← Book details Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 172

Sashe 100

Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya fada ba dan yana da tabbacin Jekadiya tana wajen ba, sai dan ya san ko bata nan dole a nemota a fada mata sakonsa, sai kuwa aka yi sa'a tana gurin ta amsa da to tare da yi ma Falmata a lama data mike tsaye, Falmata ta mike tsaye daker tana dingishi ta bi bayan Jekadiya suka fita daga bangaren, daker da wahala ta sauko stairs din saboda kafarta da bata ko son motsawa, haka ma da zata hawa sai da tai ta wai wai sannan ta samu ta haye har ta shiga cikin falon ita da Inna wuro.
Iyakar inda zata iya hange sai da ta duba ita da jekadiya amman ba su ganshi ba, gasu tsaye a rana suna ta duban inda yake ba su gashi ba, shi kuma isa ta hana shi yi musu wata alama da za su ganshi, ya hakimce cikin motar sai kallonsu yake, Jekadiya bata sa ran yana gurin motarsa ba, idan ma yana can wace daga ciki? Can dai wata zuciyar ta raya mata taje ta duba ko yana gurin ko kuma Garden duk da ta san be cika zuwa gardn din gidan ba.

“Zo mu duba nan�

Ta nufi gurin Motacinsa da suke fake a dabam da sauran motocin gidan, ta hanyar kukan motar da ta ji a kunne ne ta gane cewar yana cikin bakar motar, sai ta ja ta tsaya ita da Falmata har sai da yaga dama ya sauke gilashin motar. Da hannu yai mata alama da ta tafi sai ta juya ta koma inda ta fito, Falmata kuma ta sirina a gaban ganbun motar idonta a kasa, gabanta sai faduwa yake domin bata san dalilin kiran ba.

“Me ya samu kafarki?�

Ya fada yana kallon saman kanta daga inda yake zaune cikin motar. A tunaninta be kamata ta fadawa kowa cewar mahaifinta ne ya daketa ba, ba kuma zai mata kyakkyawar fahimta ba.

“Faduwa na yi�

Yana son ya ce garin yaya ta fadi har ta samu rauni haka, sai dai yana jin nauyin bakinsa da ganin zai shiga safgar da ba tashi ba. Dauke idonsa yai ya maida kan wayarsa yana latsa kamar ba mutum ya bari a gurin ba.

“Fada min gaskiyar abun da ya faru�

Ya furta bayan ya dauki tsawon lokaci yana chatin da Ra'ees a wayar. Ko be fito fili ya furta abun da yake nufin ya faru ba, ta san satar da ake magana yake nufi.

“Ban dauka ba, ban tana sata ba, ta shirya min abun ne ta yadda ba zan iya fitar da kaina ba, ita ta kirani tace na zo na gyara kayan Hajiya, kamin na gama ta ba ni yan kunnen yara tace na kulle a dankwalina, bayan na gama ta bani wannan sarkar tace kar na nunawa kowa na boye a hijbina.....�

Har ta gama zana yadda abun ya faru Shattima be ji komai ba hankalinsa yana kam waya, sai bayan kamar minti uku ya dago ya sake kallonta.

“Ban ji ba�

Haka ta sake karanta masa abun da ya faru kamar dazun. Aje wayar yai yana nazari, mi zai saka Jurry tai haka? Saboda ta batawa Ammy suna cewa mai aikinta tana saka ko kuma saboda wani abun dabam.

“Kin taba shiga bangaren ne kamin nan?�

“Aa�

“Then what happen da Sirleem ya dauke ki ina ya kai ki?�

Tsoro ne ya ziyarce ta, wata kila idan ta fadi gaskiya zai jefa Sirleem din a matsala hakan yasa ta zabi yin karya.

“Gida ya kai ni�

Hannunsa ya kai ya bude gurin da yake ajiyar kudi ya dauko bandir din 500 ya mika mata.

“Gashi hakkin aikin da kika yi, and idan kina ra'ayi cigaba da aiki a nan ki fadawa wani sai a sanar da ni�

Ta saka hannu biyu ta karba.

“Na gode Allah ya saka da alheri, ya baka wasu yayan masu albarka, su kuma Allah yasa masu ceto ne�

“Ameen�

Ya amsa yana kallonta, sai ta mike tsaye ta fara tafiya da dingishi, binta yai da kallo kamin ya maida dubansa gurin Nana data doso inda yake da saurinta tana sanye da Hijabinta na islamiya.

“Har kun ta so?�

“Yeah yau wa'azi ake mana yau laraba ba a dadewa�

“Zagoyo ta nan�

Ya fada yana rufe gilashin motar, sai ta zagaya ta dayan side din ta bude motar ta shiga ta zauna ba tare data rufe ba.

“Ya dan Allah karka yi bushi da ni idan na fada maka gaskiya�

Ya tattara dukan hankalinsa ya maida a gurinta.

“Ina jinki�

Cikin kunya da badama ta labarta masa abun da ya faru, na satar da tai da kuma barazanar da tai ma Hajiya har da abun da ta ji Hajiya Babba ta fada. Ba karamin mamaki ne ya kama Shattima ba, baya son ya munanawa Hajiya zato duk da ya san basa jituwa da mahaifiyarsa sai dai shi yana daukar hakan ne a matsayin kishi kasancewarsu mata, amman be yi tunanin fitowar lafazi irin wannan a bakinta ba.

“Ammy ta ji wannan?�

“Bata saurare ni ba, tana fushi da ni saboda abun da na aikata sai da aka yi rasuwar nan ne ta sauko�

Shattima ya sauke ajiyar zuciya.

“Shikenan, karki fadawa kowa wannan maganar ko da Mai Martaba ne, zaki tada masa hankali ne kawai, kuma dan Allah karki sake aikata abu makamancin wannan�

“To Ya Shattima, daman Sardauna yace na yi masa alkawarin ba zan sake aikata ba, kuma zan rika zuwa makaranta kullum zan zama yarinyar kirki, kuma duk na masa yace ma na daina zuwa bangaren Hajiya kuma ko ta bani abu na daina karba, yace wai ita ba son gaskiya take min ba Ammy ce take so na, tun ranar ban sake zuwa bangarenta ba ma, kuma ina zuwa school both islamiya da boko, ko bana jindadi ina daurewa haka nan saboda na cika alkawarinsa�

Maganar take idonta na cika da kwalla, Shattima kam kallonta kawai yake yana karantar abun da ita kanta bata san tana tare da shi ba.

“Ya dan Allah kai wani abu ya dawo I miss him, kuma yana da kirki sosai�

Shattima yayi murmushi.

“That's good gashi ya sa kin fara natsuwa ai�

Ta yi murmushi domin be fadi karya ba ita kanta ta san ta canja cikin yan kwanakin nan.

“My little girl, ya kamata a saka masa da abun da yai miki daman ai�

“Eh yaya dan Allah kaje gidan kai magana da yayarsa sai ta bar shi ya dawo aikin nan�

“Aa zamu dai saka a nemota ba zamu je ba kam, zamu saka a nemosa dai�

“No Yaya he's important to me kuma yayar shi ba, amman idan ta ga ka tafi zata bari maybe�

“Waye za a cewa Yarima yana nemansa yace ba zai zo duk garin nan? Wa zan yi ma magana yace min ba zai yi ba? Ko ke aka ce kina kiransu dole ta zo, kuma idan kika fada dole ta ji, kira daga masarauta ba kira daga makota ba ne, ke kanki da ace kin natsu kamar sauran yayanki da bata isa ta musa miki ba�

“Amman yaya ba komai ne Zaka ce sai an zo maka ba, sometimes you need to go, musamman idan abun yana da muhimmanci a gareka�

Ya dan yi shiru yana kallonta.

“You're right, zan sam abun yi�

“Yaushe? Anjima?�

Ya busar da iskar bakinsa daman ya san halin Nana akwai zakuwa.

“Tomorrow Morning�

“Okay thank Youu�

Ya daga mata kai yana murmushi sai ta juya ta fita cike da jindadi zuciyarta har wani zillo take tsabar murna da jindadi kamar ance mata Sardaunan ya dawo gidan ma gaba daya.
Sai da Shattima yai ribas sannan juya kan motar zuwa gate, a hankali yake driving din har ya fice daga gate din suna daga mishi hannu. Da hannu daya yake driving dayan hannun kuma yana rike da wayar da yake ta amsa sakonnin gaisuwar da ake masa, domin ko an kirashi a waya sai ya dama yake dagawa, daman can baya son yawan magana, balle kuma yanzu da yake jin komai ya masa nauyi, hakan yasa most of his friends musamman wandanda suka san halinsa da kuma wadanda suke nesa suke aike masa gaisuwar ta chat. Maganar da Nana tai ne yasa shi daukar hanyar da zata kai shi million quarter's, ba kamar yadda yai niyar aika mata da sakon kira ba ta waya, sai dai a yanzu ya zabi ruwa ba dan yayi niyar hakan ba sai dan abun da Nana ta fada cewar sometimes you need to go... Daman kuma hanyar gidansa ne da yake son tafiya a yanzu. Gaban gate din ya tsaya da motarsa ya danna horn, daman ya san gidan tun a lokacin data siya, shi ne mutum na farko data fara fadawa kuma ta dauko masa hoton gidan da komai, kamin ta takurashi yaje ganin gidan a lokacin da aka gama gyara. Mai gadin ya leko ganin mota yasa ya fara zuwa gurin motar ya ga ko waye kamin ya bude, sai dai bakin gilashi ne, kamar yadda motar take baka, isowa yai gurin motar a zatonsa ganinsa zai saka mutumen dake cikin motar ya sauke gilashi, amman sai ya ga tsabanin haka, hannunsa ya kai ya kwankwasa gilashin, domin aikinsa sanin wanda ya shiga da kuma wanda ya fita a gidan a matsayinsa na Mai Gadi. Anan ma Shiru Shattima be sauke gilashin motar ba, ko dagowa be yi ya kalleshi ba, sai amsa sakonninsa yake, hakan yasa Mai gadin ya juya ya koma cikin gidan dan sanarwa masu gida.

FADIME POV.
Chapter 100 · 0% Book details