← Book details Andizo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 75

Sashe 42

Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ke da Allah matsa ki ba ni guri salbiya, kalle ki da kin ciko sosai amma yanzu kin fara ramewa, an ce a yaye yaran nan amma ƙememe kin ƙi bari a yaye su, ni fa tausayin ki nake ji shi ya sa ma na ce a yaye su amma tun da na ga kin soma zama shashasha gobe zan sa matar Saddiƙu ta zo ta ɗauke su ta tafi da su can sabon gidansu su yi sati sai a dawo da su..”
Shuru Andizo ta yi tana kallon Hajiya Babba, sam ita ba ta so a raba ta da yaranta ko da na wuni ne, kuka ne ya tafo mata ta danne da kyar tana kallon Nour ta kawar da kai gefe ta ce “To shi kenan Hajiya Allah y kaimu goben, nima ina son naje ƙauye na gano su Hajja idan an dawo da su sai mu tafi a gansu har Khadija za mu tafi..”

Murmushi Hajiya Babba ta yi tana faɗin “A to madalla Allah ya kaimu lokacin, haba ko ke fa yanzu a ce yara uku sun kai shekara da wata biyu sai ya yaye su ai kema ki huta ko?”
Gyaɗa mata kai Andizo ta yi ta tashi jiki ba ƙwari ta wuce ɗakinta.
Wanka ta yi ta saka kaya marar nauyi ta fito ta ɗauki abinci ta koma ɗaki, gabaɗaya duk haushin 'yan gidan take ji gani take kamar su suka zuga hajiya Babba take son a yaye mata yara lokacin yaye su bai yi ba, sai da ta gama cin abinci ta ji an kira La'asar ya tashi ya yo alwala ta gabatar. Tashi ta yi ta hau kan gado ta ɗauki wayarta da ji ƙaran shigowar text message, ganin numéro ɗin Amira ce ya sa ta ja tsaki tana tuna wannan mutumi da yake ikirarin wai ya santa a baya, tagumi ta yi ta soma karanta saƙon.

_“Ƙawata don Allah ki yi haƙuri a kan abin da Uncle ɗina ya miki, gabaɗaya ke da shi kun rikita mini lissafi na rasa wa zan fara tambaya, shi ya ce ya san ki ke kuma kin nuna mishi ba ki, taɓa ganin shi. Amma don Allah ki, bari mu haɗu ko da ècole ne mu tattauna.”_
Tana gama karantawa ta ja dogon numfashi, tunani take to wai a ina ma ta san wannan mutumin mai kama da masu allurar ƙwaƙwalwa? Shuru ta yi tana so ta tuna inda ta san shi amma ina, tashi ta yi ta fito gadin ɗin gidan ta samu ɗaya daga cikin kujerun da aka tanadar a wajen ta zauna. Whatsapp ta shiga, tana amsa saƙonni har da na Farrah tana faɗa mata ta yi kewar ta sosai na tsayin shekara guda da ba su ga juna ba, kasancewar Farrah ta bar Nigeria ta ta fi America karatu. Murmushi ta yi tana mayar mata da reply sai ga kiran Farrah ya shigo, cike da zumudi ta ɗauka tana faɗin “Mutanen ƙasar waje kenan Allah ya ba ni kuɗi na hau jirgi ma kawo miki ziyara.”

Daga can ɓangaren Farrah ta yi dariya ta ce “Kai amma kuwa da naji daɗi, zan sa Daddy ai ya biya mini kuɗin jirgin sai ki zo gani na kuma ki zo mini da su Aiman rabona da ganin tun suna jarirai, ke kin kasa musu pictures ki turo mini na gansu.”

“A to mayar da wuƙaƙen Wallahi sam mantawa nake shi ya sa ban tura miki ba, amma da mun gama zan tura miki su har vidéo su.”

“Wow to na gode, yawwa dama ina so mu yi wata muhimmiyar magana da ke Khadija, amma ina so ki ba ni hankalinki ta yadda za ki fi saurin fahimtar in da na dosa..”
Duk da ba ta jin son yin magana sosai amma ba za ta ƙi ba wa ƙawarta ta lokaci ba ta ji me take son faɗa mata, gyara zama ta yi ta ce “To Farrah ina sauraron ki.”

“Yawwa dama na sanar da Mom ne na ce me zai hana ta ɗauko ki ki dawo gidanmu da zama, sai kuma na ga ba lalle wannan gidan surukan naki su yarda ki tafi da yaran nan ba, amma idan aka yaye su na sanar da Daddy ya biya miki kuɗin karatu ya kawo ki nan mu yi karatu tare, domin ina son mu kasance a waje ɗaya, sannan akwai w..”
Ji ta yi an warce mata wayar ta miƙe da sauri tana juyowa, ganin shi ne ta fusata ta ce “Wai kai wani irin baƙin mugu ne Ahmad? Ya za ka zo ka warce min waya ina muhimmiyar magana? Bani wayata tun da ba da kuɗinka na saya ba.” Ta faɗa tana miƙa mishi hannu..
Murmushin gefen baki ya yi ya kashe kiran ya sa wayar a aljihunsa, kallon ta ya yi da wani irin salo ya ce “Ki shirya abokina zai zo jibi ki shirya mishi abincin nan mai daɗi da kika taɓa girka mini can kwanakin baya kafin ki raina ni, sannan ki zo ku gaisa zan gabatar mishi da ke a matsayin matar da zan aura ban da wata ɗaya, ki shirya zama da ni a matsayin miji dan Wallahi aure ni da ke babu fashi..” Yana gama faɗin haka ya juya cikin takunsa na 'yan gayu ya wuce..
Sake da baki Andizo ta bi bayan shi da kallo tana nanata kalmar aure nan da wata ɗaya, jikinta ne ya musu murus ta ja ƙafa ta koma ciki.

Da dare suna cin abinci ta kalli Hajiya Babba kamar za ta sa kuka ta ce “Hajiya don Allah ki ce masa ya ba ni wayata.”
Tsayar da cin abincin Hajiya Babba ta yi ta kalli Andizo ta ce “Waye ya amshe miki waya?”
A hannu ta nuna mata Ahmad da ya yi kamar ba da shi suke ba sai cin abincinsa yake hankali kwance, hannu Hajiya ta miƙa mishi ta ce “miƙo mini wayar yarinya, me ma ya sa ka amshe mata waya?”

Tashi ya yi tsaye yana ɗaukan cup mai cike da lemo mai sanyi ya sa ɗayan hannnunsa a aljihu, sai da ya kurɓa sannan ya ce “Hajiya ki rabu da yarinyar nan wannan faɗan tsakanin ni da ita ne, wani ƙato fa naji suna waya shi ne har take wani kashe mishi murya tana kwatanta mishi nan gidan wai ya zo zance, shi ne nake tambayar ta waye shi nan ta dinga mini rashin kunya ni kuma na amshe wayar na ga ta inda zai zo gidan. Idan kuma kina son wayarki ki biyo ni tana ɗaki ki ba ni haƙuri sai ki ɗauki wayar abin ki.”
Baki Andizo ta saki tana jin ƙaryar da yake sharara mata, kallon su suka yi sauran Mamma ta yi murmushi ta ce “To kai meye naka dan ta yi magana da wani? Amma dai tun da ka ce faɗan ku ne bari mu yi shuru ku je can ku ƙarata.” Ta tashi ta bar wajen.
Hajiya Babba ma kasa cewa komai ta yi, amma dai ta yi mamaki sosai tana jinjina wa wanda har yake da gagarumar sa'ar samun Khadija.

Yana tafiya ta tashi a zuciye ta bi shi ɗakinsa, tana buɗe ƙofar ya damƙo ta yana faɗin “Wa na kama? Ƙaramar marar kunya ke da wayarki sai kin mini duk abin da na sa ki sannan zan ba ki ita.”
Ƙoƙarin kwacewa ta fara yi amma ta kasa, sai da gaji yana kallon ta sannan ya sake ta kafin ya yi wani kwakaran motsi ta wanke shi da mari, da sauri ya ɗago yana kallon ta ta ɗaga hannu za ta sake marin sa sai kuma ta fasa tana huci ta ce “Kai wani kalar jahili ne ina matar yayanka kake cakuma ta? Ko zuwa Islamiyar da ka yi ya tashi a banza? To ka shiga hankalinka ni ba irin wannan shashashun matan ba ce da kuke taɓa jikinsu da sunan wayewa, zan koya ma hankali na ba da jimawa ba.” Ta faɗa tana jan tsaki ta buɗe kofa ta fita.

Da kallo ya bi ta yana murmushi ya shafa kuncinsa ya ce “Kin ci bashi yarinya lokacin ramuwa na nan zuwa.”

Kamar yadda ya faɗa mata bayan kwana biyu Mamma ta same ta ce ta daure ta yi masa girki ba dan halinsa ba ko dan darajar baƙon da zai zo, ba dan ta so ba ta tashi tun ƙarfe goma na safe ta dora girkin shinkafa fara da miya, gefe ɗaya kuma ta haɗa musu kunun aya. Sai ƙarfe ɗaya daidai ta gama aiyukan ta fito tana runtse ido jin cikinta na murɗa mata, ɗaki ta shiga ta faɗa banɗaki ta yi wanka ta shirya cikin doguwar rigar atamfa pink colour. Mai da kwalli kawai ta sa hau kan gado ta kwanta tana riƙe da cikinta, jin ciwon na ƙaruwa ta tashi ta buɗe loka ta ɗauko maganin ciwon ciki ta ɓalli biyu ta sha tana tuna su Nour, hawaye ta ji ya zubo mata ta rungume pillow sam ta kasa cin abincin tun da sassafe da aka ɗauke mata su ta kasa fita balle su yi kuka in sun ganta ta yi zaman ta, amma da ta ji suna shirin tafiya ta tashi da sauri ta leƙa ta taga a kan idanunta suka bar gidan.

Har bacci y fara ɗaukan ta sai ga Hassana ta shiga tana tashin ta, tashi ta yi zaune kafin ma ta ce komai ta miƙa mata waya ta fice.
Kara wayar ta yi a kunne ta ji saukar nunfashinsa, “Khadija please kin ji.”
Lumshe ido ta yi tana jin yadda katararta take mugun ciwo, a hankali ta ce “Me zan yi maka?”

“Ya zo baƙon ki zo ki kawo mishi abinci sai ku gaisa, amma don Allah karki disga ni a gaban shi dan na faɗa mishi kina da hankali da nutsuwa, ki a je faɗan da ke tsakanin mu ki fidda ni kunya please matar yaya.” Ya faɗa cikin sayayyar murya.

Kashe kiran ta yi ta sauka daga kan gadon, banɗaki ta shiga ta wanke fuska ta gyara ta sako hijabi ta fito. Daret kitchen ta shiga sai ta ɗauki kayan abincin da tuni ta haɗa ta aje.
Chapter 42 · 0% Book details