Sashe 22
Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tunawa ta yi da Maman Aminatou ta shiga ɗaki ta yi simple kwalliya ta saka doguwar riga da ɗaura ɗankwalin ta ɗauki mayafi ta yaba ta nufi ɓangaren Aminatou, gabanta ne ya dinga faɗuwa dan ba ta san ba irin tarbar da za su mata, har ta juya za ta dawo sai ta tuna da maganar Hajiya Babba da ta ke ce mata indai kishiyar ta ki baƙi 'yan gidansu take leƙawa su gaisa sai ta dawo, ajiyar zuciya ta sauke ta aro jarumta ta yaba ta taka ta tsaya bakin kofar ta buga..
Su Aminatou suna cin abinci suka ji buga kofa, ta tashi da, sauri tana faɗin “Waye?”
Ta ce ita ce ta yi saurin buɗewa tana dariya ta ce “A a 'yan makaranta har kin dawo? Amma dai ba Salim ya kawo ki ba?”
Murmushi ta yi tana wasa da yan yatsunta ta ce “A'a ai shi rabon da na ganshi tun da ya kaini makaranta, na zo na gaishe da su Ummi ne Ahmad ya ce mini su ne suka kawo miki ziyara..”
Matsawa ta yi tana kallon su ta ce “Ummi ga Khadija ta zo gaishe ku.” Ta faɗa tana kama hannunta..
Suna isowa ta durƙusa ta ce “Ummi sannun ku da zuwa, ya gida ya kwana biyu?”
Cike da birgewa Ummi ta ce “Lafiya ƙalau Khadija yanzu Aminatou take ce mana kin tafi makaranta.”
“E Wallahi sai ɗazu ma na dawo.”
“Ma sha Allah to Allah ya ba da sa'a a maida hankali a yi karatu kin ji.”
“To Ummi in sha Allah, bari na koma.”
“A, haba dai ya za ki tafi bayan kinga muam, cin abinci ? Zo zauna mu ci abinci tukun.”
Duk da yunwa take ji amma sam ba za ta ci abinci a cikin su ba, girgiza kai ta yi tana tashi tsaye ta ce “Wallahi na ƙoshi na ci abinci kafin na zo gida..”
Tashi Aminatou ta yi ta ce “Haba girkin nawa ne ba za ki ci ba? Ko kunyar su Ummi kike ji? Da ai in kina jin yunwa ci kike tsaya na ɗauko miki dama nasan kamar za a yi haka shi ya sa na diba miki naki daban..”
Ita dai ba ta ce komai ba sai wasa da take da hannunta, miƙa mata kula Aminatou ta yi ta ce “To ga shi tun dai kunya kike ji.”
Amsa ta yi ta mata godiya sannan ta juya.
“Wannan mayyar yarinyar kalli yadda take buɗewa ta girma ga haske da ta yi kamar ba ita ba ce aka kawo sai ka ce kazar mayu, ni Wallahi na tsane ta ma sani ne baki yi ba Anty, naji fa ana cewa ba a san ba ubanta, shi ne Yaya Salim ya je ya jajibo miki ita wa ya sani ko tsintar ta suka yi waɗanda suka riƙe ta..”
Runtse ido Andizo ta yi da ƙarfi zuciyarta ta buga har ba ta san lokacin da kular ta subce mata ba sai ƙaran faduwar ta suka ji, da sauri duk suka ɗago suna kallon ta, Ummi da ba ta ji abin da ƙanwar Aminatou ta faɗa ta ce “Subhanallahi Khadija sannu ba ki dai ƙone ba ko?”
Gyaɗa kai ta yi ta sunkuya ta dauki abincin ta dawo gaban ƙanwar Aminatou da suke kan kujera ita da Aminatou ta ɗaura kular a kan cinyarta ta ce “Ga abincin ki na faɗa miki na ƙoshi ƙamshin shi duk ya buwaye ni har zuciyata tashi take kamar zan yi amai..”
Saurin kallon ta Aminatou ta yi tana zare ido, “Amai kuma Khadija? Ko ba ki da lafiya ne.”
Wani irin kallo ta musu wanda ya ba su mamaki ta juya da sauri ta bar palon, Aminatou ta dafe kirji ta ce “Ke shegiya ko dai ta ji abin da kike faɗa a kanta ne?”
Taɓe baki ta yi tana kawar da kai.
Da gudu ta isa ɓangarenta ta faɗa kan kujera ta fashe da kuka, sosai maganganun ta ke mata yawo a zuciya tana nanata kalmar ƴar tsuntuwa.
Da mamaki ya fito jin kukan ta, ganin yadda take kuka ya yi saurin isowa ya ɗago da ita, ganin shi ne ta faɗa jikinsa ta ƙarawa kukan ta mai, ta ce “Mai hankali da gaske ne ba ni da uba? Wai tsunto ni aka yi ba a san babana ba?”
_*Maman Nusaiba ce🤙🏻*_
[6/4, 2:14 PM] Ummu Amjad: _*AREWABOOKS@SARATALKASUM88*_
27
Saurin ɗago ta ya yi a ruɗe jin abin da ta faɗa, fuskarta ya ɗago yana girgiza mata kai ya ce “Wani mahalikin ne ya ce miki ba ki da uba? Kin taɓa ganin wanda aka haifa babu uba? Ki faɗa mini wanda ya ce miki haka..” Ya faɗa yana sake mayar da ita ya ci gaba da rarrashi ta. Dai da ta yi kuka mai isar ta sannan ta yi shuru tana sauke ajiyar zuciya, gabaɗaya ta ji tana son sanin waye ubanta indai har ba Maigari ba ne ya haife ta.
“Khadija ki daina kuka kina da uba ke ba 'yar tsuntuwa ba ce, ɗiyar halak ce ke ba a titi aka yi tsince ki ba. In dai kina son na sanar da ke waye babanki to sai kin daina kuka, sannan kin faɗa mini wanda ya miki gorin ba ki da uba..”
Wasu hawayen ne suka zubo mata ta sa hannu ta goge ta ɗago ta kalle shi, a sanyaye ta ce “To na daina don Allah ka faɗa mini indai ba su Maigari ba ne iyayena su waye suka haife ni?”
Gyara zama ya yi ya ɗauko ta ya zaunar da ita a kan cinyarsa ya ce “Idan na faɗa miki ba za ki dinga kuka ba? Sannan ba za ki shiga damuwa ba za ki yi ta addu'a?”
Gyaɗa mishi kai ta yi ya ce “Maigari da Hajja su kakanninku ne ba iyayenku ba k..”
Saurin tarar numfashinsa ta yi ta ce “To kenan ina da 'yan'uwa waɗanda muke mama da baba ɗaya?”
“Kwarai ma kuwa, yayunki su ne Umar, Buba, Aliyu, Ibrahim wato Iro uwa ɗaya ta haife ku..”
Baki ta riƙe ta ce “To kenan Hamma Giɗaɗo ƙanen Innata ne shi da Adda Ɗahare? Tun da Inna matar Maigari ce.”
Dariya ya yi yana riƙe hannunta ya ce “A a, Giɗaɗo ma yayanki ne amma ba uwa ɗaya uba ɗaya ba, su ne suka ceci rayuwarku ke da su Umar.”
Kallon ban gane ba ta mishi shi kuma ganin ta nutsu ya soma faɗa mata labarin ranar da ta zo duniya da yadda 'yan bindiga suka hargitsa musu gari har mamanta da su Umar suka zo rugar su Inna, da yadda suka gudu har suka zo garin Tilaberi da yadda aka raine ta.”
Tun da ya fara maganar take kuka har da majina, ashe mamanta da babanta duk an kashe mata su? Jikinta ne ya ɗauki rawa ta miƙe da sauri za ta bar palon jiri ya ɗauke ta kafin ya kai ga tashi sai faɗo masa ta yi a jiki sumammiya.
Ɗaukan ta ya yi yana kiran sunanta ya nufi ɗaki da ita, ruwa ya fito ya ɗauka ya koma ya yayyafa mata. Dogon numfashi ta ja tana buɗe ido ta sa mishi kuka, rungume ta ya yi yana bubbuga bayan ta tare da yi mata nasiha har ta yi shuru ƙarshe bacci ya yi gaba da ita..
Kwantar da ita ya yi yana kallon ta cike da tausayawa, shima kwanciya ya yi yana jiran ta tashi ta sanar mishi wanda ya mata wannan gorin.
Sai gaf da magariba ta tashi ya ja ta suka yi wanka, da kanshi ya shirya ta yana nuna mata kulawa duk dan kar ta sa damuwa a ranta. Bayan Sallar isha'i ya sake tambayar ta ta sanar da shi ƙanwar Aminatou ce ta faɗa mata tare da ba shi labarin duk abin da ya faru da ta je ɓangaren na Aminatou. Sosai ran Salim ya yi mugun ɓaci, ya kuma yi mamakin maganar, babu lefin wanda yake gani illa na Aminatou, tashi ya yi ya ce mata yana zuwa ta amsa da to sannan ya fita.
Daret ɓangaren Aminatou ya nufa ko nocking bai yi ba ya murɗa ƙofar ya shiga da sauri, Aminatou ta ɗago tana kallon shi sai kuma ta haɗe rai ta ce “Haba Salim kamar ba musulmi ba ka shigo gida kai tsaye?”
Wani irin kallo ya mata wanda ya sa ta sha jinin jikinta, kallon Abida ƙanwar Aminatou ya yi jin tana cewa “Yaya Salim tun da rana muka zo ba mu samu mun gaisa da kai ba, ina wuni ya gida ya dare?”
Ko ci kanki bai ce mata ya kira Aminatou ɗaki suka zauna, ji yake jinin jikinsa na tafasa ya kalli Aminatou ya ce “Wallahi Aminatou kin ba ni kunya, ban taɓa tunanin har akwai lokacin da za ki canja daga mutuniyar kirki zuwa wata ta daban ba, ke yanzu kina ganin abin da kuka aikata kun yi daidai kenan?”
Dafe ƙirji ta yi ta ce “Na shiga uku! Me kuma na yi haka Salim?”
Ɗaure fuska sosai Salim ya yi wanda Aminatou ta hango zallar ɓacin rai ya bayyana ƙarara a fuskar, gaban ta ne ke dukan uku-uku tana ta saƙe-saƙe ta ƙagara ta ji me zai ce mata, ƙafa ɗaya ya dora a kan ɗaya ya ce “A tunanina duk wani abu da kika ga ina so za ki yi ƙoƙarin kare shi ko ina nan ko ba na nan ashe ba haka ba ne, tabbas yau kin ɓata mini rai da tun da muke da ke ba ki taɓa fusata ni irin na yau ba, yanzu har kina ji kina gani a gaban ki a ci wa Khadija mutumci ki kasa cewa komai? Kuma ba wani bare ba ne ƙanwarki ce ta ci mata fuska, shin ma na tambaye ki? Waye ya ce wa Abida Khadija ba ta da uba?” Ya faɗa yana zare mata idanuwansa da suka yi jajur saboda ɓacin rai.
Jikinta ne ya ɗauki rawa ya daka mata tsawa tare da nuna mata hanyar fita ya ce “Je ki kira mini Abida yanzun nan.”
Da sauri ta fita kamar wadda aka jefo Abida sai ganin ta ta yi a gaban ta, dafe ƙirji ta yi ta ce “Me ya faru?”