Sashe 108
Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mikewa tai tsaye ta kabe jikinta ta fito a gurin ba dan ranta ya so ba, sai dan ta san idan har ta sake yunkurin zata wahalar da kanta ne kawai, idan har tana son tai saurin riki dole ne sai ta sha maganin wanda zai suma jikinta ta taimakawa aljanin maitar da take yawo da shi. Mai kula da dawakan na mata magana bata ko kula shi ba tsabar haushi da takaici ta wuce shi kamar ana turata ta nufi gate.
WASIM POV.
Bappa ya mika wakawa Wasim hannu suka gaisa, sannan Wasim ya cire hular kansa ya kalli Bappa.
“Sunana Wasim, na san baka san ni ba, duk da bani da tabbacin ko Fadime ta taba labarta maka wani abu akaina�
“Aa bata taba fada min komai ba, lafiya dai�
Wasim ya gyara tsayuwarsa tare ta saka hannayensa duka biyu aljihun wandonsa na jean.
“Na dade da sanin yarka sai dai bata tana sani na sai daga baya, ina yawan ganinta idan taje kiwo ko diban ruwa, amman ban taba mata magana ko nuna na santa sai daga baya, cikin kankanen lokaci muka shaku da ita, ni ne mutumen da ta bukaci na yi mata dabon maciji na yi mata ta dawo gida da maciji a tulu an yi haka?�
“Tabbas la shakka an yi haka�
Bappa ya fada yana kara kallon Wasim da kyau a take ya nemi gajiyar da yake ji ya rasa sawun giwa ya take na rakumi.
“Na yi mata, bayan haka ni ne mutumen daya sauya mata murya a ranar da wani zai zo ganinta daga birni sai dai ba tare da ita din ta so haka ba, ka tuna�
Bappa ya daga kai cike da gamsuwa.
“Na san da wannan�
“Ni ne mutumen daya fada mata akwai wuta maita da take bibiyarta, kuma ni ne mutumen da na kama mayyar na daki cikinta a lokacin tana cikin siffar mage, ban san iya abun da tai ba, amman ba dukan wasa nai mata ba, doka ne wanda ke taba hankali duk wata halitta mai jini da hanta, wanda n tabbatar har yanzu bata samu lafiya ba�
“An yi haka, hakikanta amri�
“Ban yi zato ba yarka ta zo tare da wata mata ta fada min cewar tana son na shiga da matar garinmu ta dauki hoto, na kaisu ba saboda matar ba sai dan saboda Fadime duk da na san garin mu gari ne da basa karbar bako, a lokacin ne muka samu akasi har mahaifina ya ganta, yasa aka kira mu ya bata naman kura yace ta ci, ta ci naman da ke saka duk wanda ba dan garin ba kaiyi a makoshi da baki, a kokarin mahaifina na horani sai yace be yarda a fitar da yarinyar daga garin ba, wanda na san yayi haka ne saboda ya san zata matsu ni ma kuma zan ji ba dadi na takurar da mahaifina yai mata, sai a nan ma na kasa bin umarninsa saboda ta matsa min da kuka cewar tana son na dawo da ita a nan, na fito da ita ba tare da izinin sarkin garinmu ba, mahaifina kenan wanda haka ne ya haddasa mata makanta, shi ma daga mahaifina ne a kokarinsa na sake min horo ni da ita, wanda ko gobe aka ce ta zo garin ko kuma ni na kaita ba zan kara ba, Kaka ne ya fada min cewar an tura mata makanta kuma kun dauketa zuwa asibiti har a inda zan same ta shi ne ya fada min kasancewarsa matsafi ne, ni na na shiga asibitin na dauke na fitar da ita daga garin da sunan zan kawo ta gurinku sai na kaita wani gurin ajiya, a inda na kaita kuma na kafeta irin kafin da ko mutuwa tai ba za a iya dawowa da gawarta har sai idan ni naje na dawo da ita...�
Bappa jin yai kafafuwansa ba za su iya daukarsa, sai ya nemi guri a kusa da kofar gidan ya rage tsayunsa, wanda hakan yasa Wasim din shi ma da kansa ya rage nasa tsawo. Ban da kallon Wasim babu abun da Bappa yake, a yadda yake ganin kamala da natsuwa a fuskar Wasim da kuma ladani alamansa sam ba zaka ce zai iya yin wani tsafi ba.
“Kenan kai dan garin can ne da ake kira da Garuk?, amman miyasa ka dauke ta?�
“Saboda za a iya taba idonta a nan, idan baku kaita asibiti wata kila zaku iya gwada yi mata na hausa, wanda ko wane a cikinsu yana da illar da zai iya saka ta rasa ganinta gaba daya, bayan wannan a nan za ku yi mata fada ba zaku saurareta ba, musamman kai da kake mahaifinta, domin a kullum maganarta Bappa zai karyata ko sai ya kusa asheta, na zabi zuwa na fada muku gaskiya domin na san ba lallai ne Fadime ta fadi gaskiya ba saboda tana tsoron ku, kuma saboda na kwantar muku da hankali ku samu natsuwa kuma ku sn cewa yar ku tana nan cikin koshin lafiya, kuma da zarar idonta ya bude zan dawo da ita dawowa ta har abada�
Bappa yayi shiru out of words be san abun da zai sake cewa ba for now. Abun da Fadime ta fada masa cewar aljanu ne kenan ba gaskiya ba ne? Ashe duk abun da take fada masa karya take shirya ba, sai a yanzu Bappa ya tabbatar Fadime ta wuce tunaninsa da iya tsara abu kamar ya faru da gaske. Dagowa Bappa yai yana fadin.
“To amman da ka....�
Da sauri Bappa ya mike tsaye yana waige waige ganin babu kowa a gurin sai shi kadai.
“Subhanallahi�
Ya furta cike da tsoro marar misaltuwa.
“Ya bace bat...!�
Da sauri Bappa ya juya ya koma cikin gidan, a gaban makociyar su Inna ya labartawa Inna komai, a take Inna ta tashi zaune tana jin kamar ta samu lafiya.
“Amman da ya taimaka ya kawo mana ita, in ya so sai mu kiyaye duk abun da ya fada�
“Ni ma abun da na tashi fada masa kenan ina dubawa sai na ga babu mutum�
“Kasan tsafi ne da su, wata kila yana da layar bata, layar zana�
“Ba mamaki, amman Fulani akwai karfin hali yanzu har ta taka taje garin nan? Anya kuwa Fulani bata da aljanu gaske? Kwata kwata babu tsoro ko fargaba komai a idonta�
Inna ta rausayar da kai.
“Fulani kam Allah dai ya shirya, gaba daya rayuwarta ban san wace iri bace, kuma babu yadda ban yi mata gargadi ba akan kar taje garin nan amman bata ji, to yanzu ya zamu yi kenan?�
“Hakuri zamu yi kawai, kuma gobe idan Allah ya kai mu sai na tafi na fada musu na na jany karar�
“Bappa Fadime ai ba kara ka kai ba, kai cijiya ka kai musu, dan haka ka kyalesu kawai domin idan ka koma wata kila ma za a ce ka kawo wani abu ne, ka kyale su kawai idan ma sun ji wani abu ai za su kira tun da Shatu tace ka bada number wayarka�
Cewar mamansu Ramla. Bappa ya amsa mata cike da gamsuwa.
“Haka ne kuma da zancen ki, amman dai idan kana jin mu bawan Allah ka daure ka kawo mana ita, mu kuma ba zamu nema mata maganin komai ba�
Inna ta daga kai tana kalle kalle kamar ance mata zata ganshi.
HAJIYA BABBA POV.
Tun rasuwar Talba Hajiya ta koma kamar wata marar lafiya, bata da kuzari walwalar duk ta gushe kullum tana dakin sai idan za ta yi wani abun sannan ta fito waje, zuciyarta ta saka sakin tunanin Talba, ba mutuwarsa take ji ba kamar rushewa al'amuranta, gashi a da tana tunanin zata fi Ammy gado ko da Mai Martaba ya rasu, saboda Talba yana a matsayin Shattima Juwairiyya da Karima kuma suna matsayin namiji daya sai Kaunar dake matsayin Nana, yanzu kuma sun za daya tun da Talba ya tafi, Sirleem kuma ba zai gaji Mai Martaba tun da ba dansa ba ne, Tunanin hakan yasa tun farko ta zo a haihu da yara a gidan amman be bata da yawa ba, sai ya bata hudu, namiji hudu mace uku.
Ga burin da take da shi na son Talba ya samu sarauta yanzu ya kau, sai abubuwan suka taru suka mata tsaye a zuciya ko abincin kirki bata iya ci. Tana zaune tana ta tunanin duniya Sirleem ya turo kofar ya shigo yana sallama, sai ta amsa masa da muryarta dake karantar da shi tsantsan damuwar da take ciki, kusa da ita ya zauna yana jin babu dadi a yanayin da ya same ta, domin duk dan kwarai ba zai so ganin mahaifiyarsa a cikin damuwa ba.
“Hajiya...�
Juyowa tai ta kalleshi cikin kwanakin nan naman fuskarta ya sauka fiye da da, ma'ana ta yi rama sosai.
“Sirleem kana lafiya?�
“Lfy kalau ya jikin?�
“Alhamdulillah, magana nake son yi da kai, magana ta karshe ba shawara zan baka ba umarni ne�
Tun kamin ta karanto masa abun da take so gabansa ya fadi.
“Minene Hajiya?�
“Bana son wakar nan da kake yi, kaskanci ne a gareka da mu da kowa ma naka, bana son wakar da kake, baka rasa komai ba a duniyar, me zai kasa ka zabi waka?�
“Waka sana'a ce Hajiya�
“Na yarda sana'a ce, amman ba ga dan babban mutum kamar kai ba, mu ya kamata ace muna kyautatawa mawaka muna musu alheri muna basu dukiya, kai fa idan ana son kiranka kai kayatar a taro ko biki, ina jin zafi kuma kaskanci ne a gareka a matsayinka na a gola a gidan Sarki kuma dan former vice president, abun da ko wane dan babban mutum yake a yanzu kokarin yaga ya yi kamar ubansa ko ma ya wuce ubansa, ka yi karatu a waje kai fa engineering ka karanta miye hadinka da waka? Why? Bana so kuma ina mai umarta ka daina, kai kadai ka rage namiji a yanzu, so nake ka zama babban mutum kamar mahaifinka ba mawaki ba�