ga wata yarinya makauniya tana fadar a boyeta kar Iya da Hajiya Babba su ganta, ina son na fada miki sai na manta�

Hajiya Babba ta juyo tana kallonta.

“Yaushe? Wacece?�

Wallahi ni ma ban sani ba, ranar da aka kai su Hajiya dai su yi mata gaisuwa.

“Ko wannan yarinyar ce Falmata?�

“Ni ma haka nai tunani, amman kuma Kausar ai ta san Falmata�

“Kira min Kausar din�

Hajiya ta fada tana tashi zaune da sauri. Jurry ta amsa da to sannan ta fice rike da plate din. Bata dade ba ta sake dawowa dakin tare da Kausar tana dake ta danna waya suka zauna a kasa.

“Kausar�

“Na'am Hajiya�

Ya amsa mata idonta na kam waya.

“Kalle ni nan ki aje waya�

Kausar ta aje wayar tana kallon Jurry kamin ta kalli Hajiya a tunanin wani laifi tai.

“Wa kika gani a dakin Ammy?�

“When?�

Ta tambaya domin ita ta manta da zancen ma. Sai Jurry ta dafa kafadarta.

“Ranar da kika je kai su Hajiyar Zariya ba kin ce kin ga wata yarinya ba har tana fadar a boye ta kar Hajiya ko Iya su ganta�

“Oh Eh me aka yi?�

“Kin san yarinyar ne? Ko Falmata ce?�

Hajiya ta tambaya.

“Aa ni ban taba ganinta ba, kuma ita fara ce sosai har ta fini haske Falmata kuma ai baka ce, kuma wannan bata gani har tana cewa wacece ni�

Hajiya ta yi shiru tana nazari.

“Duk yadda akai yarinyar ta san ni, idan ba haka ba, me zai saka ta ambaci sunana? Ko kuma Ammy ce ta fada mata wani mummunan abu a kaina?�

“Maybe, to amman kuma ai har da Iya ta ambata. Hajiya kin san yadda za ayi? Bari na tashi na je na kaiwa Nana lace sai na dubata daga can�

Cewar Jurry tana kallon Hajiya. Sai Hajiya ta daga mata kai.

“Okay�

Jurry ta mike da sauri ta nufi wardrobe Hajiya ta bude ta dauko wani tsadadden lace sannan ta maida Wardrobe ta rufe ta nufi kofa.
Kamin ta isa bangaren Ammy har da hadawa da sauri kamar wanda aka cewa jeki gata a can ki gani, door bell din daya kamata ta danna sau daya ko sau biyu ta danna sau ba adadi kuma ta hada ta knocking. Cikin rashin sa'a Nana ta bude mata kofar, sai tai tsaye kamar hoto tana kallon Nana, Nana na ganin hakan ta juya ta dawo cikin falon hannunta rike da apple daman can ba jituwa suke da Jurry ba, dama dama Kausar ko Karima amman Jurry bata shan inuwa daya da Nana. Shigowa tai cikin falon kamar yadda ta saba ba tare da sallama ba, ta nufo kusa da inda Nana take zaune ta zauna tana ta rabon ido, babu kowa a falon sai Nana sai wata yar cousin din Ammy dake zaune dinning tana cin abinci. Tunani ne ya zo mata Rahila ce bakuwar da Kausar take fada ko kuma ita ta zo tare da wata? Amman a iya tunaninta ai Kausar ta san Rahila, kuma ta ce wacan makauniya ce.

“Rahila yaushe kika zo?�

Cewar Jurry a kokarin ta na tantancewa, daga Nana har Rahila da aka kir juyowa suka yi suna kallonta, domin Nana ta san halinta ganin mutum tai masa magana ba nata ba ne, sai idan kawayenta na na kusa ko kuma wasu na bangaren Hajiya, Jurry tana da wani irin hali na ji da kai ko ta sanka zata iya yin banza da kai ko kuwa ka mata magana ne.

“Yau Anty Jurry ina wuni?�

“Lafiya Kalau ya gidan ke kadai kika zo?�

“Eh�

“Owk Ammy na ciki?�

Ta tambaya tana kallon Nana.

“No tana bangaren Mai Martaba�

Nana ta fada sannan ta mike tsaye ta nufi dinning din.

“Am Nana ga lace in ji Hajiya tace a baki�

“Ki aje nan na gode�

Ta fada a cikin yanayin da bata saba ba, ada idan Hajiya tai mata kyauta da sauri take zuwa ta karba tana murna d tsalle.

“Kuma tace a kira ki wai kin daina zuwa bangarenta�

“Ki ce ina gaisheta, makaranta bata barina zama yanzu shiyasa�

Da mugun mamaki Jurry take kallon Nana, sai da ta isa dinning din ta zuba ma kanta abinci ta fara ci, sannan Jurry ta aje lace din ta fice.

Na jiya 👆 anjima zan bada na yau inshallah
03/12/2021, 18:56 - 🤐🤐🤐🤐: *Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*

SHATTIMA POV.

“Wannan wane irin zance Shattima? Waziri na iyakar kokarinsa kana son gujewa abun da yake shirya maka? Dan Allah ka kwantar da hankalinka babu abun da zai sake faruwa Inshallah�

Ammy ta fada sannan ta kalli Baba Waziri ta ce.

“Waziri a cigaba da shirye shirye, karka biye masa, domin na gane manufarsa ya cigaba da zama a haka�

Baba Waziri yayi murmushi irin na su na manya.
Chapter 120 · 0% Book details