← Book details Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 172

Sashe 102

Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba karamin mamaki Zainab tai ba, sai dai ta alakanta hakan ta tausayin Fadime, domin bata sa ran ya santa. Sai da Fadime ta sha five alive ta ji sanyi har cikin kai da ruhu ta fara masa addu'a, murya kasa kasa gudun kar Zainab dake kicin ta ji ta

“Na gode Allah ya saka maka da alheri, ya rabaka da iyayenka lafiya, kuma Allah ya tsare ka daga sherin mayu, da zuwa garin su Wasim, duk wata bakar mata ce ta jamin min, ta zo daga can wani gari can nesa wai yola tasa na rakata a can garin, gashi nan ta tafi ta bar ni da bala'i, gashi nn na makance kuma an kawo ni gurin su mayu, Allah ya isa, da wani jikinta kamar yar tsana, wai hoto zata dauka, muguwa banzar Allah ya isa...�

Ta karasa da kuka. Zainab ta hade wani numfashi da karfi tsabar bakinciki yasa shi kin wucewa har sai da ya dawo mata ta fitar da shi, mikewa tai tsaye da zimmar marin Fadime sai Shattima ya watsa mata wani mugun kallo, na me zaki yi? Hakan yasa tai tsaye cak tana hucin da bata san ta ina yake zuwa mata ba.

“That's mean ke ce dalilin makantarta, and you're treated her badly�

“No ba ni ce silar makantarta ba she's lie, bata da hankali wannan yarinyar kuma kanta rawa yake�

Zainab ta fada tana kokarin kare kanta, uffan Shattima be sake ce mata ba, irin yadda yake kallonta kadai ya isa ya sanar da ita irin bacin ran dake cikin idonsa, and the second thing he hate is argue, ta kuma san haka.

“Ka yi hakuri ka gafarce�

Ta furta cikin muryar dake nuna tana daf fa fashewa da kuka, domin numfashinta har wani sama yake yana kasa. Fadime na jin hakan ta aje kofin lemu ta kama kafar Shattima ta rike gam.

“Dan Allah dan Annabi karka bar ni nan, yauna shiga uku na, Wallahi yau farfesuna za su yi...�

Ta fashe da kuka, ko ba a fada mata ba ta san Zainab ta ji abun da ta fada na zancen maita, domin shi kawai take tunanin zai bata mata rai, ba zancen wacan matar ba data raka zuwa garinsu Wasim, kuma ta san ba za su raga mata ba, baka taba maye ba ma ya ka kare balle kuma ka taba, abu na mu dan kura da kallabin tsire😂

    A gafarce ni jiya ban samu na yi ba, bana jin dadi ne yau ma karfin hali ne, fatar za a min afuwa kamar yadda aka saba. Allah kara mana lafiya da abun da lafiya zata ci, ya tsare mu daga dukanin abun cutarwa.

_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number  09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
03/12/2021, 18:54 - 🤐🤐🤐🤐: *Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*

Yadda ta rike masa kafa sai ka rantse da Allah idan ta saki kafar wani abun ne zai sameta, ba zuciyarta ba har jikinta ba bakinta mai sakin zance rawa yake. A take ta fara ruwan hawaye da majina, yana kokarin kwace kafarsa ta kai hancinta jikin wandonsa ta goge majinar.

“Ke Malama kafata ce kika share majina da ita�

Ta fada yana kallonta for the first time ta masa abun da ba a taba masa ba.

“To ina ruwana ko ba kai ka barni ina ta zuba ba, ba zaka fada min kace gata nan ta zo ba, kuma ka min alama kut�

Ta yi kwafa domin ta fi jin haushinsa yanzu fiye da kowa. Da me zan miki alama tun da ba gani kike ba? Ya furta a aransa a fili kuma sai ya kai hannunsa ya saka karfi ya banbanre hannayenta, wani irin hargagi tai kamar kyanwa ta kara kame kafar ta rike gam, daker ya yunkura ya mike tsaye, tana jinsa tsaye ita ta mike tsaye tana dafa shi har ta isa daidai kunkurunsa ta rike gam kamar ta samu ice, ta dora kafarta ta dama akan kafarsa ta hagu, ta hagun ta dorata a kafarsa ta dama, ta yadda idan ya daga zai yi tafiya kafafuwanta na saman nashi.

“Wallahi dole ne ka tafi da ni, ba zan zauna ba, ai kai ka bar ni ita ta zuba, baka ko min alama ba, duk ta ji komai, shikenan sai na zauna su cinye ni, ga makanta ga mutuwa aa Wallahi ba zan yarda ba�

Ta fada har da girgiza kai tana kara rike shi, be san lokacin da murmushi yai ma kansa muhalli a fuskarsa ba, murmushin da ya bayyana hakoransa.

“Ina zan kai ki?�

“Ka kai ni garinmu�

“Garinku ba nan kusa ba ne�

“To ka kai ni gidanku gobe sai ka kai ni garinku, ai gidan ku ba mayu ko?�

Yayi shiru sai kallonta yake cike da nishadi. Ya cira kafar daya ya taka tana saman kafafuwansa.

“To sauka�

“Aa Wallahi ba zan sauka kana ganina haka idan na sauka wayo zaka min, sai dai mu tafi a haka�

“Ya za yi na fita dake haka? Kin san waye ni kuwa?�

“Ina ruwana da kai ko waye, kai ka san wacece ni? Hmmm�

Ta kara kankameshi, seriously be san yadda zai yi tafiya da ita ba a haka kafafuwanta saman na shi. And what he hate the most is ka take shi amman ji yadda ta dora duka kafafuwanta saman na shi.

“Ba zan iya tafiya a haka ba�

Yadda yake amsa mata kadai abun mamaki a gurinsa, domin ya tabbatar da ba ita ba ce ta yanzu ya dauke ke ko waye da mari. Jin ya fadi haka yasa tayi kasa da hannunta ta kama rigarsa ta shadda ta rike gam, sannan ta sauka kan kafafuwan nasa.

“To mu tafi...�

Sai da ya kalli rikon da tai masa sannan ya kalleta.

“Ban san inda zan kai ki ba Wallahi�

“Ko ma ina ne ni ka kai ni�

Ya hade yawu a hankali sannan ya fara takawa tana rike da shi kamar wanda yai mata sata gefen shaddar data rika har ta tamuke. Yadda ya fito cikin falon ba zaka ce shine ya shiga dazun fuska a hade ba, domin a yanzu murmushi da nishadin da be san ta ina yake zuwa masa ba ya wanke masa fuska da zuciya. Har gaban motar ya karasa da ita ya bude front seat.

“To shiga ki zauna�

“Aa idan na shiga wai wata motar ce zaka saka ni sai ka shiga motarka ka tafi ka barni�

Ya sake yin murmushi.

“No motata ce�

“Ce Wallahi?�

Ya zaro ido kamar tana ganinsa, a rayuwarsa ba a taba bashi rantsuwa ba. Shiru yai mata a gurin sai kallon kyakyawar fuskarta yake. Jin shiru yayi yawa yasa ta kai dayan hannunta tana taba kirjinsa.

“Kana nan ai�

“Idan ba zaki shiga ba, sake ni na tafi�

“Sai ka rantse�

“Ba zan rantse ba�

“Ni kuma ba zan sake ka ba�

Ta kara gyara tsayuwa yadda zata ji dadi dadewa a gurin. Kansa ya daga sama ya sauke can kuma ya kalli gate yana mamakin yadda akai be dauke ta da mari ba tun dazun.

“Sai dai mu yi ta tsayuwa a nan har dare, Allah yasa ma ayi ruwa�

Ya wara idonsa yana kallonta like serious ya fada a ransa, ya sake yin murmushi.

“Okay i swear�

“Ka ce Wallahi Motata ce kuma ba zan tafi na barki ba?�

Ya kara zare ido, wai yarinyar nan kuwa ta san waye shi? How on earth zata saka shi rantsuwa again kamar kotu?

“Ka ce�

Ya mata shiru kamar shekararen ice.

“Ya ma sunanki?�

“Fadime�

“Okay, ki tsaya mu yi maganar hankali ni ba zan sake rantse miki ba, idan kin yarda da ki ki shiga kawai bana karya, kuma har garinku zai maida ke saboda iyayenki suna can suna nemanki idan ba su gan ki ba zasu saka ni kotu�

“A ina suka ganka?�

Ta ina zai bata labarin suna tsaye a rana?

“Shiga mota�

“Sai ka rantse kamar yadda na ce ka fada sannan�

“Wallahi motata ce kuma ba zan barki ba�

Tana jin ya fadi hakan ta sake shi ta lalaba ta shiga motar, shi kuma ya rufe yana murmushi sannan ya zagaya dayan side din. Kamin ya zagayo ya shiga motar har ta tsawwala, sai ta taji ya shiga ya zauna har yayi ma motar key sannan hankalinta ya kwanta.

“Kika sani ko ni ma maye ne?�

Ya fada yana murmushi tare da kai hannunsa ya kara gudun ac motar. Cak Fadime ta tsaya.

“Kuma fa?�

Take wani tsoron ya kamata, nan da nan sai kuka kamar ba ita ce ta gama rigima ba yanzu. Da gangan Shattima ya kyaleta tana ta rusar kuka a motar har sai da suka bar gidan suka hau babban titi.

“Wasa nake miki�

Ta ki daina kukan, shi kuma be fasa murmushin daya kusan zame masa dariya ba.

“Haba wasa fa nake�

“Rantse to�

Ta fada cikin kuka, sai ya kalli fuskarta.

“Me zan ce?�

“Ka ce Wallahi wasa na ke�

“Kina ta saka ni rantsuwa fa ba a taba sani haka ba�
Chapter 102 · 0% Book details