Sashe 38
Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
_“Nana Khadijana damo sarkin haƙuri, a yayin da nake miki wannan rubutun ban sani ba ko za mu sake yin rayuwa da ke a nan gaba ba, ba na jin wannan kwanciyar da na yi zan tashi har na yi rayuwa da ku, hakan ya sa na yanke wani hukunci wanda ban san ya za ku kalle shi ba, ko bayan na mutu Khadija ina son ku ci gaba da kasancewa a gidanmu, saboda ku ɗin mata ne da kowanni namiji zai yi alfaharin samun su a zaman shi na duniya, tabbas ni na kasance mutum mai sa'a da na same ku Khadijatuna, hakan ya sa nake so ko da a ce na mutu ke da Aminatou ku auri ɗan'uwana Ahmad dan ku haɗu ku tarbiyantar mini da yaran da za ku haifa nan gaba. Amma fa Khadija van takura muku ba idan har kuka ji zuciyarku ba ta aminta da wannan hukuncin nawa ba karki bari ayi auren nan ku auri waɗanda kuke so hakan shi ne daidai, idan kuma kun aminta da hakan iyayena za su fi kowa jin daɗin hakan har ma da naku iyayen, amma don Allah kar dan kuna ganin girmana a matsayina na mijinku ku sadaukar da farin cikinku, ba na haɗin ya zama dole idan da haka ma ku ɗauki lokaci kafin auren dan ku shaƙu da juna har ma soyayyar ta ƙullu a tsakaninku. Bissalam daga mijinki abin ƙaunar ki mai tsananin sonki Salim."_
Buɗe ta Aminatou ta yi itama kamar yadda ya yi wa Andizo bayani haka itama Aminatou ya mata jawabi ɗaya bayan ɗaya.
Fashe wa da kuka Andizo ta miƙe tsaye ta saɓa jaririyarta tana kallon su, cikin muryar kuka ta ce “Wallahi ni dai ko Adda Aminatou ta amince ni dai ba zan taɓa yarda na auri Ahmad ba, ni yaya yake a wajena babu maganar aure a tsakani ba da shi, duk wani namiji wajena kallon mace nake masa in dai ba Salim ba, tuni na cire maganar yin aure a babin rayuwata har abada zan raini yarana na ci gaba da zama na kula da su har su girma. Dan haka yau zan bar gidan nan zan muku nisa ta yadda ba wanda zai ganni bare ya haɗa ni da wani namiji da sunan miji, domin ni mijina ɗaya ne dal a duniya shi ne Salim kuma ya mutu ya bar duniyar, dan haka zan zauna na ci gaba da jiran lokacin da zan tarar da shi.” Tana gama faɗin haka ta wuce ɗaki har tana haɗa da gudu.
Itama Aminatou tashi ta yi ta ɗauki 'yarta ta ce “Mamma ki yi haƙuri da abin da zan faɗa, ko ni ba zan iya auren Ahmad ba gaskiyar magana kenan, ina ganin idan na auri Ahmad na ci amanar Salim. Za mu ci gaba da karatu ni da Khadija don Allah karku tayar da maganar nan iyayenmu su ji.” Ta juya itama ta bar wajen..
Gabaɗaya palon kasa motsi suka yi kalamansu duk ya kashe musu jiki, Liman ne ya yi ƙarfin halin faɗin “To abin da zai fi kyau shi ne ku bar maganar nan Alhaji, tun da shi marigayi da y yi wasiƙar nan bai takura ba ya ce dama in suna son hakan, to sun nuna ba sa so a yi haƙuri a rufe maganar zuwa nan da wasu watanni. A yanzu dama ba za su taɓa yarda da wannan hukuncin ba duka watan shi nawa da rasuwa? Ciwon mutuwa bai gama sakin su ba dole ku musu uziri.”
Jinjina kai Abba ya yi ya ce “Tabbas haka ne, in sha Allah za mu bi komai a hankali.”
Sallama ya musu ya tafi.
Suna zaune duk sun yi shuru suka ga ta fito Sanye da hijabi ta goyi Nour shi kuma Aiman ta saɓa shi a kafaɗa tana jan babbar akwati, gabaɗaya kallon ta suka yi, Hassana ta yi saurin tashi ta sha gaban ta ganin za ta wuce, a rude ta ce “Khadija ina za ki tafi kika ɗauko akwati?”
Gyara tsayuwa ta yi ta ce “Zan tafi ƙauyenmu ne.”
Tashi Mamma ta yi ta amshi Aiman, kamo hannunta ta yi ta ce “Babu inda za ki tafi Khadija kina nan gidan, indai dan wannan maganar ce za ta sa ki tafi to ki dawo an fasa, shi wanda yake so ayi hakan dama ai ya ce bai muku dole ba, Hassana mayar mata da jakar nan ciki.”
Lumshe idanu ta yi ta juya ta koma ciki, gabaɗaya hankalinta ya bala'in tashi, ta kuma ƙuɗiri aniyar ko ina za a je ba za ta taɓa yarda ta auri Ahmad ba..
_Maman Nusaiba_
[6/20, 2:11 PM] Ummu Amjad: _*AREWABOOKS@SARATALKASUM88*_
36
Gabaɗaya shuru palon ya yi bayan sun samu Andizo ta koma ciki, Hajiya Babba ta sauke tagumin da ta yi ta kalli Abie ta ce “Saddiƙu kunga wannan maganar a barta kar yaran nan su shiga wani hali, musamman ita Khadija da take shayar da yara uku dole a lallaɓa ta dan kar ta sa abin a ranta a samu matsala, idan aka samu nan da shekara ɗaya nasan za su gane abin da Salim yake son su yi zai zame musu alkhairi.”
Tashi Ahmad ya yi ya ce “Hajiya don Allah kamar yadda suka buƙata ku rabu da su, ni kaina abin ya mini girma gaskiya ba zan iya ba ku yi haƙuri.” Ya wuce fuu saboda tsabar kiɗima ko gabanshi ba ya gani da kyau.
Har ya zo zai gifta ta ƙofar ɗakin Andizo ya ji tana kuka sai sumbatu take.
“Wallahi ba zan iya wannan cin amanar ba, haba mijinmu ya za ka ɗora mana wannan abin mai girma wanda kai kanka kasan daga ni har Adda ba mai yarda da wannan ɗanyan hukuncin, idan har yaranka kake tunanin rayuwar da za su yi nan gaba ina so ka kwantar da hankalinka, domin na yi alƙawarin ni da aure sai dai na lahira in ana yi, kai kaɗai nake so a duniyar nan kuma ka tafi ka barni, dan haka babu maganar na sake haɗa jikina da wani namiji in ba kai ba, da kai na saba kaine ka gyara rayuwata. Allah ya jiƙan ka da rahama ina fatan ka kasance cikin hasken rahama a makwancinka kamar yadda Allah yake ba ka damar ka yi sanadin haska rayuwar mutane da dama, ina matuƙar sonka mijina.”
Girgiza kai ya yi ya murɗa ƙofar ya shiga, a durkushe ya same ta Nour na nutsu-musu a bayanta saboda ta matsu. A hankali ya tsugunna ya sa hannu ya soma kunce goyon, ram ta riƙe hannnunsa ta ce “Karka kunce mini ita.”
“Pordon matar yaya kin fa matse ta sosai ba ki ji ne? Ki ba ni ita mu tafi ɗakina.”
Make mishi hannu ta yi ta miƙe tsaye tana haɗe rai, sauke Nour ta yi ta kwantar a kan gado yarinyar ta soma kuka, zama ta yi tana hararar shi ta gyara zaman hijabi ta ɗauki Nour ta saka ta ciki ta soma shayar da ita. “Malam ka fitar mini a ɗaki da ba ka da kunya, kana gani zan shayar da yarinya ka wani tsare ni da ido kamar maye.” Ta faɗa gyara lulluɓin hijabi.
Hassana ce ta shigo da Khadija tana kuka sai jijjiga ta take, ganin Ahmad tsaye sai ta raɓa ta gefen shi ta iso gaban Andizo ta ce “Anty Khadija ga takwarar ki nan ta addabe mu da kuka a ba ta abincinta.”
Ɗago kai ta yi suka haɗa ido da Ahmad ya juya da sauri ya fice, tsaki ta ja tana hura hanci ta cire hijabin tana faɗin “Dan shegen shigigi za ka wani zo ka tsaye mini a ɗaki ga shi nan Nour har ta haɗa zufa.”
Murmushi Hassana ta yi ta ɗora mata Khadija a cinya ta gyara zama ta soma shayar da ita, harde hannu Hassana ta yi tana jinjina wa ƙoƙarin Andizo, ga ta yarinya ko shekaru 17 ba ta cike ba amma tana shayar da yara uku. Ajiyar ta sauke tana goge hawayen da suka zubo mata tuna yadda Salim yake yi wa Andizo, ko fita ya yi in ya kira ta ya ji ba ta ɗauka ba zai kira Hassana ya ce sai ta je ta ga a wani hali Andizo take ciki ya kira ba ta ɗauka ba, wucewa ta yi ta bar ɗakin.
Da kallo Andizo ta bi Hassana, sai da suka ƙoshi Khadija har ta yi bacci ta kwantar da ita a gadon Nour ta kwanta tana kallon su har bacci ya ɗauke ta..
Ahmad yana shiga ɗaki wayarsa ta ɗauki ringing ya ƙi ɗaukan kiran har wayar ta katse, sake kira aka yi ya ja tsaki ya janyo wayar yana kallon screen ɗin wayar. Ganin mai kiran ya saki baki yana zaro ido, cike da mamaki ya ce “Mr J! Tab lalle za a yi ruwa da ƙanƙara yau.” Ya ƙarashe maganar yana ɗaga kiran ya kara a kunne yana faɗin “Number wa nake gani kamar 'yan ƙasar waje?”
Daga can ɓangaren ya sa dariya ya ce “Wallahi fa nine aboki abubuwa ne suka yi mini yawa, ga damuwa ta hana ni sukoni na kasa samun nutsuwa.”
Riƙe baki Ahmad ya yi ya ce “Iko sai Lillahi wahidul ƙahar! Yanzu kai har akwai damuwar da za ta hana ka sukoni?”
“In sha Allah ina nan tafe zan diro Niger, wannan karon ta can zan bi saboda da ina da wani aiki mai muhammanci a garin nan naku.”