Sashe 6
Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Sake da baki Mom ke kallon Andizo, sosai ta yi mamaki kuma ta ji daɗi da ba ta ce Sultan ne ya sace ta ba.
“Gaskiya Hajiya mun gode yanzu tun daga Abuja ta Nigeria kika zo har ƙauyen nan duk dan ki sada Surbajo da ahalinta? Wata ɗaya da rabi kenan da sace ta, Muna godiya sosai.” Cewar Giɗaɗo yana riƙe hannun Andizo..
Murmushi Mom ta yi ta ce “Babu komai ai ɗa na kowa ne, to mu za mu koma kar dare ya mana.”
“Haba hajiya ai da kin tsaya kin kwana, yanzu yaushe za ku je Niamey sannan ku wuce Nigeria?” Cewar Umar.
Girgiza kai Mom ta yi ta ce “Karku damu babu komai ai muna da masu tsaron mu, ga wannan kayan Khadija ne na rubuta mata number wayata tana ciki, idan mun je gida za suke gaisawa da Farrah.” Ta faɗa tana tashi ta kama hannun Farrah..
Godiya sosai suka mata, Maigari ya sa aka debo mata kwai aka kai musu bakin mota, Andizo na riƙe da hannun Farrah yara kuma na bin su a baya suna kallon su.. Da kyar Farrah ta saki hannun Andizo sai da Giɗaɗo ya matso ya ce mata wata rana zai kai Andizo har gidansu ta musu kwanaki, da haka aka shayo kanta ta sake ta suna shige mota Andizo na ɗaga musu hannu har suka ɓace wa ganin ta..
Bayan ta koma gida har za ta zauna ta tuna Hajaru, da sauri ta juya ta kalli Hajja ta ce “Hajja wai ina Hajaru take.”
“Hajaru sun tafi wajen biki jiya yau za su dawo, ba ki ga yadda ta damu ba na rashin ki.” Cewar Hajja.
Dawowa ta yi ta zauna ta rafka tagumi ta ce “Allah sarki Hajaru Allah ya dawo da ku lafiya.”
Ta so ta tambayi ina Ahmad sai kuma ta fasa ta tashi ta fita suka shiga gari...
Washe gari Maigari da kanshi ya kira Salim ya sanar da shi ai wasu mutane sun dawo da Andizo, sosai Salim ya nuna farin cikin shi ranar ko aiki bai tsaya ya yi ba ya dawo gida cikin ɗoki ya nufi part din Mamma da Sallama. Amsa mishi suka yi Mamma ta kalle shi tana faɗin “Da alama wani abu mai daɗi ya faru tun da na ga yau ka yi fara'a.”
“Mamma an ga Khadija yanzu haka tana gida.”
Da sauri Ahmad ya ce “Da gaske?”
“Kwarai ma kuwa Maigari ya kira ni ɗazu ya ce wata mata ce tun daga Abuja ta ceci rayuwarta ta dawo da ita har gida jiya, ba na ce maka naji kamar Khadija ta kusanto ni ba kaƙi yarda da magana ta, to ga shi dai ta tabbata an ganta.” Ya faɗa yana faɗaɗa murmushin sa.
Hamdala suka yi gabaɗaya, Hajiya Babba ta ce “To yanzu ni abin da nake son a yi, kun ga azumi ya kusa zuwa kawai a je a ɗaura auren nan a kawo ta gidan nan ko mun huta da yawan kiran ta da yake, ni ban taɓa ganin soyayya irin taka ba Salimu.”
Wani sanyi ne ya ziyarci zuciyar Salim ya miƙe tsaye ya iso gaban ta yana ƴar dariya ya ce “To Hajiya ai sai ki sanar da su Abie ni gobe za mu tafi ni da Ahmad da Abdoul mu gano ta.”
Mamma dai na kallon ɗan nata tana murmushi, sosai ta ji daɗin samun Khadija ko ba komai ɗanta zai samu nutsuwa..
Sai da ya jima suna ta tattaunawa a kan lefan da aka haɗa, sai tambaya yake ko akwai abin da ba a saya ba? Mamma ta ce “A'a mun sayi komai tashi je ka abin ka..”
To ya ce ya tashi ya nufi part ɗinsa, shima Ahmad part ɗin su Abie ya nufa dan ya, sanar musu ganin Khadija..
Yana shiga ta tarbe shi da murna ta sha kwalliya, ganin yadda fuskar shi take dauke da fara'a sai, abin ya ba ta mamaki amma ta kawar ta ɗauko masa ruwa, sai da ya sha ya ruwan sannan ta dube shi ta ce “Mijina wannan fara'ar fa?”
Hannayenta ya ruƙo ya ce “Alhamdu Lillah Khadija ta dawo gida jiya..”
Wata irin zabura ta yi tana dafe ƙirji ta ce “Me ka ce? Da gaske ko wasa kake mini Salim?”
Ganin yadda ta ruɗe ya kamo ta ya zaunar ya ce “Ya aka yi kika ruɗe?
“To ba dole na ruɗe ba na yi farin ciki amaryarmu ta baiyana, kai gaskiya na yi matuƙar farin ciki da wannan albishir yanzu yaushe za ka kaini na gano ta?”
Dariya ya yi yana girgiza kai ya ce “Ki bari dai a kawo miki ita tukun, gobe za mu je ni da Ahmad da Abdoul. Gaskiya ina ƙara gode wa Allah da ya ba ni ke a matsayin matata, Allah ya miki albarka yadda kike son abin da nake so na gode sosai Ma famme.”
Murmushi ta yi ta miƙe ta kawo masa abinci ta ce “Bari naje na haɗa ma ruwan wanka kafin ka gama.”
To ya ce mata sannan ta wuce ɗakinta da mugun sauri.
Tana shiga kulle kofar ta haye kan gado ta zare wayarta da ke jikin caji ta danna wa Sabrin kira, tana ɗaura kafin ma ta ce wani abu ta ce “Hello Sabrin akwai matsala babba na tunkaro ni,wai kina ji yarinyar nan da na sa aka mata kurciya wai jiya ta dawo..”
Sai da Sabrin ta yi ashar ta fi goma sannan ta ce “To amma ya aka yi haka ta faru? Ko dai kuɗin da muka kai masa ya yi kaɗan ne? Kinga maza-maza ki tanadi kuɗi gobe zan kaiki gidan wani boka aikinsa sha yanzu magani yanzu, ke har maganar haihuwar sai mu masa ki riga ta samun ciki..”
Ajiyar zuciya ta sauke tana share hawaye ta ce “Ina jin zuciyata kamar za ta fashe Sabrin, amma dai ya ci amanar mu tun da har ya bari ta dawo gida, gobe za su tafi ki zo mu tafi ki kaini so nake wannan karon a kashe ta kowa ma ya huta..” Tana faɗin haka ta katse kiran ta miƙe tsaye tana zagaye ɗakin, gabaɗaya baƙin kishi ya rufe mata idanu sai tsine wa Andizo take tana shan alwashin daga gobe ta gama numfashi a duniya sai ta ga ta yadda za a kawo mata ita a matsayin kishiya...
Next Fage
_Maman Nusaiba ce_
[5/25, 1:36 PM] Ummu Amjad: *Arewabooks@saratalkasum88*
*🥏+966577675904*
19
Washegari tun ƙarfe shida da rabi Salim ya gama shiryawa ya zauna zaman jiran Ahmad da Adoul, da am jima sai ya kalli agogo ya ja tsaki ji yake kamar ya yi fiffike ya ganshi a gaban sahibarsa.
Sai da ƙarfe bakwai ta buga ya miƙe zai fita sai ga Aminatou ta fito, kallon shi ta yi cike da mamaki ta ce “Mon chéri ya kuma na ga ba ku tafi ba? Ai ni na ɗauka yanzu kun yi nisa da gari.”
Tsaki ya ja yana sa hannu a aljihu bai ce mata komai ba, kallon shi take tana jin zuciyarta na ƙara tunzura ta a kan abin da take son aikatawa, kishin mijinta take na gaban kwatance. Lumshe idanu ta yi ta buɗe shi a kansa tana yaba kanshi, wankan da ya ɗauka ya matuƙar ƙara mata kishin sa a zuciyarsa. Ya sha ƙanana kaya t-shirt orange da baƙin wando kayan sun matuƙar ƙara fito da ainahin kyawunsa, hannnunsa tsadaddan agogo ne baƙi haka ma takalmin ƙafarsa baƙi ne, sumar kansa ya taje ta yo baya sai sheƙi take. Wani kalar fitinannan ƙamshi yake tashi a jikinsa, sai hura hanci yake saboda ɓata masa lokaci da suka yi..
A hankali ta ƙara matsowa gaban shi ta kai hannu ta shafo kwantaccan sajensa mai ƙara wa fuskarsa kyau, kallon ta ya yi cikin idanu ya sa hannu ya tallafo ta ganin tana son yi wa kanta masauki a jikinsa.
“Ma famme ya aka yi? Ko akwai abin da kike buƙata?” Ya faɗa yana raba ta da jikinsa.
Kasa ba shi amsa ta yi in ba dan tana son fita ba da ba za ta bari ya yi tafiyar nan ba, buɗe idanuwanta ta yi ta danne duk wani son zama a jikinsa ta wayance da cewa “Ba komai kawai naji kana wani ƙamshi na musamman ne, ba na so wata ta yaba wankan mijinmu.” Ta faɗa tana jan hancinsa..
Murmushi ya sakar mata cikin jin daɗin kalamanta ya ce “Haba ai kema kin sani ku biyu kun isheni, daga Khadija na rufe ƙofa, wannan ƙamshin da kika ji sabon turare ne na sayo jiya shi ne na saka, kinga naji oda a waje bari na je ko sun zo gabaɗaya sai mun dawo..” Ya faɗa yana fita daga palon.
Bin bayan shi ta yi da kallo wani abu ya tsaya mata a maƙoshi, sosai ta ji haushin saka turaren da ya yi dan zai je wajen wata kucakar budurwarsa, kwafa ta yi ta zauna zaman jiran Sabrin..