← Book details Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 172

Sashe 28

Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai kawai ya kada mata daman kuma be jin zai iya kara ce mata wani abu tun da sai an yi magana da karfi zata ji, sai ya sara mata ya nufi motarsa ya bude ya shiga masu aikin daukarsa a hoto suna ta yi, da kallo ta bishi har ya tashi motar ya hau titi. Sannan ta mike tsaye ta saka hullar cikin hijabinta tana jin wani irin farinciki a ranta marar misaltuwa. Gaba daya ta manta da wani tunani da bacin rai, sai laleben hular dake kamshin turarensa take tana jan numfashi tana saukewa, yadda zata labartawa yan islamiyarsu da kawarta labarin yadda ta ga Sirleem yau kawai take tunani, har ta isa masarautar murmushi be gushe daga fuskarta ba, ji take kamar yanzu komai ya faru. Zancen wani haduwa da Iya da fargaban da take samunta idan zata shigo gidan duk ta manta sai murmushi kawai take tana jindadi a ranta. Door bell ta danna sannan ta samu guri ta zauna a gurin tana jiran a bude mata kofar, after like ten minutes aka bude kofar.
Mikewa tai tsaye sai tai arba da Iya hakan kuma ba karamin fadar mata da gaba yai ba, a take murmushin fuskarta ya gushe, Iya sai kallonta take irin kallon nan da ke nuna mata komai na jikinta har yadda jini yake gudana a jijiyarta, Falmata ta yi kasa da kanta ta saka cewa Iya ina kwana balle tace ta bata hanya ta wuce. Ba kallon bakinciki abun da ya faru kawai take mata ba har da na kurwarka dake ta yawa a saman kanta kamar fara, irin ta ce mai wuyar kamu, kurwar da ke yin kasa mai kamar hawainiya ita tafi saukin kamu sai kuma wacce take yawo a kasan kafafuwan mutum, wanda wani lokacin kasan kafafuwan mayu suke kallo su kama kurwar mutum. Akwai wance take kamar tantabara ita ma tana da wuyar kamu sai dai bata kai mai kamar fara ba wacce ke fira.

A take jikin Falmata ya fara wani tsamtsamtsam wanda hakan ke bata cewar ba mutumen arziki bace, a take ta fara karanta addu'o'in da ta iya, sai iya ta kauce mata da sauri tana mata alama da ta shigo da hannunta. Ita kuma tai saurin ficewa daga falon, sai da Falmata ta juya ta kalli ficewarta sannan ta juyo ta nufi hanyar dakinsu yan uku, tana ta mamakin yadda Iya ta rikirice saboda Addu'ar da tai.

‘Idan zan sake zuwa sai na samu furen tumfafiya na hada da goro na zauna�

Ta fada a ranta dan ta taba jin Tumba na fadar indai mutum yai haka yai arba da maye ba zai iya kallonsa ba. Yau ma bata tararda yaran ba, daman haka ya fi mata dan bata son tai wani abu ace ta yi ba daidai ba. For the first time yau tana ta ji tana sha'awar yin shara tana kirar suratul Baqara, surar da idan ka karanta shaidane sai yayi wata daya kamin ya sake shigowa gidanka, idan kuma ka karanta ayoyi goma na farkon surar a kullum, to kana cikin tsaron Allah babu wani abun da zai same ka, maita ko aljani ko wani shari kuma zaka wuni cikin nishadi.
Daga alif lam min ta fara karatun cikin muryarsa mai dadi da kwantar da hankali ga saukarda natsuwa kasancewar qur'ane take karatu, a yanayin yadda ta kare a kirar ma sai ka dauka wata balarabiya ce ba fulani ba. Har ta yi aikin ta gama karatunta take sai da ta gyara komai tsaf sannan ta fito ta janyo dakin ta rufe ta fito daga corridor, bata wani tsaya kula wadanda suke falon ba ta sa kai zata fice, sai Ammy ta kira wata mata dake zaune kasa tana kallon tv.

“Salamatu kira yarinyar can�

Jikin Salamatu na rawa ta kwalawa Falmata kira tana mikewa tsaye ta nufi inda take.

“Ke...

Falmata ta juyo a tsorace gabanta na faduwa, ita dai tsoron ta kar ace ta yi wani abu.

“Na'am�

Ta taho da sauri ta zube kasa ta gaishe da Ammy kamar yadda ta lura da mutanen gidan na yi, ko daga kai ta kalli Ammy bata yi saboda tsoron irin an talaka a gaban sarki. Sai ta karaso sannan Ammy ta yi murmushi kadan tana kallonta cike da burgewa, yadda ta ji tana karatun ya matukar burgeta ga natsuwa da kuzari aiki da take ganin kamar yarinyar tana da shi, ina ma ace Nanarta ce a haka.

“Duk abun da na ce ki rada mata a kunne�

“To ran ki ya dade�

Salamatu ta amsa, sai Ammy ta maida dubanta gurin tv kamar ba zata ce komai ba, ba dan komai ba sai dan isa da kasaita irin ta matan sarakuna musamman idan suna cikin talakawa. Falmata kan cikinta sai kadawa yake tana ta tunanin abun da tai ba daidai ba.

“Ya sunanki?�

Salamatu ta rada mata, sai Falmata tai saurin amsawa muryarta har rawa take kana jinta kasan tana daf da fashewa da kuka.

“Falmata�

“Shekarunki nawa?�

“Cikin ta sha bakwai�

“Kina zuwa makaranta?�

“Eh islamiya, bana boko�

“Saboda me?�

“Ba a saka mu ba�

Ko wace tambaya sai Ammy ta bada tazara take yinta kamar mai tunanin wace tambaya zata mata ko kuma mai hutawa sannan yai wata tambayar.
Da hannu Ammy tai mata alama da ta tashi ta tafi, daman can Falmata shi take jira sai ta tashi da sauri ta fice daga katon falon jikinta har rawa yake.
Sai da ta fice sannan Ammy ta kalli Salamatu.

“Tashi ki nemo min Gambo�

“To ranki ya dade Allah ya kara miki lafiya da imani�

Da sauri Salamatu ta fice daga falon, ba a dauki lokaci ba sai ga Gambo ta shigo ta zube kasa ta kwashi gaisuwa.

“Gambo yarinyar nan da kika kawo tana da halin kwarai ko?�

“Wallahi ranki ya dade ba zan dauko sheri na kawo a cikin iyalanki ba, ina wace ni, Wallahi sai da na duba na dubo na zabo sannan na dauko ta, kaf a unguwar nan ba yarinya matashi kamar ita wacce tai kunya da tarbiyar Falmata, Allah ya mata natsuwa da kamala, ga ilmin kamar ruwa, sai dai ace ba tai boko ba amman na muhammadiya kam babu abun da bata sani ba�

Ammy ta yi shiru har na wani lokaci sannan ta ce.

“Ma-sha-Allah, ina son ki fadawa iyayenta za ta rika wuni nan tana rainon su Labib�

“To ranki ya dade, yadda kika ce haka za ayi, yanzu ma daga nan can zanje na isar musu da sakon Hajiya, Allah ya kara miki imani�

Da hannu Ammy tai mata alama da ta tashi ta tafi, sai ta mike da sauri ta fice.

***  ***   ***

Hajiya ta sauke ajiyar zuciya bayan Jarma ya gama yi mata bayanin salin inda garin yake, da kuma abokinsa da zai musu jaroganci.

“Jarma ina tunanin kai ya kamata ka fara zuwa, domin kai ka fada masa matsalar ta yarka ce, ganina zai iya gano wani abu, sannan ba zai yiyu na shirya tafiya a yanzu ba, kai ma kuma a nemeka a rasa cikin masarautar nan, za a fara zarginmu�

Jarma ya jinjina kai.

“Na yi wannan tunanin Hajiya, sai dai jin cewar ba a musu sako sai dai mutum yaje da kansa yasa dole ne mu yi tafiyar a tare�

Hajiya ta yi shiru na wani lokaci kamin ta kalleshi ta ce.

“Zuwana kamar zuwanka ne Jarma, domin bukatar da nake da ita ita ce a kanka, idan ka je ka ga guri sai mu shirya wata tafiyar daga ni sai kai mu tafi ba tare da abokin ka ba�

“Abokina amintaccena ne Hajiya karki samu damuwa da shi�

“Bana saurin yarda da mutane kai ma ka sani, kuma ka san Shattima a can yake aiki, zai iya ganinmu�

“Haba Hajiya ya za ayi mu yi saken da Shattima zai gan mu sai kace wasu yara dai?�

“Baka san gayyadar da Zainabu ta tara ba ne, shi kanshi ba dan sa ido ne lamurran gidan nan�

“Zan fara zuwan kamar yadda kika bukata, daman can na yi tunanin fara zuwa ni kadai�

“Haka yayi, ka karanta musu komai idan ka je, idan zai yiyu ka shirya tafiyar nan a cikin satin nan�

“Assabar din nan zan tafi In-Sha-Allah, Allah dai ya bamu nasara�

“Amin�

Hajiya ta amsa tana kashe ido daya. Hannunta ta kai ta dauko wayarta ta soma neman number Talba, ta san ko yana a gari ba saba shigowa ya gaishe ta ba kamar Sirleem amman rashin ganinsa kwana biyu yasa ta damu. Ring biyu ya daga, sai da suka gaisa sannan ta ce.

“Talba ina ka shiga kwana biyu?�

“Ina nan�

“Kwana biyu baka saka mahaifiyarka a ido ba, kuma hankalinka kwance�

“Hajiya idan wani abu ya same ki ai dole a sanar da ni, na san lafiyarki kalau ai�

“Kana da labarin dai za a daura auren Teema ko?�

“Yeah na sani�

“To kai nake son ka wakilci mai martaba�

Ya zare ido kamar tana gansa.

“Wane irin ni kuma Hajiya, kin san ban saba shiga irin abubuwan nan ba, kuma dai ga Baba Waziri ga Baba Jarma ga Shattima sai ace sai ni?�

“Yanzu ina son ka fara shiga, duniya ta san da kai, wannan umarni ne ba shawara ba, idan ka shigo zan mu tattauna akai ya kamata ka fara mika hannu ana yin komai da kai�

“Gaskiya Hajiya ba zan iya ba Wallahi ban saba wannan ba�

“Shiyasa na ke son ka saba din ai�

Ta kashe wayar bata ma tsaya jiran abunda zai fada ba. Idan ba tai da karfi ba, ba zata samu abun da take so ba, a komai sai Ammy ta tura danta ko'ina shi ake gani ita ba a san da nata dan ba, tana ganin yanzu ya kamata ta zage dange tai da gaske kar a mata yar gidan jiya.
03/12/2021, 08:32 - 🤐🤐🤐🤐: *🐄🐄 FULANI 🐄🐄*

By Khadeeja Candy

*14*
Chapter 28 · 0% Book details