← Book details Andizo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 75

Sashe 41

Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsugunnawa ya yi a gaban ta sai a lokacin ya iya cewa “Kha.. Khadija !” Ya faɗa fuskarsa na bayyana tsantsan farin cikin da yake cikin zuciyarsa na ganin ta a wannan lokacin. Saurin buɗe fuska ta yi ta saki baki galala tana kallon bakinsa da yake rawar sanyi, sam ta kasa gane a ina ta san wannan fuskar sai ta ja baya ta zauna, shima gyara zama ya yi yana sauke ajiyar zuciya kamar ya yi gudun ceton rai, sai zuwa can ya ce “Khadija wai ba ki gane ni ba? Ni ne fa masoyinki wanda yake sonki fiye da kowa a duniyar nan, ke ko waɗanda suka kawo ki duniya da kaɗan za su fini sonki, ina kika shiga tsayin shekara uku ko labarinki ba na ji? Kin san kuwa irin hali da na shiga sakamakon rashin labarinki da na yi? Ina mijin da naji an ce an aura miki?” Ya ƙarashe maganar yana kamo hannayenta ya soma murzawa a hankali yana kallon ta cikin yanayin damuwa mai tarin yawa.
Sororo Andizo ta yi tana kallon ikon Allah ta rasa yaushe suka san juna da shi da yake jero mata wannan tambayoyin, tagumi ta yi ta ce “Malam ni fa ban sanka ba ka tsare ni da tambaya kamar ina cikin ƙabari, a ina muka taɓa zama da kai har muka ƙula soyayya? Ka matsa ka ba ni guri in fita yarana suna can yanzu sun fara kuka.”
Zaro ido ya yi ya ce “Wai har haihuwa kika yi?”
Cike da ƙosawa ta miƙe tsaye ta ce “E yarana uku ma.”
“Kai ƙarya ce duka yaushe aka miki auren da har za ki yi yara uku.”
Tsaki ta ja ta iso bakin gadon Amira ta ɗauki hijabi ta saka saƙala jakarta ta harare shi za ta yi gaba sai ga Amira ta shigo, ganin shi a ɗakin ya sa ta faɗaɗa murmushin kan fuskarta ta ce “Uncle kaine a nan? Dama ina cewa yanzu zan je na kai ƙawata ku gaisa wadda nake ba ka labarin an mata ga ta ƴar ƙarama.”
Tashi ya yi tsaye ya sa hannu a aljihunsa ya saki fuska ya ce “E ni ne na shigo na duba ki sai na haɗu da wadda na kwashe shekaru uku ina neman ta, ga shi Allah ya sa na ganta.”
Da mamaki Amira ta kalle shi ta ce “To dama Uncle ka san Khadija ne?”
“Sosai ma, ai ita ce mace ta biyu da na fara so a duniya amma ta ɓace mini.”
Andizo ta cika ta yi fam ta kalli Amira ta ce “Kinga ni fa ban taɓa ganin shi ba in ba yau ba, sai dai in wata ce mai kama da ni da irin suna na ya sani ba dai ni ba, zan wuce dan ba ni lokacin shi yarana nake son gani?” Ta faɗa tana yin gaba za ta fita Amira ta yi wuf ta kare bakin ƙofar. Kallon ta ta yi zuwa yanzu ita kanta Amirar haushi take ba ta, ya daga zuwa dubiya sai kawai wani sangameman mutum ya ce wai sun san juna da ita? Tsaki ta ja ta ce “Don Allah ki matsa ki ba ni waje na tafi gida.”
Girgiza mata kai Amira ta yi ta ce “Da gaske Khadija ke ce wadda Uncle ɗina yake dakon soyayyar ki a zuciyarsa? Don Allah ki saurare ni in miki bayani ƙila za ki tuna da shi.” Ta faɗa tana haɗe hannu alamar roƙo.
Dafe kai Andizo ta yi ta sa hannu ta janye Amira daga bakin buɗe ta fita suka rufa mata baya, har harabar gidan suka biye da ita Amira na kiran sunanta amma ta yi kamar ba ta ji ba ta wuce za ta buɗe get Amira ta sa maigadinsu ya hana ta shiga, tsayawa ta yi ta riƙe ƙugu tana kallon su.

“Don Allah Khadija ki tsaya direba ya kaiki, ni ba zan hana ki tafiya ba daga baya mun waya tun da na ga ranki ɓaci amma ki yi haƙuri.”
Yadda take roƙon ta sai ta yarda ta tsaya, direba ya ɗauko mota ya ta shiga ko sai an jima ba ta cewa Amira va saboda tsabar takaicin da ta shaƙa. Hannu Amira ta ɗaga mata har suka bar gidan, juyowa ta yi tana kallon shi a sanyaye ta ce “Uncle ka yi haƙuri muje ciki ka bi komai a hankali, Khadija fa mijinta bai fi shekara da wata ɗaya da rasuwa ba, ba ta son a mata maganar aure.”
Mamaki sosai ya bayyana kan fuskarsa ya sai ya juya yana ta nazarin maganar Amira ya shige ciki..

Maman Amira na ganin su ta ce “Lafiya dai kuka shigo jiki ba lakka?”
Wayancewa suka yi Amira ta ce “Ba komai Mama na raka Khadija ne da sai muka haɗu da Uncle.”
Da kallo kawai ta bi su har kowa ya shige ɗakinsa..

Babu irin kiran da Amira ba ta yi wa Uncle ɗin nata ba dan ya mata bayanin yadda aka yi ya san Andizo amma ya ki ɗauka, haka ta lalibo numéro ɗin ta ta kira ta ji wayar a kashe dole ya haƙura ta zauna da tarin tambayoyi fal zuciyarta.

Suna sauka ta fito ta mishi godiya sannan ta nufi ciki, ta kusa isa ta ga an sha gaban ta ta ɗago kai suka haɗa ido da shi, takaici ne ya rufe ta matsa za ta raɓa gefen shi ya yi saurin jan ta ya shiga wata ƙofa da ita. Da ido kawai take bin shi dan ta ga iya gudun ruwan shi, ganin su ta yi a wani katafaran palo mai girma sosai an cika shi da kayan ado. Kujera ya nuna mata yana haɗe rai ya ce “Zauna a nan mu yi magana ta fahimta.”
Kallon ka raina mini hankali ta mishi tana turo baki, kwafa ya yi yana tsare da idanu ji yake kamar ya rufe ta da duka saboda raina shi da ta yi, sai da ya daka mata tsawa ta zauna a kiɗimi tana rawar jiki, in akwai abin da ke hargitsa mata lissafi to bai wuce a mata tsawa ba nan da nan za ta rasa nutsuwarta.
Hararar ta ya yi yana kaɗa ƙafa ya ce “Shi wancan yaron da na gani kina wani sakar mishi fuska waye shi? Sannan ina kuka je da kika shiga motarsa.”
Da mamaki take kallon shi nan da nan ranta ya ɓaci ta miƙe tsaye tana riƙe ƙugu ta ce “To ina ruwan ka da inda muka je? Ni fa ba na son shisshigi a lamurana ka fita a rayuwata tun da ban gaiyato ka ba malam, ko ka ɗauka yanzu ma kamar da ne da ka kake mini wulaƙanci son ranka? Ni ba tsarar ka ba ce daga yau karka sake ƙoƙarin taɓa jikina tun da kai ba Salim ba ne.” Ta faɗa a fusace tana yin hanyar da ya biyo da ita.
Har ya je bakin kofa ta ji muryartmsa, “Idan na taɓa jikin naki me za ki ?”

A kufule ta juyo ta nuna shi da yatsa ta ce “Tabbas zan koya maka hankali in dai ka yi kuskuren sake taɓa jikina, idan kana tantama ko ganin ba zan iya ba ka sake taɓa ni ka ga me zai faru.” Fuu ta wuce ta bugo mishi ƙofar.
Tashi ya yi tsaye yana zagaye kujerun palon cike da tsananin mamakin ta, yatsa ya ciza ya shaƙi iska ya ce “Ni kuma zan nuna miki Ahmad ba Salim ba ne Khadija, idan har kika mini abin da hankalina ya ki ɗauka tabbas zan miki aika-aikar da za ki ji dama ba ki zo duniya ba.” Wata ƙofa ya bi daga cikin palon yana sauri.

Tana shiga ta samu yaran suna wasa Khadija ce kaɗai take kuka tana kiran “Mama! Mama!”
Cike da tausayin yarinyar ta yi saurin cire mayafi ta ƙaraso ta durƙusa a gaban ta tare da buɗe mata hannu ta ce “Ɗiyar Mama zo gani na zo.”
Jin muryar wadda take nema sai ta juyo da sauri sai kawai ta kama murna, sai a lokacin su Aiman suka ganta sua duk suka yo kanta suna murnar ganin ta shafa kansu ta dinga yi tana ba su haƙuri kamar wasu manya.
Dariya Hussaina ta yi ta ce “Anty Khadija uwar son ɗiya, tun da kika tafi ba wanda ya yi kuka a cikin su sai takrawar ki ita ce duk ishi kowa a gidan nan, yaya Ahmad da ya dawo ya ɗauke ta amma ta ƙi yin shuru dole ya dawo da ita, ga shi Anty Aminatou ba ta dawo ba itama bare ta goya ta duk wanda ya ɗauke ta ba ta yarda sai mama take kira.”
Murmushi ta yi ta ce “Uwarta kaɗai take so ta gani ba ku ba, kai ku matsa wannan ta fiku buƙata.” Ta faɗa tana janye su Nour ta gyara zama tana shayar da Khadija.”
Kuka suka sa Aiman ya dinga ƙoƙarin janye Khadija shi ya maye gurbin ta Andizo ta hana shi, ganin za su ƙara rikita mata lissafi ta kalli Hussaina ya ce “Don Allah ɗauke mini Aiman idan suka gama shi sai a ba shi.”
Ɗaukan shi Hussaina ta yi suka wuce ɗakin Hajiya Babba, kallon su take musamman Khadija da take sauke ajiyar zuciya duk da bacci ya soma ɗaukan ta, hakan ya sa ta ji yarinyar ta ƙara ba ta tausayi domin ta lura ta sha kuka ba kaɗan ba. A hankali ta matso kusan kujera ta kwantar da Nour itama ta kwantar da ita ai kuwa ta buɗe ido za ta fara kuka, saurin ɗaukan ta ta yi ta goya ta da mayafi tana jijjiga ta..

Hajiya Babba ce ta fito tana jan carbi sai yi take tana tofawa a gefe da gefen ta, kallon ta Andizo ta yi tana murmushi ta ce “Hajiya lafiya dai na ga yau ana tofe mana gida.”
Ba ta kuka ta ba har sai da ta zauna sannan ta ɗago ta kalle ta ta tofar da yawu, zama itama ta yi tana riƙe baki ta ce “Yau kuma ni kike tofar wa yawu Hajiya?”
Chapter 41 · 0% Book details