Sashe 64
Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 9 min read
Kamar da minti biyar sai suka ji ana buga ƙofa, da sauri ta murɗa sai ta ji a kulle ta juyo ta kalle shi, idanuwansa a rufe suke amma yana jin duk abin da take, sai da ya ji ƙaran murɗa key an buɗe kofa tukun ya buɗe ido yana kallon su. Baki ta saki tana kallon su cike da mamakin ganin su a tare, dariya Ahmad ya yi ya ce “Yar rainin hankali matsa ki ba mu hanya mu wuce mana.”
Ba ta san lokacin da ta matsa daga bakin ƙofar ba sai jin muryarsa ta yi a gaba da ita, juyowa ta yi da sauri ta iso gaban shi tana shirin kama hannunsa ya yi saurin tarewa, hararar shi ta yi ta kalli Ahmad ko zai ce wani abu amma sai ta ga ya yi murmushi hakan ya ƙara saka ta a kogin tunanin anya Ahmad yana da hankali kuwa? Taya kana ganin wani ƙato yana taɓa hannun matarka amma ka yi shuru ba ka ɗauki ƙwaƙwƙwaran mataki ba? Ko dai ya koma shaye-shayen ne ba ta sani ba? Ajiyar zuciya ta sauke jin ana jijjiga ta ta kalle gefen ta, tuna maganarsu ta ƙarshe ya sa ta juyo tana faɗin “Amira kinga abin da nake faɗa miki game da ɗan'uwanki ko? Na faɗa miki ba zai canja ba kawai sai dai wani ikon Allah taɓa jikin mace shi ba wani abu ba ne a wajen shi, to ki ɗauke shi ku bar mini gida kar ya kashe min aure, ko da yake ai shi kansa wanda nake ganin zai ji ba daɗi in wani ya taɓa ni dariya ma ya yi.” Ta faɗa goge hawayen da suka zubo mata.
Dafa ta Amira ta yi ta ce “To ai shi Uncle ɗin shi ne mijinki ni kuma yaya Ahmad na aura, ina fatan ku yi rayuwa mai albarka da samun zuri'a ɗayyiba ƙawata. Nasan kin shiga ruɗani ko? To idan kika kwantar da hankalinki in muka huta zan sanar da ke duk abin da ya faru har aurenki ya dawo kan Uncle, ya kamata mu tafi mon mari na ga Uncle yana harara ta.” Ta faɗa tana dariya. Baki Andizo ya saki tana kallon Amira jin maganarta ta yi tamkar saukar aradu, wai ita ce aka aura wa Sultan? Anya ba mafarki ba ne? Runtse ido ta yi da ƙarfi ta ce “Amira don Allah ki sabga mini mari ko zan tashi daga wannan baccin da nake mai cike da ruɗani.”
Dariya suka sa Ahmad ya miƙa wa Sultan hannu ya ce “Aboki ya kamata ku kwanta ku huta ka ga gobe za ku koma Nigeria, daga nan kuma ku wuce London za ku sha wahala sosai in ba ku yi bacci yanzu ba. Khadija sai da safe gobe za mu dawo ki ji komai daga bakina ba daga bakin Amira ba, wanda kike dakon soyayyar sa a zuciyarki shi kika aura ba zaɓin tsohon mijinki ba, don Allah ba na son jin komai daga gareki ki kwantar da hankali ku yi bacci cikin salama da safe za ki ganmu.”
Kamar gunki haka ta zama sai in ta juya ido ta kalli Ahmad ta kalli Amira da Sultan, har suka fita Sultan ya dawo ba ta motsa daga inda take ba, tunani barkatai take ta rasa wanne za ta ɗauka ta yi amfani da shi. Ƙarasowa ya yi tare da sunkuyawa ya manna mata kiss a kan laɓɓanta ta yi saurin kallon shi, hannu ya sa ya ɗago ta jiki ba kwari ya ce “Ki yi haƙuri na ɓoye miki da aka yi my wife, mu je ɗaki mu kwanta gobe za ki ji komai.”
Ba dan ta so ba ta saki jiki ya ruƙo ta suka nufi ɗaki ya zaunar da ita bakin gado, ƙugu ya riƙe yana tuna irin kalar wahalhalun da ya sha kamar zai sheƙa kafin ya same ta a matsayin mata, murmushi ya sakar mata ya ce “Kin wahalar da jaririyar zuciyata my wife yanzu da sai dai ki ji labarin na mutu, yake Allah ni ya kira a matsayin mijinki sai ga shi kin zama tawa har abada, tashi ki yo alwala nima zan je na yo mu yi Sallah mu gode wa Allah da ya nuna mana rana mai ɗunbin albarka.” Ya faɗa yana fita daga ɗakin. Ita dai umarnin Ahmad take bi da ba dan haka ba da tuni ta tayar da aljannu dan dolen sa ya mayar da ita inda suka ɗauko ta, ta matsu gari ya waye domin ta ji yadda aka shirya wannan badaƙalar ba tare da ta ankara ba, miƙewa ta yi ta shige banɗaki.
Bayan ta fito sai ga shi ya dawo da jallabiya milk haɗe da hula fara a kansa, kallon shi ta yi a zuciyarta ta furta “Ma sha Allah.” Ba ta san ta fito fili ba sai da ta ji ya ce “Yaya ta mini kyau ko?”
Sunkuyar da kai ta yi cike da jin kunyar maganar da ta yi a zuciya ta fito fili, darduma babba ya shinfiɗa irin wadda ake shanfiɗawa idan an fita yawon shan iska, gaban wardrobe ya isa ya buɗe ya fito mata da red ɗin hijabi, tsayawa ya yi a gaban ta ya buɗe ya sa mata sannan ya kamo hannunta ya iso da ita kan dardumar shi kuma ya yi gaba kaɗan da ita, iƙama ya tayar suka soma gabatar da Sallah kamar yadda addini ya tanadar. Bayan sun gama ya juyo ya dafa kanta ta ji wani abu mai sanyi ya mamaye zuciyarta, lumshe ido ta yi tana shaƙar ƙamshin turaren da ya sa, firgicin da ta shiga ne ya sa ko kaɗan ba ta ji ƙamshin da ke tashi a jikinsa ba sai yanzu. Addu'oʼi ya yi ta jero musu na samun zaman lafiya, ita kuwa ta kasa kunne tana jin daɗin sautin muryarsa da yadda yake yin addu'ar cikin kwarewa, sosai ta yi mamakin hakan domin a sanin ta da shi a baya ya ce mata shi ko Sallah bai ma san yadda ake yi ba. Bayan ya gama ya yi mata tambayoyi game da addini ta ba shi amsa ya ja kumatunta ya ce “Ustaza Khadijatu.”
Duk da tana jin haushin shi amma sai da maganar ta ba ta dariya ta yi murmushi tana kai hannu ta ɗora a kan nasa, a hankali ya zare mata hijabi ya tashi ya fita ta bi bayan shi da kallo, gabaɗaya ya rame sai tsawon kawai ta girgiza kai tana kawar da kanta gefe. Bai ɗauki lokaci ba ya dawo hannunsa ɗauke da plate da ledoji biyu, a gaban ta ya dire ya cire jallabiyar ya zauna, saurin runtse ido ta yi tana faɗin “Meye haka kuma?”
Dariya ya yi ya miƙa hannu zai taɓa ta ta kauce ta ja baya, cikin zafin nama ya damƙo ta ya ɗora ta a kan cinyarsa, shuru ta yi jin bugun zuciyarsa ta ɗago ta kalli ƙirjinsa, ɗinki ta gani a ƙirji wajen ya yi huce ta ɗago kai suka haɗa ido, so take ta tambaye shi amma ta kasa hakan ya sa ya kai hannu ya shafa wajen ya ce “Ai ya warke yanzu sabon aiki za a mini nan da kwana biyu, amma zan sanar da likitan ya bari sai nan da sati ɗaya in na gama hutawa sai mu tafi ki raka ni, kuma dama ƴarki ta matsa sai ta zo na ce ta bari zan kawo ki har inda take sannan ta haƙura.”
Tausayin shi ne ya lulluɓe ta amma ba ta ce mishi komai ba, kazar ya diba ya kawo bakinta ta kauce ya kalle ta yana dafe kai ya ce “Oh my wife! Ki yi haƙuri fa na ce ki ci kazar nan mu kwanta.”
Ganin yadda ya narke mata kamar mai shirin yin kuka sai ta amsa tana wani yatsina fuska, haka ya dinga ba ta har ta ƙoshi sannan ya saukar da ita daga kan cinyarsa ya zuba milk ya ba ta ta sha, goge hannnunsa ya yi ya ce “To nima a ba ni.”
Zaro ido ta yi ya ɗage mata gira ɗaya ta sunkuyar da kai, ta rasa me ya sa Sultan sam shi ba shi da kunya ko ta sayan gishiri. Zamewa ya yi ya ɗora kansa a kafaɗarta yana faɗin “Yunwa fa my wife Kar ta illata miki miji, yau fa ko breakfast ban ci ba.”
Saurin kallon shi ta yi ya gyaɗa mata kai ya ce “Yes da gaske zamuɗin ganin ki ya sa naji duk ba na jin yunwa, sai yanzu naji kamar an mini yasa.”
Murmushi ta yi ta janyo kazar ta dinga ba shi yana ci yana mata wani irin kallo wanda ya sa har sai da ta dara ta ce “Wannan kallon fa?”
“Wallahi ji nake kamar na fi kowani namiji sa'a a duniya, yau dai ga ƴar kwailata ta zama babba kuma na auri abuna, ɗazu ma sai da Ahmad ya ce mini mijin kwaila na ce ai tafi matarsa hankali.”
Murmushi ta yi tana girgiza kai ta ci gaba da ba shi abincin har ya ƙoshi. Bayan sun gama ta ɗauke dardumar shi kuma ya ɗauke kayan abincin ya mayar, yana dawowa ya ɗauko towel ya cilla mata ta cafe tana kallon Shi da alamun tambaya, hanyar banɗaki ya nuna mata ta maƙale kafaɗa, bai ce mata komai ba ya wuce ciki bayan kamar minti uku ya fito ya yo wajen ta.
“Mu je mu yi wanka za mu fi jin daɗin kwanciya.”
Ja baya ta yi ta ce “Tab! Da kai zan yi wankan?”
“Kwarai da gaske da mijinki za ki yi wanka.”
Ƙin yarda ta yi ganin tana ɓata mishi lokaci ne ya ɗauke ta cak ya shige banɗaki, duka take kai mishi amma ya ƙi aje ta sai jin ta ta yi a cikin ruwan ɗumi. Rasa me za yi ta yi a wannan lokacin ganin ya soma cire mata kayan jikinta, ta kulle ido gam tana jin shi ya gama wanke ta tas ya saka mata towel ya dauko ta suka fito. A gado ya aje ta ya dauki ƙaramin towel ya goge mata kanta da jikinta tana zaune tana ji, bayan ya gama shirya ta shima ya ja ya zauna a gaban madubi ya shafa mai ya feshe jikinsa da ture mai daɗin ƙamshi wanda ya sa ta buɗe ido ta kalle shi a sace amma ta kasa ɗauke idanuwanta. Bayan ya gama ya juyo suka haɗa ido ya ƙaraso bakin gadon ya hau ya janyo ta ta takure a waje ɗaya, bai matsa mata ba ya rabu da ita ta kwanta yadda take so, ƙarshe ma can ƙuryar gado ta koma ya yi ta magana amma ta yi mirsisi ta kyale shi. Kasa haƙuri ya yi sai da ya dawo da ita jikinsa a haka ya rufe su a bargo babu jimawa bacci ya ɗauke ta, shi kuwa kasa baccin ya yi yana kallon yadda take juyi a kansa tana sharar baccin ta son rai, sai karfe ɗayan dare sannan bacci ya ɗauke shi.