Sashe 20
Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ƙarfe 3:am na bugawa ta yi motsi da nufin ta yi juyi ta ji da gam a an riƙe ta a firgice ta buɗe ido ta ganshi yana ta sharar baccin shi sai sauke ajiyar zuciya yake, fuskarsa ta kalla da ya cusa a ƙirjinta kamar irin na ɗa da uwa wanda ake shayarwa, dogon numfashi ta ja duk wata gajiya da ciwon jiki ba ta jin su sosai har zazzaɓin ya sauka. A hankali ta kai hannu ta shafa fuskarsa, hannnunsa da ya ɗora a in da ba ta so ta ɗauke tana turo baki gaba ta ɗaka masa duka a kafaɗa ta ce “Tashi ka saukar mini a gado nan dai ai ba gidanka ba ne, shi ne har ka wani lallaɓo ka zo ka kwanta mini a jiki ni fa ba ƴar is..” Kasa ƙarasa maganar ta yi sakamakon rufe mata bakin da ya yi. Lumshe ido ta yi tana amsar saƙon sa, hakan ya sa shi ya ɗago da ita ya kwantar da ita ai kuwa ta yi saurin tashi tana aika masa harara tuna abin da ya mata jiya, da hannu ta nuna masa ƙofa ta ce “Ni ka fita ka bar mini ɗaki ko na maka ihu ɓarawo..”
Kanshi ne ya sara ya sa hannu ya dafe ya koma gefen ta ya kwanta, ganin yadda yake juyi yana cije lips sai ta yi gasaƙe tana kallon shi cike da masifa ta ce “To ba yarda ba zan yi ka kwanan mini a nan har da wani riƙe ciki, ni fa gobe ma zan ce wa Hajiya Babba ta kaini ƙauyenmu tun da ba za ka saka ni a ècole ɗin ba, kuma na ga har yanzu ba ka faɗa mini inda Saminu yake karatu ba ballantana ka kaini na ganshi..” Ta faɗa tana zuro ƙafafuwanta.
Saurin buɗe ido ya yi yana kallon bayanta, gashin kanta da ya hargitse ya taɓa ta juyo a fusace tana hura hanci ta ce “Kai ban son a taɓa mini kai fa bori nake, idan kuma kana tantama ci gaba yau mai raba mu da kai sai Allah, alƙur'an idan ba ka kaini wajen Saminu ba sai na koma garinmu..”
Dafe saitin zuciyarsa ya yi a tunaninshi ta manta da babin Saminu zuwa yanzu, wani irin zafi ya ji ya ziyarce shi sam ba ya son jin tana maganar wani namiji daban in ba shi ba. Ganin ba zai tashi ba ta daddage ta kuma ɗaka masa duka a gadon baya ta ce “Tashi na ce.”
Lumshe ido ya yi yana murmushi domin ji ya yi kamar susa take masa a jiki, sam ya ji ba zai rabu da ita ba a wannan yanayin da yake ciki, da dabara ya dawo da ita ta kwanta suna facing ɗin juna, in ban da harara babu abin da take masa ya rasa ta ina zai shayo kanta su jone, can idear ta faɗo masa ya kalle ta yana huci kamar ba shi da lafiya, a hankali ya kamo hannunta ya dora a kan ƙirjinsa ya ce “Ma femme kina so ki rasa ni a daren nan?”
Saurin girgiza masa kai ta yi tana zare ido, daɗi ya ji ya ƙara matso ta ya yi ƙasa da kai ya zo sautin kunnenta ya soma magana cikin raɗa.
“Khadija in dai ba ki so na mutu ki yi duk abin da na ce, sannan kar ki yi kuka kuma karki ce komai duk abin da kika ji..”
Kallon ka raina mini hankali ta yi mishi ta buge hannnunsa da ya ruƙo ta, sai da ta kusa sauka a gadon sai kuma ta dawo ta haɗe fuska ta ce “Amma dai ina faɗa maka karka zama mugu, idan kuma kaƙi jin maganata sai na koma garinmu.”
To ya ce mata ya lallaɓa ya mata wayo ta yarje masa, sai da tafiya ta yi nisa ta ji abin ya fi ƙarfinta ta sa mishi kuka marar sauti ya yi saurin rufe mata baki ya ce kar ta ɗaga murya za a jiyo su,ba dan ta so ba ta yi shuru sai hawaye da ke ta zarya kan kuncinta tana kai masa duka.
Tashi ya yi da sauri ya je ya haɗa musu ruwa ya dawo ya ɗauke ta suka shige banɗaki, sai da ta yi ta masa daru da kyar ya shayo kanta ya mata wanka ya gyara ta sosai sannan shima ya yi ya ɗauko ta suka fito, zaunar da ita ya yi ya gyara musu gadon ya sa sabon bedsheet ya kwantar da ita.. Jikinta ya taɓa ya ji zazzaɓin ya sauka ya sunkuya ya manna mata kiss a kumatu ta lumshe ido tana jin shi ba ta ce komai ba, sai da ya rufe ta da bargo kamar yadda ya ganta sannan ya mike zai fita ya ji ta riƙe hannnunsa ya kalle ta cikin wani irin shauƙi mai wuyar fassarawa, dawowa ya yi ya durkusa ya shafa fuskarta da ta yi fayau ya ce “So nake na tafi kar Hajiya Babba ta zo ta ganni ɗakin nan ta ci ubana”
Sakin shi ta yi ba ta iya ce masa komai ba ya ɗago ta ya rungume ji yake kamar kar ya tafi ya bar ta ita ɗaya a ɗaki, to amma ya zai yi tun da Hajiya ta shiga lamarin? Sai da ta yi bacci sannan ya fita ya janyo mata ƙofa..
Yana zuwa palo ya kwanta kenan ya ji fitowar Hajiya Babba ya yi saurin kwanciya ya yi kamar mai bacci. Sai da ta zo saitin shi ta tsaya, riƙe baki ta so ma kiran sunansa.
“Kai Salimu! Salimu! Tashi ka fitar mana a gida ka koma naka, ashe dama da na ce ka tafi ƙin tafiya ka yi ka zauna a palo har bacci ya ɗauke ga shi asuba ta gabato? To ni ba gantalalliya ba ce maza tashi.”
Miƙa ya yi ya buɗe ido ya ce “Hajiya ƙarfe ɗaya ta yi kuwa?”
Salati ta ɗauka ta watsa masa yatsu biyar tana cewa “Ungu nan dan butar uwaka, ni za ka tambaya ƙarfe ɗaya? To tashi ka tafi..”
Murmushi ya yi ya tashi ya ɗauki wayoyinsa ya ce mata sai da safe ta raka shi da zagi har ya fita...
Daret part ɗin ta ya wuce ya shige daki ya kwanta yana mai jin zuciyarsa wani iri.
Sai da Andizo ta yi kwana biyar cif a ɓangaren su Hajiya Babba, idan kwanan ta ya zo sai ya bari sai hajiya Babba ta yi bacci ya lallaɓa ya je su kwana shi da matarsa, ita kuwa zuwa lokacin sai ta soma sakin jiki da shi saboda da yadda yake kulawa da ita tamkar flower da ke samun barruwa a kodayaushe, gabaɗaya ta soma canjawa idan yana waje ba ta yin magana sai dai ta yi ta satar kallon shi tana murmushi a ɓoye, yayin da shi kuma duk wani motsin ta a kan idanuwansa take yi,wata irin ƙauna yake mata wadda yake jin idan babu ita a gefen shi to rayuwarsa ta yi babban gyiɓin da ba za taba samun mai cike shi ba...
Landi (Litinin)
Sanye take cikin riga da sket 'yan kanti kayan sun mata kyau sosai, idan ka ganta yanzu za ka rantse ba Andizo ɗin da ka sani ba ce a baya, sosai ta canja ta yi haske jikinta ya murje ta ƙara girma, sai dai har yanzu rashin kunyar nan tata tana nan babu bin da ya canja sai ma abin da ya yi gaba, babu lefin tsaye ba na zaune za ta kira Salim yana tsaka da aiki ta yi ta masa kukan wai tsoro take ji ita dai ya zo ya ɗauke za ta zauna a wajen shi, idan ya ga ba ya da aikin kirki a ranar sai ya sa a zo a ɗauke ta ya kai ta wajejan shakatawa sai yamma su dawo. Ganin haka ya sa itama Aminatou in yana kwanan ta sai ta masa waya ta ce tana son su fita shan iska. Da farko bai gane ba saboda yana ɗaukan Andizo ne sai daga baya ya gane ya dage iyakar bakin ƙoƙarin sa wajen ganin ya musu adalci kar ɗaya ta ce ya fi fifita ɗaya a kanta, duk da kuwa yasan Andizo ba ta da matsala sai dai ita Aminatou in yana ɗakinta ta dinga bin hanyoyin da za ta hana shi zuwa ɗakin Andizo a daren ranar, shi kuma sai ya nuna mata wannan ba adalci ba ne ranar kwanan da ba nata ba ta hana shi zuwa inda yake. Wani lokacin sai sun yi faɗa sannan ya bar ɓangaren ta..
Da murna ta ta buɗe motar ganin ta a babbar makaranta, fitowa ya yi ya kama hannunta suka nufi ciki, duk inda suka nufa su ake kallo har suka isa office ɗin babban malamin makarantar..
Bayan sun gaisa Salim ya nuna mishi Andizo da ta yi ƙasa da kai ba ta ce komai ba tun bayan gaisuwar da suka yi.
“Ga ta nan tun watan da ya wuce nake cewa zan kawo ta, to aiyuka sun mini yawa ne.”
Murmushi ya yi ya ce “Ayya Allah sarki Allah ya taimaka ai kuna ƙoƙari ranka ya daɗe, ya sunan ƙanwar taka?”
Kallon Salim Andizo ta yi ta murguɗa baki ta ce “Ka faɗa mishi ni ba ƙanwar ka ba ce, ni ƙanwa Hamma Giɗaɗo da su Hamma Umar ce, su Hassana su ne ƙannenka.”
Da mamaki Malam ya kalle ta Salim ya yi saurin cewa “Malam matata ce ita, sunanta Nana Khadija Umar.”