Sashe 30
Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Ba wai ana nufi kwan nan biyu ba, kwana biyu na malam bahaushe ake magana Hajiya�
“Wai wacece ke da kike fada min wannan maganar? Banza a banza kashi a masai? Shattima ya fi ni iko da Nana ne ko kuma me? Ke kina kara nunawa Ammy wannan bakin abun na ki na wani yan uba, mu yaran gidan mu ba su san wannan ba, kowata da yai nan ma ai bata mata tarbiya za ayi�
Hajiya Maryam ta yi dariya
“Hajiya kenan, ke kuma abun da kike gyara mata tarbiya ne? Shattima ai ya san da ke a gidan amman ya dauke ta ya kawo ta gurin kanen ubanta kuma be ce a kawo ta ko'ina ba sai a nan bangarena, har waya sai da ya daga ya kirani yace na kula masa da Nana, kin ga kuwa dan gyara aka kawo ta ba baci ba�
“Eh Lallai Hajiya Maryam, ni kike fadawa magana haka? Yanzu da Ammy ce za ki mata haka? A a sai ni da nake kishiyarta ko? Ba komai komai yana da lokaci ai wata rana sai labari, Ke Zarah tashi ki kira min Nana�
Hajiya Balki ta karasa tana kallon karamar yar Hajiya Maryam. Zarah ta tashi ta fita daga falon zuwa bangaren da dakunansu suke, ta kira Nana suka fito tare, Hajiya na ganinta ta mike tsaye.
“Idan Waziri ya zo ki ce masa na dauki yata, idan kuma ban isa da ita ba, sai ya zo ya dauko ta�
Haka ta saka Nana na gaba suka fice daga falon, tun kan su karaso driver ya bude musu baya, Hajiya ta shiga Nana ma ta zagaya ta shiga ko tsinke bata dauka ba a gidan. Sai da direban yaja motar suka fita daga gidan sannan Nana ta rungume Hajiya a cikin motar.
“Na gode Hajiya�
Hajiya ta yi murmushi.
“Anything for my daughter�
“Ke ba kamar Ammy kike ba kina so na sosai kuma kina min duk abunda nake so i love you so much Hajiya�
“I love you too Daughter�
“Kuma Hajiya ina son sabon driver, bana son school bus tana kai ni makaranta, shi zai rika kai ni islamiya da boko ma, tun da can na fadawa Ammy ta dauka min sabon driver ta ki�
“Karki damu zan daukar miki sabon driver, duk abunda kike so shi zan miki daughter zan saka a samo sabon driver ya rika kai duk inda kike so�
Ta dago da sauri tana kallon Hajiya cikin wani irin jindadi marar misaltuwa.
“Akwai wanda yai min magana Hajiya, yace zai iya kuma yana so�
“To ki nemo shi daga gobe zai fara tukaki ki bashi keys din motar kuma ki fada masa yadda ake biyan wacan driver ni zan din ga biyansa every month�
Da sauri Nana ta kara rumgume ta ta kwanta jikinta tana jin wani son ta fiye da Ammy.
*** *** ***
Kofar wani gidan ta kwankwasa aka bude mata, matashiyar matar ta leko.
“Hajiya kuna siyen danyen man shanu?�
“A a muna da Allah bada sa'a�
“To amin�
Ta amsa tana lasar bakinta, a nan ta janyo kurwarta ta warware zanenta ta saka yar tsokar ta kulle, ta maida zanen ta daure ta yi saurin bari wajen har da hadawa da gudun, duk da bata matsi kurwar ba ta ta ga matar tana da aljanu kuma za su iya tashi, ko da yake na Amo sun fi na matar karfi.
Cikin unguwar Nasara ta shigo gidan data saba kawo musu danyen manshanu suna siye, tana buga gate din mai gadin ya bude mata, ta gaishe shi da far'arta tana kallon kurwarsa dake kasan kafafuwansa.
Nisa kai tai cikin gidan har ta isa bakin kofar falon da ke bude ta zauna kasa tana sauraren hirar da Hajiyar ke yi da kanenta yaranta su ka zo da gudu suka rumgume Amo.
“Oyoyo Amo ta zo Oyoyo�
Ta muku ya zaunar da su saman kafafuwanta tana dariya tana musu wasa.
“Shi fa be ma san da maganar ba, kuma ita Ammy tace kar na bari ya ji sai komai ya kama�
“To sai matsalar wannan abun da ke tare da shi�
“To ai ni ma shine, kar a aura masa yar mutane ta mutu, shi kansa yanzu abun da yake tsoro kenan shiyasa ya cire ransa daga auren ma�
“Sai dai idan ba za a fada ba�
“Idan kuma ba a fada ba, ai an cutar da yar mutane, kuma ita yanzu Ammy tace ta damka min ragamar komai, wai ko a nan Katsina din ne su zauna tukunan�
“Ai kam samun mata yanzu ga Shattima aiki ne, ga kudi ga kyau ga ilmi ga sarauta amman fa ana tsoron mutuwa�
Ra'ees ya shafa kansa cike da damuwa dan wannan aikin da Ammy ta bashi ba karamin aiki ba ne. Karamar yar Hajiyar ta shigo tana tsalle.
“Momy ga Amo can ta zo�
“To yar gidan Amo�
Ta fada tana dariya sannan ta mike tsaye ta fito waje suka gaisa da Amo. Sai da ta bude manshanun suka fara ciki ta siye wanda zata siye sannan Amo tace.
“Hajiya na ji kuna neman mata�
Hajiya ta yi dariya.
“Muna nema kan amman ai shi mai son matar ne da matsala�
A nan Hajiya ta labarta mata waye Shattima. Sai Amo tace.
“Kai duk canfi ne Hajiya, ku bar wannan maganar ma, karku sake fadin haka abun da Allah ya kawo ai shi yake kasancewa, ni da za ku yi shiru da bakinku akwai yar da nake riko sai a bashi ita, indai za a saka ni gaba ayi komai�
“Aiko da kin kyauta mana, zancen fadin haka daga yanxu ma mun daina�
Amo ta yi dariya tana kallon sabon cikin Hajiya take dauke da shi, da be wuce sati biyu ba, amman ita tana ganinsa da idonta hudu na maita. A nan ta fada musu addirenshi da wanda za a nema idan aje.
“Indai da gaske suke suka je Malam zai bashi aurenta, dan shi kanshi neman mijin da zai aureta yake, shekara goma sha 16 babu wanda ya taba tambayar amrenta�
Har lokacin tana kallon cikin, wata zuciyar na ce mata ta taba wata na cewa ta bari sai ya kara kwari. Bayan sun gama yanke komai ta siye manshanun ta sallame ta taso tana ta jindadin indai ta zama jagaba ita ce zata samu kudin komai ai.
FADIME POV.
A yadda ta kabartawa Inna labarin cewa tai wani ta ji a jikinta akwai wata wuta tana binta kuma wutar maita ce, bata son ta fadawa Inna gaskiya dan kar ta mata fada ko kuma ta hana ta zuwa gurin kiwon.
“Dubi kike ne da kika fara ne Fulani?�
“Minene Dubi Inna?�
“Bokaye suke yinsa su duba hannun mutu ko idonsa su fada masa abu, ana basu kudi�
Gyada kai Fulani tai tana dariya a ranta tana tunanin ta samu sana'a.
“To yanzu idan nai miki Inna za ki ba ni kudi ko?�
Inna ta watsa mata harara.
“Bari Malam ya ji da wannan dabi'ar sai ya zaneki kin san dai babanki malami ne ko?�
‘To ni ina ruwana da wata malantarshi�
Ta fada a ranta tana turo baki gaba, a dayan bangaren kuma tana ayyana irin kudin da zata samu idan tai wannan sana'ar. Waya sani ma ko aljani ne ya zo ya taimaka mata?
Bayan kwana biyu Inna da Fadime na zauna waje, Amo ta fito daga bukkatar tana fadin.
“Inna Fadime na yi ma Fadime miji�
Kamin Inna tace komai Fadime ta nufe ta da far'a tana dariya, kwatakwata a rayuwarta babu wanda ya taba zuwa yace yana sonta sai yau.
“Da gaske? Ina miji?�
“Ke arrr Fulani babu kunya�
Inna ta fada cike da jin haushin yadda Fadime take rawar jiki. Fadime ta rufe ido ta dawo da gudu ta rufe kanta jikin Inna sai a lokacin take jin kunya wai.
Amo ta zauna tana dariya ta labartawa Inna.
“A can bunni inda nake kai mansanu, samarayin gidan abokaine yake neman mata nace ga Fadime nan tun ita yar boko ce kuma tana da kyau ba kamar hajjo ba�
Inna ta jidadi sosai cikin ranta duk da tasan Amo ba zata kawo mata abun alheri ba, amman jin yau ana son yarta yasa ta jidadi abun da ba a taba ba ko da wasa.
“Ai na ce su zo su yi magana da Malam indai da gaske suke.�
Amo ta fada sai Fadime ta ce
“Allah yasa su zo Allah ya kawo su lafiya, yana da kyau?�
Inna ta rafka uban tagumi tana kallonta, Amo kuma ta saka dariya domin ita dadin rashin kunyar da Fadime take, take ji domin ba al'adar fulani ba ce. Ganin yadda Inna take hararta yasa ta fita daga gidan da gudu tana dariya, kai tsaye ta nufi gidansu Ma'u ta fada labari, tana isa ta tarardar Ma'u na yi ma wasu mutane kwatancen wani gari da ke yamma da su. Mutum uku ne da wata dalleliyar mota daya na tuki daya a baya daya kuma a mazaunin gaba. Gurin madubin motar Fadime ta je tana duba fuskarta kamin ta fara shafa motar, wanda hakan ya ba Jarma tsoro yana ganin kamar lekensa take ta ga ko waye ne, kamin a gama musu kwatance su kama hanya duk ya takura.
“Kiyaye....�
Ta fada tana daga musu hannu kamar ta san su, ta bi motar da kallo sai da ta daina hangota sannan ta talkamo kawarta ta fara bata labari.
*** *** ***
Jarma yaja tsaki cike da jin haushi.
“Wai yanzu kai Saminu ka san baka san gari ba kasa mu ka kamo hanya haka?
Saminu dake gaban mota ya juyo yana kallon abokinsa.
“A a fa na san hanya, garin da shi jafaru yake zuwa ci rani ne ban sani ba, amman muna isa muka ce gidan liman ance babu wanda be san shi ba a garin, ka ga sai mu tambayi Jafarun sai ya shige mana gaba mu shiga cikin garin tun da shi ya san yan garin da yawa kuma yana yi wa mutane jagoranci amman mu kai tsaye ai ba za mu shiga garin ba�