← Book details Andizo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 75

Sashe 30

Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun da suka kama hanya surutu take mishi tana ba shi labarin rayuwarta ta baya, shi in banda eh ko a'a babu abin da yake ce mata saboda ransa bai so tafiyar nan ba. Ita kuwa ko a jikinta ƙarshe ma bacci ta yi abin ta har sai da suka zo kofar gidansu ya tsayar da mota ya soma tashin ta.
“Khadija tashi mun zo yau dai ga ki ga Maigari.”
Saurin buɗe ido ta yi ta kalli waje daga ta ga su Maigari a zaune suna kallo motar, zabura ta yi za ta fita ya yi saurin kulle motar yana kallon ta cikin yanayin damuwa. Ɗago kai ta yi suka haɗa ido ta turo baki tana kawar da kai, ruƙo ta ya yi ta kwanto kanta a jikinsa sai ta yi saurin tashi tana kallon shi, da mamaki ta ce “Shin ba ka da lafiya ne?”
Girgiza mata kai ya yi bai ce komai ba, ta kai hannu ta dafa saitin zuciyarsa ta ce “Haba ni dai ban yarda ba mu sauka mu gaisa da su Maigari ka wuce asibiti a duba lafiyarka, ji fa yadda ƙirjinka daga ciki da yake bugawa kai ba ka jin ciwo ne?” Ta faɗa tana ɗaga rigarsa ta leƙa wai ko za ta ga abin da yake sa wajen bugawa da sauri-sauri..

Dariya ce ta subce mishi ya riƙe hannunta, shi wani lokacin mamaki da al'ajabi take ba shi in ta yi masa wani abin kamar babbar mace, wani lokacin kuma in ta yi wata maganar shirmen sai dai y yi gum da bakinsa ko kuma ya yi dariya, idan kuma ya ce zai yi dariya mai yawa ta hau sama ta tayar da rigima. Cire glass ɗinsa ya yi da ya dora a goshi ya aje a gefe, murmushi ya yi ya ce “Khadijana kenan, Allah ya nuna mini ranar da za ki gama gane komai na rayuwa ki zama babbar mace, yanzu ke ba ki san yadda zuciya ke bugawa ba a jikin ɗan'adam? Lalle da sauran ki har yanzu.”

Hararar shi ta yi ta ce “To dama haka zuciya ke bugawa?”

“E mana to ke ba ki taɓa jin taki zuciyar na bugawa kamar haka ba?”

“Kai Alƙur'an a'a, ni kam ai ba ni da wannan.”

Kyale ta ya yi ganin in ya biya ta sai su wuni a motar, buɗe mata ya yi ta fito shima ya fito, Andizo da murna ta nufo su Maigari tana faɗin “Maigari ba za ka tashi ka mini barka da zuwa ba?”

Dariya ya yi ya kalle ta yana yaba kiwon Salim ganin yadda ta yi shar abin ta ga cikinta da ya girma kamar ya kai wata bakwai, tashi ya yi ya ce “A'a, lale maraba da uwar masu gari uwata ta kaina ni kaɗai a duniya sannun ku da zuwa.”
Dariya ta yi ta rusuna saboda ta so ta durkusa sai ta kasa ta ce “Ina kwanan ku? Barkan ku da rana Liman ya gida ya su Goggo?”

A tare suka amsa suna washe baki dan ta birge su, ga ta ta samu kulawa ta musamman sai ka rantse da girman Allah ba Andizo ba ce mai wuni tana neman fitina.

Ciki suka nufa har Maigari yana gaba suna biye da shi, a farfajiyar gidan ya hango Ɗahare shanya kayan wanki ya kira sunanta, saurin juyowa ta yi ai kuwa suka yi ido huɗu da Andizo ta zaro ido ta ce “La Surbajo Hamma ce nake gani ko kuwa dai gizo5ne idanuwana ke mini kamar kullum?” Ta faɗa tana murza ido dan tabbatarwa.

Dariya Andizo ta yi ta iso gaban ta ta ce “Adda Ɗahare ni ce dai ba gizo ba ne nake miki.”
Rungume juna suka yi suna ta murar ganin juna, jan ta ta yi suka iso bakin rumfa ta shiga ɗaki ta tashi su Hajja tana sanar da su zuwan Andizo. Duk da mamaki suka fito suka ganta tsaye da ƙaton cikinta tana dariya, da sauri ta nufe su Hajja ta yi saurin taro ta tana faɗin “Ke ki bi a hankali ba ki gani ba ke kaɗai ba ce? Har yanzu kenan ba ki daina wannan shirman naki ba?”

Rufe fuska ta yi tana dariya dafa cikin ta kalli Inna ta ce “Innata ina su Hamma?”
Mirmu Inna ta yi ta kamo hannunta suka zauna ta wuce ta kawo mata ruwa mai sanyi, sai bayan ta sha sannan Inna ta ce “Su Hamma sun kusa dawowa Maigari ya aike su nan ƙauyen kusa da mu wajen ɗaurin auren ɗiyar abokinsa.”

Ɓata fuska ta yi kamar za ta sa kuka ta juyo ta kalli Salim da ke gefen ta zaune, fakar idon su Inna ya yi ya taɓa hannunta suka haɗa ido ya kashe mata ido ɗaya ta banka mishi harara.

Bayan sun gaisa sun ci abinci Salim y musu Sallama zai tafi ya dubi Hajja ya ce “Hajja ga ta ba na kawo ta ta muku sati ɗaya, zan dawo rana itayau na ɗauke ta saboda nan da kwana goma zan yi tafiya..”

Riƙe baki Hajja ta yi ta ce “To amma ai da ka barta a nan har ka je ka dawo daga tafiyar, ka ga cikin jikinta ya tsufa haihuwa yau ko gobe gara tana wajen manya a dinga lura da ita, duk da nasan a can ɗin ma akwai Hajiya Babba.”

Murmushi ta yi ya sassa kai ƙasa, dsam ya san za a rina wai a saci zanin mahaukaciya, a sanyaye ya ce “A a Hajja, idan tssn nan ba za take kula tana zuwa awon ciki ba, amma a can ita da abokiyar zaman ta tare suke zuwa a yi musu komai su dawo, sannan makaranta take zuwa boko da arabi idan tana nan karatun nata zai ja baya. Idan zan tafi a wajen Hajiya Babba za ta zauna har na dawo, kai ko na dawo ɗin ma ba lalle ba ne ta dawo ɗakinta sai bayan ta haihu, sannan ma Hajja cikin ai bai kai lokacin haihuwa ba..”

Kallon Inna Hajja ta yi irin me za ta ce game da hakan, Inna ta ce “A to shi kenan in dai a wajen Hajiya Babba za ta zauna, Allah ya sauke ta lafiya shi ne fatan mu.”

Godiya sosai ya yi ya musu sannan ya miƙe ya fita, ɗaka mata duka a cinya Ɗahare ta yi ta ce “Shashasha mijin naki zai tafi ba za ki je ki masa Allah kiyaye hanya ba? Maza tashi ki je ki masa sallama.”
Kuka ta sa saboda dukan ya shige ta, kama ta Ɗahare ta yi ta tashi tsaye ta yafa mayafi ta nufi waje tana faɗin “Sai na haɗa ki da Hamma da ya zo in ce mishi dukana kika yi daga zuwa na, dama ai Mai hankali ya ce ba wata kewa ta da kuka yi naƙi ji yanzu ga zahiri na gani.”

Fuska haɗe Inna ta ce “Haba Ɗahare ya za ki ɗaka mata duka haka? Ba ki ganin ba ita kaɗai ba ce.”

“Yo ai gara da ta mata haka, ka zo da mutum ya ce zai koma ta kasa tashi ta mishi Allah kiyaye hanya?” Cewar Hajja.
Shuru Inna ta yi jin Hajja ta sa baki a maganar.

Har zai kunna motar ya ganta ta fito daga gida tana share hawaye, kallon ta yake yana murmushi a tunaninshi kukan rabuwa da shi ne take, sai da ta zagayo saitin da yake ya buɗe glass ya kalle ta da wani irin yanayi ya ce “Ma femme ko ba ki son zama mu koma?”

Girgiza kai ta yi ta ce “Adda ce ta dake ni a cinya wajen sai zafi yake mini.”
Da mamaki ya kalle ta sai kuma ya kawar da mamakin ya ce “Yi haƙuri da zarar na zo ɗaukan ƙi zan rama duk abin da ta miki kin ji shalele.”

Gyaɗa mishi kai ta yi ya ɗauko kuɗi ya miƙa mata ya ce ya tafi ta ɗaga masa hannu, sai da motarsa ta ɓace wa ganin ta sannan ta koma ciki, ranar har dare ba ta sake yi wa Ɗahare magana ba ta ce sun ɓata sai bayan kwana biyu za su shirya.

Da dare su Giɗaɗo suka dawo daga wajen biki nan suka samu Andizo, ai kuwa ta yi ta murna tana rungumar su ɗaya bayan ɗaya tana faɗin “Alƙur'an na yi kewar ku su Hamma.”

Dariya Iro ya yi yana cire babbar rigarsa ya jefa wa Ɗahare ya ce “Kai su Andizo an zama manya iyye, Adda don Allah ki wanke mini kayan nan yanzu ki shanya mini shi va ne so su kwana a haka.”

Hararar shi ta yi ta wurgo mishi rigar ta ce “Wallahi babu wanda zan yi wanki da daren nan, jaka kuka mayar da ni da za kuke kawo mini kayan wanki duk lokacin da kuka ga dama? To ba zan wanke ba.” Ta faɗa tana tashi ta bar musu wajen.

Dariya Umar ya yi ya ce “Yawwa ƙanwata karki sake musu wanki tun da ke baiwarsu ba ce.”

“In ka sake ce mini ƙanwarka sai na masga maka mari, saboda ka raina ni ni ce ƙanwar taka?”

Tashi Inna ta yi ta karkade zaninta ta ce “Yo Umar ai ya fiki da shekara ɗaya dole kuwa ya ce miki ƙanwarsa.”

Dariya suka sa ita kuma Ɗahare taƙi fitowa daga ɗaki sai cika take tana batsewa saboda maganar Inna, Hajja ce kawai ta goyi da bayanta ta ce kar ya kuma ce mata ƙanwarsa..
Chapter 30 · 0% Book details