← Book details Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 172

Sashe 36

Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta fada a ranta, a fili kuma maganin da Inna ta aje gaban Fadime take kallo, tana ganin Inna ta shige daki tai saurin isa gaban Fadime ta saka hannunta tana taba ganin, ba karamin dadi ta ji ba na samun sa'ar lalata aikinsa, daman can idan maye ya taba magani baya aiki komai aikinsa kuwa musamman idan na maganin mayu ne.

“Sha za ki yi Fulani?�

“Eh maganin mayu ne Inna tace min�

“Ai wlh kam sun yi yawa yanzu ko'ina Allah dai ya kyauta�

Ya mike tsaye ta karasa gaban murhu ta gyara wutar, sannan ta koma dakinta ta dauko hijabi mai kaloli ta saka ta fice da sauri daga gidan.
Bata yada zango a ko'ina ba sai gidan aminiyarta Lami, tana yi sallama Lami taja ta sukai cikin bukkarta dan kar kowa yaji abunda za su fada.

“Lahiya kike kau Amo�

“Ina lahiya Lami, kurwa nan da nace zan sai da miki na sake ta yau?�

“Saboda me?�

“Wallahi ina zaune na fara jin wuta da azaba, daga gani gurin wani babban malami suka kaita, dan har kirana yake, da asiri ya tonu ai kara na sakar musu kurwar ƴa�

“Kai kiken Amo baki da juriya Wallahi, ai da kin gwada rikewa ki gani, ba a saurin saki fa yanzu, ko kuma ki sassauta mata daurin ta samu lahiya suna barin gurin mai magani ki kawo min ita na yanke shegiya�

“To nikam na sani, ke ai kika maida abun wasa da kin bani kudi da yanzu na siyar miki ita, kuma Wallahi mai garita, daurin da na mata har wani naso take�

“Aikin gama ya gama tun da kin sake, amman Wallahi da kin sha kudi, kuma irin wannan cikin ruwa zaki ajenta saboda mai kitse kin san bata son zafi in dai ba yankawa za ayi ba, saboda gudun irin haka, kila kin aje ta guri mai zafi azaba ta yi ma macce yawa dole aje neman magani�

“Aa Wallahi cikin kwarya na aje ta, ni yanzu damuwa ta Fulani ce, an cire mata wuta?�

Lami ta rike baki.

“Dazun aka kawo min labari wai anganta da kan maciji�

A nan Amo ta kwashe labarin duk abunda ya faru ta fada mata.

“To ai ba gajiya ake ba, ki sake aika mata wutar idan kuma kika samu sa'a ki kame kurwar daddake mata kai hankali ya juye�

“Ai in bata ciwo gareni ba zata mutu, dan na samo mata wani miji mai kashe mata, ance duk mace da ta aureshi sai ta mutu ina tunanin shi ma maitar yake amman ta sayarwa dan ance kudi gareshi sosai, kin san masu saidawa sun fi arziki ba kamar mu ba�

“A ina? Kuma?�

A nan bata kowaye amiyar ta ta komai ba.

“Bari na yi sauri na koma na bar girki kan wuta�

“To ko kam kar Malam Jaure ya dawo ya fara nemanki, bari sai dare mu hade gurin rawa�

“A a yau ba ni fita tun da dakina yake, sai jibi�

Daga haka tai mata sallama ta dawo gidan a guje, ta shige cikin daki ta cire hijabin ta aje ta fito waje tana kallon kofin maganin da Fadime ta sha magani da shi. ta san ta sha ne kawai amman ba zai mata aiki ba tun da saka masa hannu.

Bayan sallah magariba Bappa ya shigo shi da wani abokinsa Malam Isuhu Inna ta shimfida musu tabarma aka kira Fadime ta fito daga bukkar Inna bayan ta kare sallah magariba ta zauna saman tabarmar.

“Kina da alwala?�

“Eh yanzu nai sallah�

Ta amsa tana kallon wata doguwar takadar da Malam Isuhu yake budewa.

“To Malam Bissimillah�

Malam Isuhu ya matso kusa da ita ya haska fitilarsa yana ya fara karanta mata ayoyin kona aljanu, tun da aka fara karatun Fadime take zaune guri daya tana saurare, idan ya karanta ya karanta sai yace

“Wanene?�

Sai Fadime tace

“Ni ce Fulani�

Tun yana yi yana tsayawa ya tambaye ta har ya gaji ya daina sai karatun kawai yake mata, da Fadime ta ga abun nasa ba mai karewa ba ne sai ta fara lankwashewa tana burkice ido kamar da gaske aljannu ne suka zo.

“Muna aljanu gamu nan mun zo, mu ne�

“Ku suwa?�

“Mu aljanu�

“Miye sunanka?�

Ta dan yi shiru tana tunanin sunan da zata fada, can kuma ta fadi sunan Bappa.

“Sunana Sama'ila�

“Miyasa kika shiga jikinta?�

Mutumen ya tambaya.

“Saboda.....saboda... Muna son mu bada magani�

“A ina kuka hadu da ita�

“A daji..... �

“To ku fita daga jikinta ko na kona ku�

“Ba zamu fita ba�

Ta fada tana ta mulmula a kasa kamar wata mai aljanun gaske, sai mutumen ya cigaba da karatunsa da nufin kona su, Bappa kuma ya shiga dakinsa ya dauko bulalar dorina ya shada mata, a take tai saurin tashi ta zuba da gudu zuwa wajen shanun da suke gidan.

“Mun fita ba zamu sake dawowa ba�

Malamin yace.

“Karya suke haka suke idan suka ga ana kona su�

Bappa ya bita har can ya zuba nata wata bulalar yana fadin

“Ku fita daga jikinta yanzu nan�

“Bappa sun fita tun dazun ni ce dan Allah ka tsaya�

Ina Bappa be yarda Fadime bace sai auna mata bulalar yake, tun tana fadin sun tafi har ta fara kiran Inna ta ceceta.

“Inna nice Wallahi ni ce dan Allah ki zo kar Bapppa ya akashe ni�

Inna ta zo da sauri ta rike bulalar tana fadin.

“Sun fa tafi Fulani ce kake duka�

Sai a lokacin Bappa ya sarara mata bayan ta sha buloli da sunan aljannu.

HAJIYA BABBA POV.

Tsananin mamakin da yake fuskarta ya wuce misali, ta san Jarma ba zai mata karya ba, amman sam bata gane inda labarinsa ya dosa ba, Fadime Falmata Sardauna za su watse musu shiri?

“Wacace Fadime?�

Ta tambaya a fili tana kallon Jarma.

“Ni ma abunda na gagara sani kenan, balle kuma Falmata da Sardauna, amman ni ina ganin kamar Sardauna na Yola yake nufi�

“Sardauna ai yana da nisa da Sarautar nan, balle nai tunanin haka, idan na shi ne to su waye Falmata da Fadime?�

“Abun da na gagara sani kenan, kuma na yi wauta ko da yake tsoro ne a ya hanani tambayar ko me suke nufi, kuma ita Ammy ai Zainab ne sunanta ba Fatima ba balle nai tunanin ko ita ce....�

Be karasa ba Hajiya ta daga masa hannu alamar yai shiru sai dai har lokacin mamaki be bar fuskarta ba. Kwankwasar dakin da ake take saurari kamin ta ji muryar Nana.

“Hajiya Hajiya....�

“Daughter ke ce?�

“Ni ce�

Hajiya ta tashi da kanta ta bude mata dakin tana kokarin kirkiro murmushi.

“Daughter na ya aka yi?�

Ta tambaya tana rike da kofar dan bata son Nana ta hango Jarma a dakinta, duk da ta san ya saba shigowa sai dai rufe dakin da makulli da akai zai saka shakku a zuciya.

“Wayarki za ki bani sai na kira wanda na ce miki ina son ya zama driver na�

“To tsaya nan bari na dauko miki�

Hajiya ta rufe kofar ta dawo ta dauki wayar sannan ta koma gurin kofar ta bude ta mika mata.

“Tafi da ita can idan kin gama ki bawa Karima ta aje min�

“Okay�

Ta karba ta juya cike da jindadi, dan ta san Number AA na cikin wayar Hajiya, saboda ta ari wayar shi ta kira Hajiya da line, duk kuwa da bata da tabbacin number tana nan har yanzu ko an goge, ba dan zata iya ganewa number ba sai dan ta gwada sa'arta.

Bayan ta wuce Hajiya ta sake rufe dakin ta dawo ta zauna. Sai Jarma ya rage murya yace.

“Ashe Nana ta fara dan hali?�

Hajiya ta yi murmushi.

“Ai har abun da yafi dan hali sai Nana ta yi, matukar ina raye ƴaƴan Ammy ba za su taba albarka ba Wallahi har a abada kuwa, yadda take son ganin bakincikina ita sai na ga nata kukan�

Ta karasa tana wane kashe ido zuciyarta cike da kiyayyar Ammy.

*FULANI -it's not free, pay 300 to 0314795884 Abubakar Gt bank, then send the evidence to 08036126660 Æ´an nijar za ku tura 500cf to +22790165991*
03/12/2021, 09:20 - 🤐🤐🤐🤐: *Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence via 08036126660*

Tana cikin bukkarta Hajjo ta leko tai mata ya jiki, daker ta amsa mata da sauki kamar ita taja mata akai mata dukan, Amo ma dake ta mamaki ta leko.

“Fulani ya jiki?�

“Na ji sauki�

Sai da ta kare mata kallo sannan ta juya ta fita, cikin jin haushi Fadime ta fito daga dakin ta zauna a waje, Inna ta dauko koko ta kawo mata ta saka mata ludayi.

“Ki sha yana da zafi�

Kallon kokon kawai tai ta dauke kai tana ta jin haushin dukan da akai mata, gaba daya yanzu laifin Wasim take gani domin shi yaja mata koma minene.

‘Ai ban ce yai min a lokacin ba, amman wai yai min mugunta�

Ta fada a ranta, a fili kuma sai tai kwafa har sai da Inna ta juyo da tsoro ta kalleta, domin yanzu tsoronta take ji ganin abunda ya faru jiya. Mikewa tai tsaye ta karasa gurin Inna tana dan murmushi kamar ba ita ba.

“Inna yaushe shi mutumen zai zo?�

“Wane mutume?�

“Shi mana�

Ta rufe ido tana dariya wai ita kunya. Inna ta tabe baki, ta wani bangaren bata ganin laifin Fadime, tun da ba a taba cewa ana son ta ba ba a taba sallama mata ba da sunan fira ba dole kuwa idan ta ji ana sonta ta jidadi.

“Ban sani ba�

“Inna in be zo ba ni a kai ni to, kin san su mutane birni basa zuwa kauye ko saboda irin hanyar nan, kin ga tun da na iya boko shikenan sai mu yi ta magana da turanci zai ji na burge shi�

Ta fada tana ji wani irin dadi a ranta, jiya har mafarkinsa tai, ta ganshi wani mummuna amman bata ji komai ba saboda neman mijin kawai take ita dai burinta ta ga miji. Jin Inna ta mata shiru yasa ta tashi ta koma inda take ta zauna tana kallon yadda Inna ke raba kokon da ta dama.
Chapter 36 · 0% Book details