← Book details Andizo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 75

Sashe 75

Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwana uku ta yi tana zaga gari ta je gidan su Hajaru ta samu ba kowa, cikin jimami ta dawo ta tambayi Hajja.
“Hajja ni kuwa lafiya na ga gidan su Hajaru ba kowa? Kuma har dabobinsu duka babu me ya faru?”
Aje mata ɗumamen tuwo ta yi a gaban ta ya sha man shanu da daddawa, sai da ta zauna sannan ta ce “Ai sun tashi shekara ɗaya kenan da tashin su, sun koma can jahar Zander mahaifin Hajaru ya je can yin kasuwanci Allah ya buda mishi, shi ne ya dawo ya kwashe iyalinsa suka koma can, ita Hajarun shekaranjiya Maigari da su Liman suka je ɗaurin auren ta.”
Zaro ido ta yi sai kuma ta yi dariya ta ce “Kai, don Allah? Kuma shi ne ba ku faɗa mini ba?”
“To yanzu ba ga shi kin ji ba, yayunki ma an sa bikinsu saura sati uku, Maigari ya ce ya sanar da mijinki a faɗa miki tun kafin ki haihu ma.”
Wani farin ciki ne ta ji ya ziyarce ta ta rungume Hajja tana faɗin “Gwaurayen yayuna bana sun shirya aure kenan? Kai naji daɗi Alhamdu Lillah ina nan har a yi biki.”

Da dare ta kira Sultan suna tsaka da musayar kalamai ta shigar da ƙorafin ƙin sanar mata da ya yi a sa bikin su Giɗaɗo, haƙuri ya ba ta aka wuce wajen sai da za su sallama ta ce “Amour ina son zan je Zander.”
“Yin me ?” Ya tambaye ta.

“Kasan ƙawata Hajaru? To sun koma can da zama an yi an mata aure ina son na ganta, please kar ka ce mini ba zan je ba don Allah ka dubi girman abota.” Ta faɗa murya na rawa.

“Babu komai zan sa a nema miki ticket daga Niamey sai ki isa can, amma please da an gama biki in kika, je can Zander kwana ɗaya za ki ki dawo Niamey wahsegarin ranar ki dawo Nijeriya, gabaɗaya kewar ki ta addabe ni gaskiya ina jin ba lalle na jure ba a ce nan gaba sai kin yi kusa wata ɗaya kafin ki dawo.”
Haƙuri ta dinga ba shi tana mishi kalaman soyayya mai ratsa zuciya, sai da ta ji yana dariya har da ƙyaƙyatawa sannan suka yi sallama.

Biki ya kankama su Andizo ana ta shige da fice, sosai Sultan ya sakar mata bakin aljihu ta dinga bacaka da kuɗi, kafin ta tafi sai da ta bi duk dangi ta musu kyauta matasa masu zuwa makaranta ta saya musu machine.

Bayan ta je Zander Mama ta yi murna da ganin yadda ta koma babbar mace, Hajaru har da kuka ta rungume Rudwan sai yanzu ta ƙara tabbatar da cewa lalle abotarsu tana nan ita da Andizo sun riga da sun zama 'yan'uwa. Washegari ta koma Niamey.

Da dare Abie ya duro garin tare da su Nour sun ƙara girma da wayo ga surutu, Andizo har da kuka daɗin ni'imomin da Allah ya mata wai yau ita ce da yara uku, a tare suka kwana tana sa su a gaba cikin so da ƙauna.
Da safe sai ga Aminatou ta wasu mata biyu sun lulluɓe jikinsu da hijabi, bayan sun gaisa ne sai duk suka ji wani irin ɗoyi na tashi a palon sai suka fara done hanci, Aminatou ta ce “Munafukai sai ku mata bayani ai ko, ai duk wanda ya ce zai ka da ikon Allah sai ƙarshensa ba, zai yi kyau ba.”
A tare suka ɗago suka durƙusa a gaban Andizo ta yi saurin toshe hanci, kuka suka sa ɗayar ta ce “Don Allah ki yafe mana Khadija a kan cutarwar da muka miki.”
Da mamaki duk suke kallon su Andizo ta kalle su da kyau sai ku. A ta kalli Aminatou ta ce “Su waye wannan Adda?”
Kwafa ta yi ta ce “Ai, dama ba za ki gane su ba, Sabrin ce da Halisa.”
Kwalalo ido waje ta yi ta ce “Subhanallahi! Me ya same su?”

“Su ne suka haɗe baki suka miki asiri kika zama abar tausayi, yanzu kuma ƙaiƙayi ya koma kan masheƙiya shi ne suka rasa in da za su saka kansu sai neman ki suke, ko ni sai da Ummi ta sa baki na ce in naji kin zo zan kawo su su nemi yafiyar ki, amma Wallahi da ni ce ba za yafe musu ba irin halin da suka jefa ko maƙiyi ya ganki a wannan yanayi dole ya zubar da hawaye. Ita wannan da ta yi ƙaryar ƴar gwamna ce ashe ƙarya take babanta ɗan kasuwa ne.” Ta karashe maganar tana nuna Halisa.
Kuka suka sa suna ruƙon ta yafe musu abin da suka aikata mata, Ahmad ya zaburo zai yi magana Hajiya Babba ta hna shi, duk da sun cutar da ita amma sai ta ji sun ba ta tausayi ta share hawaye ta ce “Me na muku kuka cutar da ni?”
Halisa ta ce “Ni saboda ina son Mr J Shi Kuma ya ce ke ce zaɓinsa, kuma daga ke ba ƙari ya rufe zuciyarsa da makulli, na shiga hanyar da zan samo kanshi amma na rasa, kwatsam muka haɗu da Sabrin dama mun yi Ècole da ita nan nake sanar da ita damuwata, ta ce da ni ai ita ta tsane ki domin ta yi ta bin hanyoyi kala-kala dan ta fitar da Aminatou daga gidan Salim ta aure shi ke kika ruguza mata komai, ƙarshe suka yi rabu da Aminatou shi ya sa ta ji ta tsane ki. Sai ga shi ta ji labarin an sa muku rana da Ahmad gefe ɗaya kuma ta ji labarin son da Mr J yake miki, shi muka je wajen wani boka kowacce aka mata aiki aka turo miki baƙaƙen aljannu suke wahalar da ke, shima Sultan Sabrin ta ce a sa mishi ciwon ƙoda duka biyu su lalace ƙarshe kuma a kashe shi.”

Salati duk suka ɗauka Andizo ta girgiza kai ta ce “Ashe haka kike ƙi na Sabrin? Kawai dan na hana ki kashe aure? Ashe dama can zuwan da kike yi gidan nan Salim kike so? Alhamdu Lillah da Allah ya nuna muku iyakarku ko iya haka aka bar ku da shi ya isa ya hana ku sukoni, kun cuci kanku ku tashi mun yafe muku ni da mijina Allah ya sa mu dace.”
Ahmad ya ce “Tab Wallahi Khadija kina da ƙarfin imani da kika yafe musu, maza ku bar mana gida tun da ta yafe muku.”
Tashi suka yi suka fita Aminatou ta ce “Gaskiya Sabrin muguwa ce ashe lokacin da take zuga ni so ne take Salim ya sake ni ita kuma ta aure shi? Sai ga shi ma mai gajeran kwana ne ya bar mana duniyar, Allah ya jiƙan shi da rahama.”
Amin suka ci aka ci gaba da hira. Bayan kamar awa ɗaya suka kaita filin girji ita da su Nour, sai da suka ga tashin su sannan suka dawo gida..

Tana isa Abuja kwana biyu ta yi suka koma London, ranar ta ga soyayya ya nuna mata irin kewar ta da ya yi itama ta nuna mishi tata kewar.

Haka suka ci gaba da rayuwa Sultan harkoki sun ƙara buɗewa ya ƙara girma da cikar zati, Rudwan sai ƙara wayo yake.

_BAYAN SHEKARA BIYAR_
A cikin wannan shekaru abubuwa da dama sun faru ciki har da rasuwar Inna da Maigari, Andizo ta yi kuka kamar ba gobe da kyar da addu'a ta dawo haiyacinta, a lokacin yaranta uku da Sultan namiji da mata biyu, an yi auren su Hassana aka kai su Diffa, itama Farrah an aurar da ita ɗan abokin Sultan ta aura.

Suna zaune a palo Farrah ta kawo musu ziyara ga su Rudwan sun cika palon da hayaniya, sai da ta gaji ta daka musu tsawa sannan suka yi shuru.

A hankali yake saukowa daga matakalar bene idanuwansa sanye da glass ɗan sirri, da sauri Farrah ta miƙe ta taro shi ta rungume shi ya shafa kanta ya ce “My daughter ke dai har yau ba za ki girma ba, ba kya gani yanzu kin zama babba?”
Turo baki ta yi suka, ƙaraso ya zauna a kusa da Andizo tana musu dariya.
Kiran sunanta ya yi ta juyo suka yi fecing ɗin juna, a sanyaye ya ce “Na sa an gudanar da bincike a kan baba ɗazu suka gama suka kira ni, am so sorry Shekaranjiya sojojin Niger sun gama ɗaya daga cikin shugaban 'yan bindiga, garin su tsairatar da mutanen da suka ɗauko wasu suka mutu, a ciki akwai baba wanda ciwon zuciya ya kashe shi, likitoci sun ce ya jima da ciwon damuwa da ta maye gurbin farin ciki ita ta yi sanadiyar mutuwar sa.”
Wani irin ƙara ta yi sai ta zube a jikinsa, da gudu Farrah ta ɗauko ruwa ya yayyafa mata ta farfaɗo. Kuka sosai ta sha ta ce dole ya dakar da duk wani abu sai ta ga fuskar mahaifinta kar su binne shi yanzu, haka ya kira Giɗaɗo ya sanar da su suka ce dama ba an ce sai gobe za a ba su gawar.
A ranar ya nema musu ticket suka yo Niger, saukar yamma suka yi a Niamey ko ruwa ba su sha ba suka wuce Tilaberi.

Kusan kwana ta yi tana jera nafilfili tana roƙa wa iyayenta da su Maigari gafarar Ubangiji, washegari aka kawo gawar babanta ta sa ta gaba ta mishi addu'a, yau ce rana ta farko da ta ga fuskar mahaifinta wanda kullum take fatan ta gani, amma ganin ya zo mata ba yadda ta so ba. Sai da Umar ya je ya janye ta tana kuka wiwi, haka aka kai shi gidansa na gaskiya .
Bayan sati suka koma London Andizo ta fauwala wa Allah lamarinta suka ci gaba da shinfiɗa rayuwa mai kyau da tsafta...
_Alhamdu Lillah a nan na kawo karshen wannan littafin mai suna *ANDIZO* Kuskuren da ke ciki Allah ya yafe mini, darasin da ke cikin Allah ya ba ni ladan. Ku kasance da Maman Nusaiba nan gaba kaɗan in sha Allahu zan zo muku da zazzafan littafi mai sun *ZAWAJUL MUWADDA* Daga jin sunan labarin kun san akwai abubuwa kala-kala a, ciki. Ina sonku masoya one love 🫶🏻_
*Taku har kullum Maman Nusaiba ce🤙🏻*
Chapter 75 · 0% Book details