← Book details Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 141 OF 172

Sashe 141

Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta tambayi kanta tana kallon kayar cike da kyankyami, daukarsu tai ta je ta shiga bandakin Iya ta jefasu a ciki, sannan ta fito ta dauki tukunyar dake saman gadon tana dubawa. Tukunyar kasa ce da aka rufe bakinta da jan kyalle, sai da tai kamar ta bude kyalle ta gani ko miye a ciki sai wata zuciyar ta hana ta, daga tukunyar tai sama ta buga ta da kasan tile din iya karfinta. Take rukunyar ta watse kasa sai ga wani dan karamin maciji a ciki mai kai biyu. Wani ihun tsalle Zainab da daka tare da saka ihu ta ta ranta a ana kare sai waje. Mai gadin na ganinta ya mike tsaye da sauri yana tambayar ba'asi.

“Hajiya Lafiya?�

“Maciji dakin Iya�

“Maciji kuma ta ina ya bi�

“Oho je ka kashe shi dan Allah�

“Kai ai sai dai a kira mutane, ina ni ina kashe maciji wani ma aljani ne, ai shiyasa ake cewa kar mu yi saurin kasu su mu hada su da Allah su tafi�

Ko kamin ya gama maganar Zainab ta bude gate din ta fita daga gidan gaba daya, shi ma binta yai gurin neman mutanen da za su kashe macijin, ba su wahalar samun zaratan maza ba domin unguwar akwai manyan samari duk da kasancewarta sabuwar unguwa, har cikin gidan suka shiga Zainab ta tsaya daga waje tana fada musu inda dakin Iya yake, daga bakin kofa suka tsaya suna dubawa ba su koma ba hakan yasa suka fara yamutsa dakin ko za su ga inda macijin ya boya, tun suna yi da dan tsoro tsor har su kao ma dakin daidai ba su ga komai ba, hakan yasa suka fara tunanin ko ya fito falo ne duk da kasancewar falon babu wani guri da zai iya buya, amman a haka suka rika duba ko'ina har kasan kujerun, har cikin kicin ba su ga komai ba. Daya daga cikinsu ya zo yana tambayar Zainab.

“Amman ke kin ga macijin da idonki? Ko kuma tsoro dai kika ji?�

“Na ganshi Wallahi da idona�

“Abun mamaki ni ban ma ta inda zai iya shigowa ba, ko ban dakin ban ga wata hanya da zai iya biyowa ba�

“Wani lokacin a sabon gida ana samun irin haka gaskiya, domin iskokai suna haka, ko a gidansu Najeeb an yi musu haka kamin su samu zama lafiya�

Dayan ya fada, maganar da yai sai ya saka Zainab ta tuna cewar tukunyar da ta fashe ta tsafi ce wata kila macijin aljani ba macijin gaske ba.

“Sai dai idan iskan ne kamar yadda ka fada, amman dai ni na san na ga maciji gaskiya�

“To sai dai ayi ta addu'a Allah ya tsare gaba�

Amin din ma ta ji ba zata iya amsawa ba balle tace musuta gode, haka ta bi su da ido har suka fice sannan ta dawo kusa da dakin mai gadi ta zauna tana ta tunanin yadda zata koma cikin gidan.

********

Kusan kofar gate din gida biyu dake gefen na Baba Waziri dama da hagu fake suke manyan motoci na alfarma saboda rasuwar Maijidda, domin mutuwa mai ban tsaro duk wanda ya ji Maijidda ta rasu sai yayi mamaki domin ba a san ta yi ciwo ba sai idan na kusa da ita ya fada cewar ta kwana a asibiti da zazzabin taifot, hakan yasa har wandanda ba su san ta ba jin cewar budurwa ce suke zuwa gaisuwa, daman kuma Baba Waziri mutumen mutane ne, ta ko'ina zuwa ake masa gaisuwa ga familyn Hajiya Talatu da Hajiya Maryam su ma sai zuwa suke kamar an turosu, yan uwa abokai da suruku kai ma sai zuwa suke.
  Sai dai abun da kewa kowa tausayi shi ne Hajiya Talatu da ke ta shikar dariya ta fita hankali, sai kuma ta hada ta waka, duk wani abun da ta gani sai ta fade shi tace na jiya, hakan yasa aka sake maida ita a dakin aka rufe har sai da aka dawo daga kai Maijidda a gidanta na gaskiya, sannan Baba Waziri ya bada izinin a janyo mota a sakata a ciki a kaita asibiti.
Ana fitowa da ita duk abun da ta gani sai ta ce.

“Kai wando na njiya? Ke riga ta jiya? Takalmi na jiya? Hijabi na jiya? Kai mota ta jiya, fulawa ta jiya... Fadime ta jiya, Falmata ma ta jiya, Sardauna ma na jiya, Jarma ma na jiya, Shattima ma na jiya, ga Ammy ta jiya, ga Nana ma ta jiya, kai Jurry ma ta jiya, Mai Martaba na jiya, Hajiya Babba ta jiya...�

Komai ta gani sai ta fada ta ce na jiya, idan kuma bata fadi wani abun ba to zata kama sunanyen mutanen da suke ranta tana fada sai kuma ta bushe da dariya, sai dai babu wanda ya kawo komai a ransa kowa yana tunanin mutuwar Maijidda ne ya taba ta, haka aka sakata a mota aka nufi asibiti da ita yaranta sai kuke suke, ga mutuwar yar'uwa ga rashin lafiyar uwa.

Ana kiraye kirayen sallah la'asar mai napep ya sauke Iya gida na biyu kamin gidan Waziri, sai da ta fito sannan ta ba shi kudinshi tana jin jikinta na wani tsam tsam tsam kamar ba lafiya ba, habar zanenta ta kamo ta kai a idonta tana murzawa saboda ta samu idon yai ja ace ita ma ta yi kuka, domin abu ne mawuyaci ka ga maye na kuka, is hardly, suna da karfi halin bala'i da bushewar zuciya, sai da ta murza idon har ta ji ya dan soma mata ciwo sannan ta nufi gidan tana ta mitsika idon kamar munafuka.
  Haka ta ratsa cikin manyan motocin ta shiga cikin gidan, kai tsaye ta nufi bangaren Hajiya Talatu, tun a bakin gate din ta fara hango mutane a harabar wasu akan kujeru wasu akan tabarma wasu akan carpet, cikin karfin hali ta nufi gurin tana isa ta fara musu sallama tana kukan karya.

“Jama'a to sannu mu da wannan rashi�

Mutanen da ke kusa da ita suka masa mata duk da kasancewar ba kowa ya san ta ba a gurin, wadanda ta sani suka santa suna daga can ciki, sai da tai musu gaisuwa sannan ta mike tsaye tana kuka ta fara tsallaka mutane har ta isa bakin kofar falon ta shiga ciki tana fashewa da wani sabon kukan, can ta dago kai ta karewa mutanen da suke cikin falon kallo ka zata ga yaran Hajiya Talatu tai musu gaisuwa ko kuma wanda ta sani sai tai arba da abun da ba tai zato ba balle tsammani, tsaye tai cak lokaci daya ta daina kukan tana kallon ikon Allah. Maijidda take gani tsaye a kofar dakinta tana kallonta fuska babu annuri.

“Ahhh ahh ahh Jama'a ba Maijidda ce ta rasu ba?�

Iya ta tambaya da karfi tana kallon Maijidda da ita kadai take ganinta. Duk mutanen da ke kallon kallonta suke har Ammy dake zaune a one seater rike da carbi da kuma abokiyar zaman Hajiya Talatu wato Hajiya Maryam dake kusa da kujerar Ammy.

“Jama'a ba ku amsa ni ba, ba Maijidda ce ta rasu ba?�

Ta sake tambaya da karfi.

“Ita ce mana�

“To ya nake ganinta gata nan a tsaye tana kallona�

Iya ta fada tana nuna kofar dakin Maijidda, kusan duk wanda ke cikin falon sai da ya juya yana kallon kofar dakinta dake rufe babu wanda ke ganinta sai Iya, sai mutanen da ke kusa da ita suka fara matsawa suna mata kallon tsoro.

“Maijidda...�

Iya ta kira sunanta bata amsa ba, kuma bata motsa ba sai wani mugun kallo iya take ganin Maijidda na mata.

“Ke kika cinyenta kenan shiyasa kike ganinta, ku nemo maza su fitar mana da matar nan a tsareta can waje�

Ammy ta fada daga inda take zaune, da saurin mutanen da ke gabanta suka tashi domin aiwatar da abun da ta fada, Iya kam bata ma san wainar da Ammy take toyawa ba domin hankalinta na gurin zanenta da ta ji ana ja, tana duba kasa sai ta ga Luna Luma da Labib.

“Luma Luna Labib?�

Ta fada tana dukan kirjinta, sai zaro ido take jikinta nata rawa, kamar jira ake ta dago nan ma sai ta soma ganin yayan Ammy da ta cinye da kuma Jakadiya da wata Jekadiya da duk matan da ta ci na Shattima sai da ta fadi sunansa domin ganinsu take ido da ido suna mata mugun kallo.

“Miyasa na ke ta ganin mutanen da na cinye? Miyasa zan yi ta ganinsu bayam na riga na cinye kurwarsu? Ya haka wai haka? Lafiya dai? Me ke faruwa ne?�

A gabar da tai maganar ne mazan da Ammy tace a kira suka shigo sai Ammy ta daga musu hannu alamar su dakata, matan dake jikin kofar kam tuni wasu sun yi waje wasu kuma sun masa can nesa da inda take.

“Miyasa na ke ta ganin mutanen da na ci? Mai Martaba? To ai shi ban ci shi ba, na kurwarsa na nan aje ban cinye ba�

Ta fada tana kallon Mai Martaba dake tsaye gabanta.

“Jama'a ku min rai, ya haka wai?�

Tana kiran jama'a sai kowa ya kara nisantarta, Ammy kuma ta mike tsaye da sauri tana nuna ta.

“Mai Martaba fa kika ambata Iya? Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un ku kira min Wazari�

Duk wani abun da Ammy take fada da hayaniyar mutane bata jin ko daya gaba daya idonta baya nuna mata komai sai nutanen da ta ambata su kawai take gani. Wani irin zafi ta soma ji a jikinta kamar ana yanka mata reza a fata, can kuma ta soma jin kankarar maitar dake cikin cikinta ta soma motsawa tana mata yawo. Da farko bata ganin kowa yankan kawai take ji ta ko'ina har sai da tai magana.

“Yankana ake fa! A jikina ina jin yakan wuka�

Kamar jira ake tai magana sai ta soma ganin mutane da ta cinye suna yankanta ta ko'ina kamar an aikosu. Mutanen da ke falon kam kowa ya hade waje daya yana kallon yadda take tisge tufafin jikinta tartsatsin wuta na fita a jikinta kamar ana ƙira. Ƙofar Kitchen aka bude mutanen dake cikin falo suka samu fita ta gurin domin Iya na tsaye kusa da kofar falo ne.

SIRLEEM POV.
Chapter 141 · 0% Book details