← Book details Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 160 OF 172

Sashe 160

Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta karasa tana danne kukanta, ya fara takawa tare da ita suna tafiya. Tana tafiya hawaye na wanke mata fuska, a ranar mutuwa ne kawai Zainab ba tai ba akan kuka, duk yadda take jin rashin kyautar Iya da yadda take jin kamar zata iya tafiya ta barta mutuwarta ya kawar mata da komai, sai ta ji kamar ace bata mutu ba, no matter how bad she is ta ji tana bukatarta a kusa da ita. Da kukan tai bachi da shi ta farka da asuba ma haka tai ta kuka sannan tai alwala bayan ta gama sallah asuba sai ta daga hannunta da zimmar yi ma mahaifiyarta addu'a sai kuma ta fashe da kuka, idan ta yi mata addu'ar za a amsa mata ko kuma aa?
Within a month Zainab ta koma abar tausayi bata iya cin komai sai yayan itatace da ruwa, jikinta ya koma very weak bata da wani kuzari, duk yadda Wasim yake son ta sake sai ta kasa bata komai sai yawan kallon mutane ko saurare abu mai wahala ta bude baki tai magana, abubuwa da yawa sun taru sun yi mata yawa, gashi a nan bata chat balle ta rage wasu abubuwan.

After some months...!!!
   
       **     **     **
As usual suna zaune akan wani dutse yana ta mata fira amman kwata kwata hankalinta ba ya gurin, ko saurarensa bata yi.

“Wasim... Idan na bar garin nan zaka rika kawo min ziyara ne?�

Kallonta yai jin yadda ta dauko wani zance na dabam, ba akan firar da suke ba.

“Zan biki dai mu tafi tare, ta ya zan kyale ki rayu inda baki da kowa kuma ke kadai?�

“Bana ka aikata wani laifi da zai saka yan'uwanka su ga laifinka, kai kana jindadin zama a garin nan, kuma kowa na ka yana nan be kamata ka bi son ranka ba ka aikata kuskure, bana fatar wani ya sake aikata wani kurkuren saboda ni�

“Idan har babu ke a garin nan, ai garin ba zai min dadi ba, ban ga amfanin zamana a nan ba matukar ba ki tare da ni�

Ta kalleshi

“Saboda me?�

Sai shi ma ya kalleta ido cikin ido

“Saboda ina son ki...�

Saurin mikewa tai tsaye tana maida numfashi tare da hade yawu da karfi, zuciyarta ta shiga bugawa tana rabawa sassan jikinta jini. Daman da dade da fahimtar hakan a kalamansa da yanayin yadda yake mu'amalantarta sai dai bata tsammaci haka daga bakinsa ba a yanzu, kuma a irin wannan lokacin. Shi ma mikewa yai tsaye yana kallonta.

“Kin ji abun wani iri ko? Ni ma haka na ji a lokacin da abun ya fara kamani...�

Ta yi shiru bata ce komai ba, shi maWaziri shirun yai can kuma yana kallon yadda hawaye ke sauko mata.

“Cancanta ba ko? Ko kuma na yi sauri ne? Ko kina duba alakar addininki da nawa ne?�

Hannu ta kai ta share hawayen ta da ta tafiya ba tare da kalleshi ba.

“Zan shiga ciki na huta�

Da kallo ya bita har ya daina hangota sannan ya sauke ajiyar zuciya, ya saka hannayensa biyu ya shafa kansa zuwa fuskarta, he can't lie to himself shi kansa ya san yana son Zainab kuma yana tausayinta fiye da yadda yake tausayin kansa, but still yana jin son Fadime har yanzu a ransa, maybe sooner or later zata fice mishi daga rayuwa da tunaninsa but for now idan ya tuna yana jin wani iri.

FALMATA POV.

Tana jingine jikin gadon shi kuma ya dora kansa saman karamin cikin nata yana sauraren hausar da take karanta masa.

“Ko wane jaririya ko jaririya su kan yi kuka a lokacin haihuwarsu da kuma kurciyarsu, sai dai kuka bayan girma kowa yana da dalilin yinsa
Da ace na wa kukan na mutuwa ne, da nafi kowa farinciki, ashe ba sai rai ya bar gangar jiki ake mutuwa ba, na tabbatar da mutuwa kala biyu ce, kaico ni Aminatu!
A yanzu kan na gasgata cewar na dade da mutuwa gangar jikin ce kawai a aje, kuma na yarda mace bata da gata, gurin yan'uwa da al'ummarta...�

Ta rufe babin tana juya bayan littafin tare da karanta sunansa tare da sunan marubuciyar.

“BAKAR WASIKA Na Khadeeja Candy, gaskiya daga ganin littafin nan zai yi abun tausayi�

Dan dagowa yai kadan ta kai hannunsa ya taba bakinta.

“Ko?�

Sai tai murmushi ta kalli agogo.

“Ka ce 9:30 zaka tafi gashi har 10 ya wuce fa�

Lumshe ido yai ya saka dayan hannunsa yana shafa wani bangare na cikinta

“Ban gaji da ganawa da dana ba ne shiyasa, let him meet his dad�

Ya karasa tare da kissing din cikin nata na 5 months.

“Kai ne oga kuma kai kake karya dokar kamfani�

“Zan fada musu madam ce ta hana ni fitowa tana ta ba ni.... �

Be karasa ba ta buge masa baki domin ta san abun da zai fada, ba kunyarta yake ba dirty talk any how yake mata, shi da fada ita da jin kunya. Sai ya tashi yana dariya tare da gyara suit dinsa.

“Me zan dawo miki da shi?�

“Bana son komai�

“Really....�

Ya kanne mata ido zai fara barin zance ta dauki fillo ta jefa masa, sai ya fice dakin da gudu yana kyalkyalar dariya, ita ma dariyar tai ta sauko da kafafuwanta kasa.

“I love you babyn Baby�

Ya fada da murya da zata iya jinsa, murmushi tai ta mike tsaye ta isa gurin window tana kallonsa yana daga mata hannu har ya shiga motar yana jefo mata kiss, ita kuma ta karba ta manna a kumatunta duka biyu.

_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number  09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
03/12/2021, 18:59 - 🤐🤐🤐🤐: *Khadeeja Candy*

*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*

Tumba ta fito da ido waje tana kallonsa, sai a yanzu da Naja take fadar sunansa ta gane ko waye duk da ba wani saninsa tai can sosai ba, sai dai tana ganin hotunansa da wakokinsa can sama sama.

“Sirleem dai mawaki�

Tumba ta fada tana nuna shi jikinta na rawa, kamar ta unkura ta tashi sai kuma ta saka tsabar mamaki da kuma rashin kafarta ta hadu.

“Allahu Abkar, to to to ni ban gane wannan abun ba, daman can shi ne yai siffar tsofi ko kuma babansa ne?�

“Shi ne dai�

Falmata ta amsa tana kallon Sirleem. Tumba ta girgiza kai tana kallonsa, domin a iya tunaninta sun aurawa Falmata tsoho ne kuma inda zata je ta sha wahala ashe gurin jindadi ta kaita ba tare da ta sani ba, daman can waya isa yai ma bawa abun da Allah be masa ba?

“Allahu Akbar Allahu Akbar, wani abu sai Allah, hakika abun da Allah ya rubutawa bawa be isa ya wuce shi ba, Wallahi yanzu kam na yarda�

Ta fada cikin kuka, tana kallon Baba da shigowar kenan rike da jakarsa ta zuwa kasuwa, Naja taje ta sauri ta karba saboda halayen kirkirin da ta kirkiro masa ganin ya fara wulakanta mahaifiyarta balle kuma ita, sai ya fisge abarsa ya karaso yana kallon Falmata.

“Wa na ke gani haka?�

Ya tambaya cike da far'a kamar ba shi ba, abun da Falmata ba tai tsammani ba daga gareshi.

“Ni ce Baba Sannu da zuwa�

Ta fada tare da kai hannu ta karbi jakar sai ya girgiza mata kai ya duka da kansa ya aje.

“Yanzu kuma Allah ya dauke miki wannan nauyin, dawainiya ta koma gurin mijinki�

Ya fada yana kallon yarsa cikin da farinciki da ya shafe shekaru be yi ba, Sirleem ya duka yana gaishe shi cike da girmawa tare da aje masa ledar turaren da ke hannunsa, kana ya kai hannu aljihunsa ya dauko kudo mai kauri ya saka a ciki ledar.

“Lafiya Kalau Wannan fa?�

“Wanda kuka aura min ne Baba�

Baba ya ja baya da sauri yana nuna Sirleem ganin zankadaden saurayi a gabansa bayan kuma shi ya san tsoho ya aura mata.

“Wannan? Ko dai idona ne ba su gani daidai kamar yaro na ke gani�

“Shi ne Baba�

Baba ya kalli Falmata wanda ta amsa masa cikin tsoro domin har yanzu be yarda ba.

“Ya akai ya zama yaro? duba dai�

Sirleem yayi murmushi tare da mikewa tsaye.

“Baba zan tsaya a waje Fatima za ta warware muku komai inshallahu�

Ya nufi kofa daga Tumba har Baba da Amaryar tasa kallonsa suke har ya fice.  Baba ya kalli Falmata.

“Ban gane ba, daman can ke kin san yaro ne?�

Sai ta girgiza kai ta fara bashi labarin farkon haduwarsu har zuwa aure da abubuwan da suka faru, tun Baba na tsaye har kai ya dauko kujera ya aza ya zauna yana sauraren Falmata, tana fada Tumba na kuka Naja ma ta rafka uban tagumi tana kallonta. Sai da ta kai aya sannan Baba ya share hawayen da suka cika masa ido yana fadin.

“Allah ya dubi zuciyarki da maraicinki, da kuma halayenki na kirki da kika rike shiyasa ya bude miki kadan faga falalarsa da kuma rahamarsa, na sani na cutar da ke iyakar cutarwa, kuma har ga Allah bana jin dadin abubuwan amman ya zamin kamar dole na musguna miki, mahaifiyarki ma na mata...�
Chapter 160 · 0% Book details