Sashe 17
Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tun da suka fito Andizo ta dinga kallon waje, hakan ya sa Ahmad ya buɗe mata glass yana ce mata ƴar ƙauye ta zo birni ta ce eh ɗin ai ba shi ya kawo ta birnin ba.
Kamar an ce ta kalli madubin jikin motar ta ga wata baƙar mota na bin su, ba ta kawo komai a ranta ba ta kawar da kai sai dai hankakinta bai kwanta ba.
Sake dubawa ta yi ta ga duk in da suka bi motar na bin bayansu, ta dawo ciki tana cewa Ahmad “Ka ga wata mota na bin bayan mu tun da muka tafo daga wajen masu abinci..”
Hannu Ahmad ya kai ya gyara madubin gefen shi ya hango motar na biye da su, gudu ya dinga yi amma still tana bun su, abin ya ba shi mamaki sai ya samu waje ya yi packing dan tabbatar da su ɗin suke bi ko kuwa dai rainin hankali ne irin na wasu matasan..
Yana kallon su suka zo wucewa madubin motar a buɗe yake, hakan ya ba shi damar ganin su biyu ne duk sun saka facemark haɗi da glas. Sai da ya tabbatar sun yi nisa sannan ya canja hanya, sosai yake mamakin kallon da suke mishi, ita kuwa Andizo takurewa ta yi a jikin kujera da ta runtse ido wannan gardi take gani yana kallon ta, sosai abin ya yi tasiri a zuciyarta tsoro ya baibaiye ta kafin su isa sai rawar ɗari take. Hankalin Ahmad bai kawo kanta ba saboda burinsa bai wuce ya kai ta wajen Salim ya dawo ya ƙara bincikar masu motar nan..
Yana gama packing a wani babban wajen shaƙatawa ya kalle ta, dariya ya yi ya ce “Matsoraciya tashi mu je.”
Da kƴar ƙafafuwanta suka iya daukar nauyinta ta bi bayan shi sai waige take duk ta firgice, can ta hango shi cikin matasa sun kai goma kamar wadda aka tsikara ta kwasa a guje ta nufe shi.
Abdoul ya matsa daga kusan Salim ya ce “Ku matsa daga nan ga amaryar Oga nan ta zo.”
Kallon ta yake da kyau yana nazarin fuskarta, tashi ya yi tsaye ya taro ta suka haɗe da wani irin sauri ta faɗa jikinsa ta ƙanƙame shi ta fashe da kuka, ƴar dariya ya yi a tunaninsa kewar shi ce ta sa ta kuka, sai da ya ji kukan na gaske ne sannan ya ɗago ta ya ga yadda jikinta yake ɓari.
“Subhanallahi! Ma femme lafiya kike kuka ? Waye ya taɓa mini ke ya amshi hukunci?”
Saurin komawa ta yi ta kuma ƙanƙame shi idanuwanta a rufe sai kuka take, hakan ya sa Abdoul ya kalle su ya ce “Hmm ai amaryar can ta Salim ba dai rigima ba, ku kalla fa daga zuwa duk ta sa ya susuce kamar ba Soja ba..”
Na gefen shi ya ce “Yo ita mace ina ruwan ta da wani muƙaminka in dai ta shirya rikita ka, ko kai shugaban ƙasa ne idan kana gaban ta kallon sa'anta take maka.”
Dariya suka sa suna faɗin “Ai kuwa dai to muma Allah ya aurar da mu.”
Ɗaukan ta ya yi suka koma ɗayar shinfidar da babu koma a kai, zaunar da ita yake ƙoƙarin yi amma sam taƙi yarda ya aje ta, hankalin Salim ya tashi dan bai taɓa ganin ta a cikin wannan yanayin ba sai yau. Ƙara rungume ta ya yi a hankali ya tashi ya saɓa ta a kafaɗa ya nufi motarsa, su Abdoul na tsokanar shi ya yi banza da su.. Saka ta ya yi a motar ya zagayo ya shigo ta yi saurin ruƙo hannunsa tana shasshekar kuka, cikin wani kalar yanayin damuwa ya ƙura mata idanu, hannunta ta ɗaga masa irin na yaro in yana so a ɗauke shi, ba yadda ya iya ya janyo ya ya rungume a cinyarsa ya tayar da motar suka bar wajen.
Yadda take shigewa jikinsa duk ta hana shi yin tuƙin da kyau Allah dai ya kaisu lafiya bakin wani hôtel, ya fito da ita ya kulle motar ya nufi ciki. Masu tsaron wajen suka sara mishi kai kawai ya jinjina ya wuce, duk wanda ya haɗu da shi sai ya kalle su..
Sai da ya kaita har kan gado sannan ya aje ta, zama ya yi ta matso da sauri ta ɗaura kanta a kan cinyarsa murya na rawa ta ce “Ma.. Mai hankali don Allah ka kaini garinmu kar su sake sace ni.”
Hannu ya sa ya cire mata hijabin ya gyara mata kwanciyar, a hankali ya shiga shafa kanta yana tofa mata addu'a lura da ba ta cikin haiyacinta.
Ajiyar zuciya ta dinga saukewa ɗaya bayan ɗaya tana ƙara riƙe shi, har ya ɗauki waya zai kira Ahmad sai kuma ya fasa ya ci gaba da mata addu'a. Sai da ya tabbatar ta daina sumbatun sannan ya sunkuya saitin kunnenta ya ce “Dijan mai hankali.”
Buɗe idanuwanta ta yi ta juyo da fuskarta suka yi facing ɗin juna, hannu ya sa ya share mata hawayen ya ce “Wani abu kika gani a hanyar ku ta zuwa nan?”
Gyaɗa masa kai ta yi wasu hawayen suka zubo mata, rayuwar da ta yi a gidan Sultan ta faɗo mata ta yi saurin komawa jikinsa ta ce “Wallahi mugu ne shi har giya yake sha, kuma ba ya Sallah wai ya ce ni matarsa ce an ɗaura mana aure.”
Mamaki da al'ajabi suka rufe Salim ya ɗago ta ya zaunar ya ce “Waye shi wanda ya ce ke matarsa ce?”
“Shi ne wanda ya sace ni wai so na yake, labarin komai ta kwashe ta faɗa masa, amma ba ta faɗi sunanshi ba kuma ba ta ce Mom mahaifiyarsa ba ce.”
Wani irin kishi ne ya turniƙe Salim jin har ya taɓa canja mata kaya, nan da nan idanuwansa suka yi jajur kamar an watsa mishi barkono, jijiyoyin kansa suka fito ran maza ya ɓaci. Saurin rufe idanunsa ya yi cikin karaji ya ce “No Khadija me ya sa kika bari ya taɓa jikinki? Me ya sa?”
Gani yadda ya birkice sai ta fashe da kuka ta tashi tsaye ta haye kansa ta tallafo fuskarsa cikin kuka ta ce “Don Allah ka yi haƙuri mai hankali tsoron ka nake ji da ka yi haka, kuma fin ƙarfi ya nuna mini ban bari da kaina ba, ni to dama ban faɗa maka ba. Don Allah ni dai karka zama mugu irin shi, haka yake yi wa masu aikinsa ya yi ta shan giya...”
Ƙanƙame ta ya yi yana fitar da numfashi fat! Fat! Fat! Gyara mata ruƙo ya yi ya kwanta ya ɗaura ta a kanshi gabaɗaya jikinsa rawa yake, da sauri ya janyo musu bango ya rufe su.
Andizo ta yi shuru tana sauraron bugun zuciyarsa, sosai ta tsorata da yadda yake mata ta kalle shi a duhu ta ce “Mai hankali ba ka da lafiya ne?”
Hannunta ya janyo ya ɗaura a saitin zuciyarsa yana huci ya ce “Khadija kin ji yadda zuciyata ke bugawa saboda tsananin kishin ki da nake? Wallahi ko waye shi a duniyar nan sai na binciko shi na hukunta shi, sai na sare masa hannanyen da ya taɓa jikinki, tabbas zai gane bakin rijiya ba wajen wasan makaho ba ne..”
Ita dai shuru ta yi tana jin yadda yake sumbatu, haƙuri ta dinga ba shi tana cewa ya tashi su tafi asibiti jin jikinsa ya ɗauki zafi sosai, shi kuwa a yadda yake ji in ba Sallah ba da ta zama wajibi a gareshi ba ya jin akwai abin da zai tayar da shi daga kan gadon nan..
Jin tana masa kuka ya ce “Ki daina kukan ranar Litinin zan kaiki makaranta.”
Murna ta maye gurbi kukan sai ta shiga fada masa kalar jakar da take so da kayan rubutu, ya ce duk zai saya mata da haka bacci ya dauke ta, shi kuma da kyar ya samu bacci ya ɗauke shi...
“Sir da gaske nake maka yau ɗin nan mun ga wata mai kama da wadda ka ba mu photon ta, sai dai mun gansu tare da wani..”
A zabure ya tashi daga kan gado ya saki murmushin da rabon da ya yi shi tun wayarsu ta ƙarshe, “Ina kyautata zaton ita kuka gani tun da kun ce nan cikin gari aka kawo ta, amma dai ku ƙara bibiyar su.” Ya faɗa yana nufar wata kofa inda matan turawa ne tsirara wasu daga su sai bra da pant suma da su da babu duk ɗaya suna wanka. Kashe wayar ya yi ya nufi wajen ruwan wankan sai yanzu ya ji nauyin da ya danne masa zuciya ya ragu, zama ya yi a bakin ruwan sai kuma ya faɗa ciki. Da sauri wata daga cikin matan ta biyo shi ta shiga ta same shi, ƙoƙari haɗa jikinta da nashi ta ke ya matsa ya ba ta waje, sake biyo shi ta yi ya ce “Stop Jennifer.”
Kamar ba ta ji shi ba ta kuma biyo shi, hakan ya sa ya fita daga ruwan itama ta biyo shi kamar rakumi da akala. Gaban shi ta sha tana masa maganar wai ko bai ganta ba ne tana ƙoƙarin faɗa wa jikinta, tsawa ya daka mata. “He! Don't touch me Jennifer. ” Ya faɗa a zafafe yana nuna ta da hannu ya ƙara da cewa “I've got a wife.” Yana faɗin haka ya hankaɗa ta ta faɗi tim ya yi gaba, gabaɗaya hankalinsa ya tashi tun da suka sanar da shi sun ga mai kama da ita, ya ƙagara su gama buga wasan nan ko ya koma gida, saboda gani yake su Bansh ba sa yin aikin yadda ya dace, in shi ne da cikin sauƙi zai samo ta. Da wannan tunanin ya je ya hau mota ya bar wajen..
_Maman Nusaiba ce🤙🏻_
[6/1, 11:42 PM] Ummu Amjad: _*AREWABOOKS@SARATALKASUM88*_
25