Sashe 13
Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
“Subhanallahi!” Aminatou ta faɗa ganin yadda suka yi mugun kyau, suna tsayawa ta dinga masa magana bai ji ba hakan ya sa ya ɗago duƙa daidai tsayinta yana kallon ta, kallo irin na wanda ake matuƙar so suna magana, Ahmad ya sa mai ɗaukan photo ya ce ya musu photo a haka ai kuwa sai ganin hasken camera suka yi, Salim ya ɗago kai ya kallo wajen suka haɗa ido da Ahmad ya masa alama da ya juya, ba yanda ya iya ya juya ya kama hannunta suka dinga rausayawa nan da nan dangi aka zo ana ta musu liƙi. Bayan an gama aka buƙaci uwar gida sarautar mata ta shigo fili, gyara mata mayafi Sabrin ta yi ta zaro ɗaurin kudaden da Salim ya ba su ta ce “Ki musu liƙi da kyau ƙawata karki bari a raina miki.”
Murmushi ta yi ta miƙe ta kalli wajen zaman Ummi ta ga ba ta nan, da mamaki ta ce “Ashe da gaske Ummi take gidan ta tafi?”
E kawai suka ce mata ta soma takawa tana nufar su kowa ya zuba mata idanu, Salim ma ita yake kallo yana sakar mata murmushi har ta iso, kallon Andizo ta yi tana murmushi ta iso daf da ita ta rungume ta ai kuwa aka ɗauki tafi da guɗa, Andizo ta yi murmushi ta sake ta ta iso ga Salim ta rungume shi tana faɗin “Félicitation mon mari Allah ya ba mu zaman lafiya.”
Bubbuga bayanta ya yi cike da farin ciki, ya jinjina wa ƙoƙarin ta ya ɗago ta ta yi saurin wayancewa ta soma musu liken kuɗi, yan'uwanta suma suka gabata zo suka ding mata liƙi har da Andizo, sosai suka birge mutane..
Bayan an gama aka tashi lafiya kowa ya ci ya sha ya koma gidansa baƙi kuma aka kai su masauki, Andizo taƙi bin Salim ta ce a wajen Ɗahare za ta zauna, bai musa mata ba dan ya san washegari kamar war haka tana tare da shi, da kanshi ya kaita har ɗakin ya gaishe su sannan ya tafi..
Kasancewar ta mugun gajiya Sallah kawai ta yi ko abinci ba ta ci ba ta kwanta bacci..
Washegari bayan sun karya suka yi shirin tafiya, Ɗahare ta janyo Andizo gefe ta mata nasiha ta ƙara ja mata kunne, ita kuwa sai ma hilla hannayenta take tana cewa “To Adda ai Hajja ta faɗa mini komai, kuma zan yi duk abin da mai hankali ya ce.”
“Yawwa yarinyar kirki haka nake son ji, yanzu mu za mu tafi sai wata rana ki kula da kanki, sannan Hajja ta ce duk abin da kike so iya mijinki za ki tambaya, in ba ya nan ki zo wajen Hajiya babba saboda amanar ki Hajja ta ba ta kina ji na da kyau ko?”
“E Adda ku gaishe da Maigari da su Inna.”
To ta ce mata tana ɗaga musu hannu har motarsu ta tashi, wajen su Umar ta iso da suma suke shirin tafiya ta ce “Hamma ku gaida gida.”
Murmushi Umar ya yi ya ce “To Autar Hajja yanzu dai an girma a daina rashin ji irin na gida kin ji, ban da fita yawo ki yi zamanki a gidanki.”
Dariya ta yi ta ce “Oh ashe nima, ina da gida ban sani ba? To Hamma ina Hamma Giɗaɗo yake?”
Nuna mata shi ya yi cikin mota ya jingina kansa a jikin kujera kamar mai bacci, zagayowa ta yi saitin shi ta ce “Hamma am to a gaida gida.”
Buɗe ido ya yi ya kalle ta da wani irin yanayi, da kyar ya iya cewa “To Surbajo am ban da tsokana kin ga nan ba garinmu kike ba, sannan ki kula da Sallah a kan lokaci har da dare ma in za ki kwanta kike yi kin ji.”
To ta ce masa sannan ta ja baya suka bar gidan, juyawa ta yi suka haɗa ido da Sabrin da suka fito daga part ɗin Aminatou, kallon tsana ta yi wa Andizo.
Andizo ta wani ɗauke kai tana jan tsaki ta yi gaba, kallon farko ta ji ba ta son matar hakan ya sa ta yi saurin shigewa part ɗin Mamma.
“Kut! Ki ji fa Aminatou wannan kishiyar taki tsaki fa ta mini.”
“To kema ban da abin ki meye na kallon ta yarinyar da ba ta fi a kaita gidan raino ba? Ba ki ga ni ban kalle ta ba girmana zan kama na riƙe ta yadda za ta mini biyayya haka Ummi ta ce na yi.”
Tsaki Sabrin ta yi ta wucewar ta..
Da dare aka shirya Andizo aka kai ta ɓangaren su Salim, in da aka fitar mata da ɗakuna huɗu da Palo biyu babba da ƙarami sai banɗaki uku, sosai gidan ya tsaru duk wani kayan more rayuwa Salim ya zuba mata, saboda ya cewa su Maigari kar su wahalar da kansu shi zai yi mata komai. Hajiya Babba ta gama yi wa Andizo nasiha duk suka fita aka janyo mata kofar suka kulle ta ta baya. Tana nan zaune a tsakiyar gadon ta ji zaman ya ishe ta ta yaye mayafin ta fito Palo ta zauna a kan kujera, ruwan da Hajiya Babba ta kawo mata ta ɗauka tana sha ta ji ƙarar buɗe kofar, yi ta yi kamar ba ji ba.
Da sallama ya shigo hannnunsa ɗauke da leda, mamaki ne ya kama shi ganin amarya a palo ta miƙe ƙafa ko ɗankwali babu a kanta, da dariya ya iso tsakiyar palon ya aje kayan ya tsaya yana kallon ta.
Ɗago kai ta yi suka haɗa idanu ta sakar masa murmushi, hakan ya ba shi damar yin magana cike da tsokana.
“Gaskiya ma femme ba ki da kunya, ke yanzu ko kukan rabuwa da dangi ba ki yi ba? Kuma ke da zan ganki a ɗaki sai kuma na zo na ganki a waje?”
Murguɗa masa baki ta yi ta miƙe tare da rike ƙugu ta ce “Yo to so kake zafi ya mini illa? To alƙur'an dole ne ya fito yo ina dalili ni ba mayya ba a kimsa ni a ɗaki a rufe, ko an ce ma ni baƙuwar boka ce?” Tana gama faɗin haka ta sa kuka ta nufi ɗaki da sauri, cikin hanzari ya bi bayan ta yana kiran sunanta amma kafin ya zo tuni ta rufo kofar, da karfi ya tura kofar ta buɗe ya hango can tsakiyar gado ta yi ruf da ciki tana kuka. Gadon ya hayo ya ɗago ta ai kuwa ta birkice ta faɗin “Ba ni ba ce ba ni da kunyar? Alƙur'an in na kwana gidanka in zama karas..”
_Maman Nusaiba ce🤙🏻_
[5/29, 2:07 PM] Ummu Amjad: _*AREWABOOKS@SARATALKASUM88*_
23