← Book details Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 133 OF 172

Sashe 133

Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Saboda ke ne, duk abun da ya faru da halin da na ke ciki saboda ke ne Iya, saboda zargin da Shattima yake yi akan mu ya rufe mu a dakin horo, dakin da ko dabba ba zata iya zama a ciki ba, haka na kwana cikin sauro babu abun shimfida balle na rufi, ban taba tunanin zan wulakanta kamar haka ba, ban taba tunani wata rana zata zo da rayuwa zata zame min haka ba, a yau na yi nadamar haihuwata da kika yi, ba ni da dangi, ba ni da kowa ba uba, ga uwa ta zame min wata kala, da wanne zan ji?�

“Ce masa akai ke kika dauki yarinyar nan?�

Zainab ta share hawayenta ba tare da tace komai ba ta wuce dakinta wasu hawayen na sauko mata. Ko kadan Iya bata jidadin abun da Shattima yai ma yarsa ta, cikin bacin rai da tunanin irin abun da za ta yi masa ta shiga nata dakin ta zauna bakin gado tana mamakin yadda Shattima da kansa zai taba mata ya, duk abun da take yi bata taba tunanin taba shi ba, bata taba tunanin yi masa komai ba sai dai taba matansa ko yaya saboda tana masa fatan samun Zainab amman a yanzu ta kaita karshe shi da Ammy, domin a yadda ta fahimta abu ne mai wahala wata mu'alama mai karfi ma ta sake shiga tsakanin Zainab da Shattima, ita kuma a yanzu zama a masarauta yayi mata wahala, ba m masarautar ba har mutanen cikinta a yanzu dole wadanda suka san sirrinta su yi mesa da ita, hakan na nufi ita da Zainab din ba su da makoma. Sauko tai kasa ta zauna ta janyo kular namanta ta bude ta fara ci.

“Shegiyar kurwa ko mai babu�

Ta fada tana cin nama cike da jin haushi, bata tashi ba sai da tai ma naman kat ta cinye komai..

HAJIYA TALATU POV.

Maijidda ta shari bachi iya bachi bata barka ba sai kusan asuba, kamin ayi sallah ta shiga bandakin dake asibitin tai fitsari tai alwala ta fito ta zauna bakin gadonta. Hajiya Talatu sai murmushi take mata tana jindadin lafiyar da ta samu duk kuwa da kasancewar bata da wani sukuni sosai.

“Ya jikin na ki?�

“Alhamdullah na ji sauki�

“Allah kara lafiya, ni ai da farko na tsorata sosai Wallahi, ko da muka kawo ki asbitin nan ba ki san inda kan ki yake ba�

Ta dan yi murmushi tana kallon yatsun hannunta. Hajiya Talatu da kanta ta tashi ta hada mata tea da kayan tea da aka kawo mata tun da dare, ka dan ta sha ta zauna jiran sallati, ana yin kira ta karbi hijabin Hajiya Talatu ta saka ta gabatar da sallah azuba, bayan ta gama ta mikawa Hajiya Talatu sai ita ma ta gabatar da tata sallah. Misalin takwas aka kawo musu abun karyawa, a nan Hajiya ce tai hidimar zuba mata ta bata a plate sai tea a wani karamin kofi ta mika mata. Gaba daya sai ta Maijidda ta ji komai ya fita a ranta dan kwan kawai ta ci ta sha ruwan shayi kadan ta aje.

“Lafiya? Ko wani abun kike so a girka miki�

Hajiya Talatu ta tambaya

“Aa bana jin cin abinci ne, jikina ina jinsa kamar ba nawa ba�

“Ciwo kike ji?�

“Bana jin ciwo komai kawai dai ina ta jin wani yanayi na dabam�

Hajiya Talatu ta aje kofin shayin da ke hannunta.

“Kamar ya?�

“Ban san ya zan misalta ba, ina ta jin kewarku Momy, ina ta jin kamar zan tafi na barku�

Ta fada idonta na cika da hawaye har wani ya fara sauko mata, bata taba jin irin yanayin da take ji a yanzu ba bata taba jin kewar kowa kamar yanzu ba, gashi ta rasa yadda zata misalta yanayin da shi ba na ciwo ba ba kuma na lafiya ba, ba na dadi ba ba kuma na bakinciki ba.

“Kin gani Jidda bana son maganganun nan na banza, daga ciwo sai ki fara wani zancen mutuwa wane irin magana ne wannan dan Allah?�

“Wallahi Momy ina jin wani yanayi na dabam, ni dai dan Allah ki yafe min ko da na mutu�

“Ba ma za ki mutu ba, sai kin yi aure kin haifi yayanki na gani da yardar Allah, Allah dai ya baki lafiya ya yaye miki ko minenen�

“Ameen�

Ta amsa tana kwantawa saman gadon sai kallon dakin take, ta yi shiru kamar ba ita ba, motsin ac da hayaniyar mutane da take ji a waje sai ya zo mata a wani yanayi na dabam, can kuma ta juyo ta kurawa Hajiya Talatu ido tana ta kallonta irin kallon na bankwana, irin kallon nan da kake ji kamar kar ka tafi ta bar komai na ka. Hajiya Talatu kam hankali ya tafi gurin wayar da take sai dariya take.
Misalin 9am da yan mintuna Hajiya Talatu ta fita waje saboda masu gyara dakin da suka shigo su yi mopping, kamar fitar Hajiya Talatu ake jira sai wani bachi mai dadi ya fara kewayar Maijidda tun tana hamma har ta fara jin jikinta ya zama very weak ko hannunta ta gagara dagawa, nan da nan bachi yai gaba da ita bachin da babu farkawa, bachinta na karshe a idan duniya, bachin daga shi zata farka ta ji a dakinta na gaskiya.
Mai shara ta yi tai gama tai mopping ta fita ta rufe dakin, Hajiya Talatu bata dawo dakin ba sai da Haroon ya shigo tare kanwarsa.

“Bachi take�

Hajiya Talatu ta fada ganin tana jan numfashi tana maidawa a hankali, har zata tashe ta sai Haroon ya hana ta.

“Ki kyaleta kawai idan na shigo anjima sai na dubata�

“Tau ba matsala�

Sama sama su kai fira da Hajiya sannan ya fice ya bar kanwarsa Hajiya na Fadin.

“Allah yasa da sun zo su sallame mu, tun da tace jikinta ba ya mata ciwo komai yanzu zaman Asibiti ba dadi�

Ta fada tana gyara zamanta, wani irin zabura Maijidda tai daga cikin bachin da take ta matse hannunta tai wani abu kamar zata tuma sama daga kwance da take sai kuma tai lamooooo babu motsi.

“Subhanallahi jidda�

Hajiya Talatu ta fada tana mikewa tsaye ta isa gaban Maijidda din, hannu ta kai ta taba ta tana kokarin tashinta.

“Jidda Jidda...�

Haka Hajiya Talatu tai ta kiranta tana motsata, amman bata motsa ba, kuma ba ta amsa kiran ba, sai Hajiya Talatu ta kwantar da kanta jikin Maijidda tana sauraren numfashinta. Nan ma bata ji alamum tana numfashi a razane ta dago tana kallon Afra.

“Afra je ki kira likita yi sauri�

Sai tai rasa akan gaba domin tana rufe baki, likita ya turo kofar dakin ya shigo tare da nurse yana dariya da alama wata maganar suke. Tsakanin Hajiya Talatu da Afra sai ka rasa wane ya fi saurin sanarwa likitan abun da yake faruwa, da sauri likitan ya karasa inda Maijidda take kwance yana dubata, fita yai da sauri ya kira wasu likitocin biyu suka shigo cikin hanzari suka hau bata taimakon gaggawa amman ina mai kira yayi kira rai yai halinsa Maijidda ta bakunci lahira...
Dayan likitan ne ya fitar da Hajiya Talatu waje ita da Afra, sai ta tsaya bakin kofar tana kuka hankalinta a tashe, gaba daya ta rasa abun yi ko zama ta gagara yi. Bayan wadansu mintuna likitoncin suka fito ko wanensu fuska babu annuri hakan ya sanarwa Hajiya da Afra cewar sun rasa Maijidda rashi na har abada, Maijidda ta yi bachi da babu farkawa a duniya, ta tafi inda ko wane mai rai ke tsumayin zuwa.

“Hajiya... Ku yi hakuri�

“Ban gane na yi hakuri ba likita kamar ya na yi hakuri? Me kake nufi?�

Ta tambaya cikin kukan tun kan a sanar mata.

“Hajiya kin san duk mai rai mamaci ne, ki yi hakuri Allah ya karbi abarsa�

“La'ilaha illahu innalillahi, wayyo ni Allah na Maijidda�

Cikin wani irin fitar hayyaci da ihu da kururuwa Hajiya Talatu ke fadar hakan ta nufi dakin da Maijidda take ciki sai likitan ya riketa, Afra kuma ta zube a gurin tana ta borin iska, aljanunta na son tashin.

FADIME POV.

Misalin sha biyu na rana direban Mama Fulani ya isa da Fadime asibitin da Muhseen ke aiki. A harabar asbitin ya fara motar sannan ya fito ya zagayon bangaren da Fadime take ya bude mata ya rika hannunta ta fito, sannan ya rufe motar yaja ta su kai gaba, ita dai tafiya kawai take tana sauraren hayaniya da kuma irin hanyar da suke bi, idan ta ji wani tunanin zai zo mata sai tai saurin kawar da shi.

“Kai dan Allah duk kana ganin mutanen nan?�

Direban ya kalleta sai ya ji tausayinta ya kamashi sanin cewar bata ganin komai, a lokacin ne ya gane lalli ga ni da ji wani babban ni'imace da Allah ke ma bayinsa.

“ina gani diyata�

Sai tai shiru ta cigaba da saurare tana ayyana yadda surar kowa take a ranta, a haka har suka shiga office din da Muhseen din yake. Ba su tararda shi cikin ba hakan yasa dole sai da suka dan jira ya dawo.

“Sai yanzu tun dazun na ke ta jira fa, likitan ma ya kusan tashi�

Muhseen din ya fada yana karasa gaban teburinsa.

“Ina kwana?�

Fadime ta fada sai ya wara ido da mamaki.

“Wow gaisuwa dai?�

“Eh ita wannan da kace mamata ce ita ce tace na rika gaishe da mutane, wanda ka ce dan'uwana ne ya zo tace na gaishe shi, kuma na gaishe da matarsa duk na gaishe su, tace ina kwana ake cewa da safe da rana ina wuni...�

Kai tsaye ta labarta masa wannan tana kallon saitin inda yake tsaye kamar tana ganinsa, kara bude ido yai da mamaki, sai ya ji ta burgeshi. Ya kalli direban

“Am za ka iya tafiya, idan an gama zan maida ita gida ko na kira ka kawo ka dauke ta�

“To ranka ya dade�
Chapter 133 · 0% Book details