Sashe 159
Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel · about 8 min read
Suna sauka airport matoci har biyu suka zo daukarsu, a iya tunaninta masarautar za a sauke su sai ta ga an nufi wata unguwar da bata sani ba da su, ba dan hoton Baba Waziri da ta gani a falon Hajiya Maryam ba wato uwargidan da tace ba a yola take ba, domin bata san kowa ba a cikin iyalan gidan, daga Hajiya Maryam har yaransa da kuma yaran Hajiya Talatu da kulawarsu ta dawo karkashin Hajiya Maryam, sakamakon haukacewar da mahaifiyarsu tai wato Hajiya Talatu.
Sun samu tarba ta musamman daga gurin Hajiya Mairo, sannan ta kaisu masaukinsu, a nan su ka yi karo ta kalolin abinci da aka jera musu, ga lafiyayyen gurin bachi da bandaki mai kyau, plasma da ac suna kunne suna aikinsu, ba laifi Fadime ta natsu saboda kunyar da take ji, sai dai ta taji muryar Namiji sai tai ta saurare tana son taji ko yana tare da Shattima ne. Washe garin ranar da suka iso da safe Baba Waziri ya shigo ya gaisa da su, kuma ya isar musu da sakon gaisuwar Ammy da Mai Martaba. Two days after aka canjawa Fadime daki, aka kaita wani dakin na dabam, baka jin komai sai kamshi, gadonta da take bachi kamar an yi ambaliyar turare, kullum da safe mai aikin Hajiya Mairo zata shigo mata ta turare tai n jiki da na tsuguno da kuma na wanka, order Hajiya Mairo tai mata tun daga Zamfara har yola, Yar gidan Mai Fata tai mata gadin kayanyaki kala kala tun daga na gyara jiki har na turaruka da kuma kayan mata, hadi tai mata na musamman na Amaren, kullum mai dilka zata zo tana gyara mata jiki, Fadime bata fara kuka ba sai da aka fara mata shafa mata halawa, ta soma jin zafi tana ganin yadda ake fitar mata da gashin jiki kamar ba a sonta. Ba dan tana jin kunyar Hajiya Mairo ba da babu yadda za ayi ta kyale ana zaluntarta da sunan gyara, yanayin turaren da ake saka mata ana ana turara mata a jki da tufafi da kuma dakinta sai kamshi ya soma bin jikinta ta zarar ta wuce zaka ji kamshi yana tashi, farinta ya kara fitowa ga dogon hancinta gwanin sha'awa sai dai ta yi rama saboda fargabar gyaran jikin da ake mata kullum da shi take kwana take tashi a ranta, domin har ga Allah abun ya isheta sai dai babu yadda ta iya.
A zatonta haka gyara jikin ne kawai a iya jikinta abun zai tsaya, sai gashi ta ga ta Hajiya Mairo da kanta take saka ta gaba tana bata hade haden da aka karbo mata daga Zamfara, duk wanda Fadime ta sha ta ji a shi da dadi sai ta aje mai zakin sai ta shanye duka.
“Wannan naman duka za ki cinye�
“To�
Ta karba ta dan ci kadan sai ta ji shi kamar ba naman kaza ba, saboda hadin maganin da ya sha.
“Inna tace na daina shan abu mai daci yana da illa ga lafiya�
Hajiya Mairo ta yi murmushi.
“Wannan ba wata illa da zai miki sai dai ya kara miki lafiya, ki yi kokari ki cinye�
“To�
Ta saka bowl din a gabanta kamar ci zatai da gaske, ganin hakan yasa Hajiya Mairo ta fice daga dakin, Fadime na ganin ta fita ta tashi ta shiga bandakin ta kunna fanfon ta wanke kazar ta dawo da ita ta ci ta a haka ba tare da magani ba.
“Haka kawai sai a rika bawa mutum abubuwa cikin mutum ma sai ya lalace�
Ta fada tana turo baki, duk yadda ta zo ta cinye kazar sai ta kasa saboda babbar kaza ce kuma Hajiya Mairo ta riga ta cika mata ciki da garin magani masu kyau.
Kwantawa tai saman gadon tana ta nishi kamar mai nakuda saboda cikar da cikinta yai.
“Ni gaskiya na gaji, kullum sai an bani wannan bakin abun, su nan garin haka suke aure ni Wallahi garin mu ba haka ake ba�
Ta wani turo baki gaba tana jun cikin ya kame mata ta ko'ina, daker bachi yai gaba da ita, la'asar na yi aka tashe tai sallah sannan aka bata na yamma, wannan karon da hawayenta da komai ta sha tana ta tsirewa Hajiya Mairo albarta a ranta. Ranta be washe ba sai ta aka fara gabatar da events, ta fara ganin fata da rawar jiki kamar za a cinyenta. Ranar da akai bukar kai wasu yan'uwan Bappa da Inna suka u
Iso, the following day akai sa lalle na al'adar mutanen Yola sannan akai Walima, aka daura aure on Saturday. A babban masallacin jumma na Katsina aka daura auren Shattima da Fadime, akan sadaki 800k.
 Fadar irin farinciki da Bappa yake a wannan lokaci ba zai yiyu ba, baki bude sai gaisawa yake da mutane yana sanye cikin Blue Shadda mai dan karen tsada sai wani haske take, a babbar Hotel aka yi liyafar cin abinci, sai abun da ranka yake so kake ci, kusan duk wanda yake jigo a masarautar ya hallarci daurin auren ban da Jarma, da aka nema aka rasa tun lokacin da asirin su Hajiya Babba ya tonu, sai ya tattara komai nasa da iyalansa ya bar garin. Misalin 4 jirgin da sukai booking ya tashi zuwa Yola, karka ku so ganin Fuskar Shattima, murmushinsa ya kasa boyuwa, zuciyarsa kal kamar be taba shiga wata damuwa ko bacin rai ba.
 A daren ranar da aka daura auren Ammy tai bikinta tare da kawayenta, sai kuma Amarya da aka jira mai walima ta zo tun daga sokoto birnin Shehu tana gabatar da karatunta, babu wanda zai yi ma Fadime kallo daya ya dauke ido, saboda kyau da tai, maroon lace ne jikinta da farar alkibba sun haskata sosai ta yi kyau kamar ba ita ba, ba laifi ta kama kanta sosai domin tun da aka fara bikin Hajiya Mairo da wata yar'uwar Mai Martaba suka saka ta gaba suna koya mata tafiya da kuma yadda zata rika amsawa mutane idan sun gaisheta, sannan suka gargade ta ba kowa za tai wa murmushi ba, ba kowa zata sakarwa fuska ba. Hakan yasa bata wani sake ba har sai da ta hango Inna ta shigo gurin tare da tagwarta, kana ganin tufafin da suka saka kasan hadimar ta Ammy ce, Ammy da kanta ya mike ta tarbi Inna dake sanye da atamfa yar ubansu da Hijab ta zaunar da ita kusa da ita, sai Inna ta ji wani girma da kwarjini ya kamata, tana kallon yarta a guri na musamman da aka kawata ita kuma gata a kusa da matar sarki.
Â
 Sai kusan 11pm aka yi addu'ar rufewa bayan mutane da yawa sun gabatar da jawabai ciki har da Ammy, a gaban teburin kowa rika aje takeaway mai cikin da kayan dadi da kuma abubuwan tsinuwa irin su agogon hannu wasu tsarka kowa da abun da yake samu a ciki sai dai duk abun da aka saka a cikin sarka ko agogo worth 50k.
 On that day Fadime ta kwana a gidan Sarauta kuma ta wuni da mahaifiyarta tana ta mata nasiha kala kala, da yamma aka shiga da ita bangaren Mai Martaba yai mata maraba da shigowa cikin familynshi sannan ya dora mata da nashi nasihan, karku so ganin yadda wayoyi suke daukar Fadime da camera, daman tun da aka fara events din ake daukarta a video da hotuna, sai haskawa take ga ta ta sha jan lallen kamar dan ita kawai akai shi. Ita kanta a yanzu ta san ta taka wani matsayi a rayuwa, matsayin zama surukar sarki da kuma matsayin zama matar aure, wadannan abubuwa guda biyu sun zo mata a lokaci daya. Kwance tai a cinyar Inna tana ta hawaye sai a lokacin ta fara missing din abubuwa da ta saba da su, ba ma kamar Inna da kawayenta da kuma Bappa, domin mafi yawan nasihar da Inna take mata na ta yi uwa mijinta biyayya ne, a cewarta su yanzu sun sauke nauyi hakkinta da kulawarta yana karkashin mijinta ne, daga karshe Inna ta rufe mata da bankwana tana hawayen ita ma.
 Misalin 8pm aka shiga da amarya gidanta gaba da baya manyan motoci ne na alfarma, daidai kofar shiga falon aka faka motar Amarya aka shimfida mata wani jan carpet wanda zata taka ta shiga ciki, Gwaggonta da wata Gwaggon Shattima ne suka riko hannunta suka fito da ita motar hadimai na zuba kirari, masu guda suka karade gidan da guda, daga bisani aka soma busar sarakuna.
“Ki ce bismillahi�
Gwaggon Shattima ta fada tana sanye da black lifaya tana rike da hannun Fadime, Jekadiya kuma na daga baya tana fesa mata turare. Daker Fadime tai bismillah saboda kukan da take domin a yanzu ta yarda rayuwarta ta canja kuma ta yarda ya rabu da su Inna da Bappa zata koma rayuwa da Shattima da yan'uwansa, ga wani jazabar aure da take jin tana sauko mata, a katon falon na biyu aka daunar da ita baka jin komai sai guda da kamshin turare ta ko'ina, daga waje kuma masu busa suna ta aikinsu.
ZAINAB POV.
Bata gamsu Iya ta mutu ba har sai da Wasim ya kaita gurin kabarinta ta saka hannunta ta taba kasar gurin sai ga ta tana hawaye da murmushi a lokacin daya, ko za a kasheta a yanzu ba zata iya fadar yadda take ji ba, ba ta san yadda zata misalta ba.
“Finally...�
Ta furta tana mikewa tsaye sannan ta sannan ta juyo ta kalli Wasim da ke tsaye bayanta, takawa ta fara yi har ta isa inda yake tsaye yana kallonta cike da tausayi.
“Ban taba mafarki ko tunanin wata rayuwa za ta zo min a haka ba�
“Haka ne abubuwa da yawa ba mu saka su a tsarin rayuwarmu ba kuma su kasance mana�
“Yeah haka Allah ya tsara, yana tsarawa bawa abun da yake so ba abun da bawa yake so ba�