Sashe 9
Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai da suka gama shawara sannan suka dawo cikin ɗakin suka same ta ta takure a ƙuryar gado tana rawar jiki, gyaran murya Andizo ta yi ta canja muryna ta ce “To tun da kin ce ciki gareki za mu rabu da ke, amma bayan kwana biyu za mu dawo in dai muka ga ba ki canja hali ba to mun san ba cikin gaske ba ne. Sannan abu na ƙarshe ki ba wa mijinki haƙuri kuma ki miƙo wannan kuɗin da kuke cutar shi kuna amsa..”
Da hanzari ta tashi ta ɗaga katifar gadon ta lalibo su ta miƙa musu, ganin idanuwanta a buɗe Hajaru ta ce “In ba ki rufe idanuwanki ba muna taɓa hannunki za ki ganki a dajin ƙare kukan ka.”
Saurin rufe ido ta yi ta miƙa musu suka amsa, Andizo ta sake jadadda da mata in dai ba ta yi abin da suka ce ba za su dawo, ta amsa da to suka ce kar ta buɗe ido in ba ji ta yi Iliya ya shigo ba sannan suka fita..
Sanda Hajaru ta miƙa wa Andizo ta ce “Duƙa kike tafiya nima zan yi tun daga gida na zo mana da ita na aje a baƙin kofa.”
Har ta buɗe baki za ta yi dariya sai ta tuna inda suke ta rufe bakin suka fito a duƙe kamar tsofaffin gaske..
Iliya da ya jingina da jikin katanga yana baccin wahala ya ji ana kiran shi da muryar tsafaffi ya yi saurin tashi, kallon kofar shiga ya yi ya ce “Malam har kun gama?”
Gyaɗa kai Andizo ta yi tana rawar jiki irin an tsufa tukuf ɗin nan ta ce “E Wallahi yaro ai dama na faɗa maka mu za mu raba ta da aljannun, ka shiga babu wata matsala dama aljanun jikinta abokanmu ne mun zo mun tafi da su..”
Zaro ido ya yi zai yi magana ta ɗaga masa hannu ta nuna masa kofar shiga, sai da ya zo zai shige ya ce “Gaskiya kuna da kirki sosai, yau zan yi barci hankalina kwance ba tarzoma..” Yana faɗin haka ya wuce da sauri suma suna ganin ya shige suka wuce..
Sai da suka je bakin dandali suka cire kayan Hajaru ta ba da ɗankwalinta suka goge fuskarsu, zama suka yi a bakin hanya suka dinga sheƙa dariya suna tafawa. Bayan sun gama Andizo ta fito da kuɗin ta haske fitilar waya suka buɗe kuɗin, sai da suka lisafa jika goma ce cif har da dala goma a kai Hajaru ta riƙe baki ta ce “Muguwa ji fa uban kuɗin da ta tara, gobe sai na kai masa abin shi.”
Tashi Andizo ta yi ta ce “ Tab ki rabu da shi zan aje kuɗin in ta haihu sai mu kawo a matsayin gudumawa, mu je wajen Saminu tun da na zo ban ganshi ba, shi ko ya je ya ganni ma tashi mu isa sai na masa rashin mutumci..” Ta faɗa tana mayar da kuɗin ta ƙulle a jikin zaninta suka nufi in da Saminu ke zama..
Andizo ta riƙe kugu ta tsaya a gaban shi, a hankali ya soma bin ƙafafuwanta da ta mulke su da mai ƙasa ta baɗe su, saurin daga kai ya yi yana kallon ta. Murmushi ya sakar mata yana kallon gefe da gefe ya ga ba kowa, gefen shi ya nuna mata ya ce “Dije zo nan mana mu yi magana.”
Ba muso ta dawo gefen shi ta zauna sai hura hanci take, Hajaru ta zauna a kusa da ita ta kalli Saminu da jikinshi ya yi sanyi sai wani irin kallo yake yi wa Andizo ita kuwa ko ba ɓangaren shi ba ta kalla ba..
“Gaskiya dai Saminu amana ba ta ce haka, yanzu masoyiyar taka ta ɓata na tsayin satuttuka, kuma ta dawo ka kasa zuwa ka gano ta? Anya ba munafukai sun shiga sun fita suna haɗa ka da ƙawata ta ba?” Ta faɗa tana riƙe ƙugu.
Hannayensa ya haɗe waje ɗaya ya kalli Andizo da take cika tana batsewa, a sanyaye ya ce “Wallahi Dije ina matuƙar sonki kawai dai an hana ni zuwa wajen ki ne, ki yi haƙuri kar ki yi fushi da ni hakan ba zai mini daɗi ba.”
Hararar shi ta yi ta ce “Mai ƙarya dai ɗan wuta ne Saminu, karka yi ƙarya dan ba na son ka zama ɗan wuta in, da gaske ne ka faɗa mini wanda ya hana ka zuwa inda nake mana.” Ta faɗa tana cuno baki gaba, sosai ta ji haushin rashin zuwan shi ganin ta..
“Wallahi Hammanki ne da wannan ɗan birnin suka ce kar na sake zuwa in da kike, shi Hamma Giɗaɗo cewa ya yi kar na sake kula ki in ya ganni da ke zai ɓata mini rai, shi ya sa kika ga ina yin baya-baya da ke ba wai dan ban damu da ke ba ne. Jiya har fanke na zuba da zafin sa na ba wa Talle ya kai miki sai ga shi ya dawo yana kuka, ya faɗa mini Hamma Giɗaɗo ne ya kwace fanken ya koro shi da bulala..” Ya ƙarashe maganar yana sunkuyar da kai.
Tun da ya fara maganar Andizo ta saki baki tana sauraron shi, mamaki fal ranta jin wai Hammanta ne ya hana masoyinta zuwa inda take, a fusace ta miƙe ta dawo gaban shi ta durƙusa ta ce “Saminu!”
Ɗago kai ya yi suka haɗa ido idanuwansa sun cika taf da hawaye, lumshe su ya yi dan kar ya bari su zubo amma ina ya makaro dan tuni Andizo ta gani, a ruɗe ta ce “Wallahi in ban rama maka abin da Hamma ya yi maka ba ka ce ni ba ɗiyar Hajja da Maigari ba ce, shi ne kake kuka dan ya hana ka gani na? Me ya sa ba ka faɗa mini ba tun wuri na masa kashedi kar ya sake shiga tsakani na da kai? Ka yi haƙuri yau Hamma ya taro bahar maliya, alƙur'an sai na sa shi kuka shima tun da har yake takura maka..” Ta faɗa a masifance.
Murmushi mai ciwo Saminu ya yi, shi ya san ko giyar wake ya sha yanzu Andizo ta fi ƙarfin shi tun da har an sa mata rana, ita kuma a ganin ta tare za su tafi can birni su yi karatu da shi sai faɗa wa mutane take cike da kwarin gwiwa, shi kam in ta sanar masa kallon ta kawai yake ya rasa yaushe za ta gane wayo ne aka mata aure za ta yi ba karatu ba..
Tashi ya yi ya zuba mata fanke ya isa can gaba da su kaɗan ya sayo mata ranke guda huɗu ya haɗa ya miƙa mata, ƙin amsa ta yi ta maƙale kafaɗa, ya kalle ta ya yi murmushi komai nata tafiya yake da shi, sai dai in ya tuna ya kusa daina ganin ta sai ya ji gwiwarsa ta sace.
“Ki amsa Dije in dai da gaske kina sona.”
Jim abin da ya faɗa sai ta sa hannu ta amsa tana faɗin “Kar fa ka damu da zarar mun tafi birni ai ya huta da ganin mu ballantana ya takura maka.”
To kawai ya ce mata suka masa sallama suka tafi..
Sai da suka kusa zuwa gida Hajaru ta ce “Andizo Wallahi Saminu tausayi yake ba ni, yanzu in aka ce ba za a tafi da shi birni ba shi kenan nan an raba ku ko?”
“Kan uba! Ke ki bar faɗin wannan maganar ma, yo ai shi mai hankalin ya ce za mu tafi da Saminu har Maigari ya faɗawa, ki bar wannan batun ma zo mu cinye fanken nan gobe ko jibi mu je gidan Laure mu gani ta canja ko kuwa sai mun mata duka za ta daina ƙarya..”
Ba ta sake cewa komai ba suka samu gefen hanya suka zauna ta baje musu fanken suka yi bismillah suka fara ci. Bayan sun gama Andizo ta ce “Ki zo mu je ki kwana a gidanmu yau.”
Har za ta yi gardama sai kuma ta fasa dan ta san halin ƙawarta ta ba mutumci ba ne da ita tsaf za ta mata dibar albarka.
Washegari Andizo bayan ta gwada kayayyakin da Mom ta kawo mata sai maganar Saminu ta faɗo mata a rai, ta haɗe kayan ta nufi ɗakin su Giɗaɗo da sauri tana kwada masa kira.
“Hamma ! Hamma! Ka fito yau ni da kai a gidan nan ban ga ba mai raba mu sai Allah, kai alƙur'an daga yau ma zan iya fasa ce maka Hamma inga ta fankamar da kake kana takurawa masoyina..”
Buba ya tashi zaune yana faɗin “To fa masifatu layar ƙanzo, yau kuma da Hamma Giɗaɗo za a yi? To bari na tashi na bar muku ɗakin kafin ta iso ta cika mini kunne.”
Ko kallon shi Giɗaɗo bai yi ba sai ma gyara zama ya yi yana jiran zuwan ta.
Ba ko sallama ta faɗo ɗakin, kanshi ta tsaya ta da hannu ta damƙo kwantacciyar sumarsa ta ɗago kansa da ƙarfi, tana hura hanci ta ce “Ina dai faɗa maka karka sake tare mini masoyi kana masa barazana, dan mugunta shi ne har da saka shi kuka ka hana ya zo inda nake? To ka fita idona na rufe tun kafin na ɗauki fansa a kanka. Ko dan ka ga ka hana ni rama abin da su Hajja suka mini kake tunanin na canja daga yadda ka sanni ne? To alƙur'an zan maka dukan tsiya in ga mai kwantar ka a gidan nan, ina ruwan ka da Saminu?” Ta sake shi tana huci ta kuma nuna shi da tsaya ta dora da cewa “Idan kunne ya ji gangar jiki ya tsira, kar ka ganka ƙato ka linka ni a tsayi tsaf zan maka duka babu abin da ya shafe ni da kai Hammana ne..”