← Book details Andizo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 75

Sashe 59

Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Amira na ta ƙoƙarin ganin ta samu Ahmad a waya amma ko ta kira ba ya ɗauka, hakan ta tuna lokacin da Andizo ta sanar mata yana dawowa daga aiki ta saici lokacin ta nufi gidansu. Bayan ta shiga gidan ta gaishe da su Mamma tana tambayar su ya labarin wajen jikin Andizo suka ce da sauƙi ɗazu suka kira aka ce ta samu bacci, gyara zama ta yi ta ce “Mamma ina Ahmad yake?”
Kafin Mamma ta ce wani abu sai ga shi ya iso palon sanye da ƙananan kaya na zaman gida, kallon shi ta yi tana miƙewa tsaye ta ce “Yaya Ahmad ina wuni?”
Sai da ya zauna sannan ya ce “Lafiya lau Amira ya gida?”
“Alhamdu Lillah, dama wajen ka na zo.”
“OK to muje ɓangarena.”
Gaba ya yi ta bi bayan shi tana ta addu'ar Allah ya sa kar ya ƙi amincewa buƙatar da ta zo mishi da ita...

_Maman Nusaiba ce_
[7/5, 3:39 PM] Ummu Amjad: ADZ

45

A palo ya mata masauki ta zauna tana bin ko'ina da kallo, wajen fes-fes da shi sai ƙamshin turaren wuta ke tashi mai Sanyin daɗi, lumshe ido ta yi ta shaƙi ƙamshin sai kuma ta yi saurin buɗe ido tuna abin da ya kawo ta. Gyara zama ta yi sai ga shi ya kawo mata ruwa a gora ya zauna tare da miƙa mata fuska a sake, amsa ta yi itama ta mishi murmushi ta ce “Merci.”
Kawar da kai gefe ya yi sai da ta gama sha ya juyo ya fuskance ta ya ce “Amira me ke tafe da ke?”
“Alfarma na zo nema a wajen ka yaya Ahmad, duk da nasan da wahala ka mini ita saboda girman ta.”
Da mamaki ya ce “To wannan ɗin wata irin alfarma ce mai girma haka Amira? Kawai ki faɗa naji in dai ba ta fi ƙarfina ba in sha Allah zan miki, ko kin manta ke ƙawar matar da zan aura ce wadda take ji da ita sosai?” Ya faɗa yana ƙare mata kallo.
Sunkuyar da kai ta yi ta sa hannu ta goge hawayen da suka zubo mata, shi ne kallon ta yake har ta zame ƙasa ta durƙusa a gaban shi tare da haɗe hannaye waje ɗaya ta ɗago kanta hawaye sun wanke mata fuska kuka ya kwace mata. Zaro ido Ahmad ya yi yana faɗin Subhanallahi! Amira Wai me ke faruwa? Ki sanar da ni don Allah.”
Tsayar da kukan ta yi ta ce “Ban san da wata fuska za ka kalle mi ba yaya Ahmad, amma idan har za ka mini wannan alfarmar ka ɗauke ni da kowacce irin siffa ma na yarda in dai a kan buƙatar da na zo maka da ita ne.”
Tagumi ya yi yana jiran ya ji wannan buƙata ta Amira da ta saka ta kuka, goge hawaye ta yi ta ɗora da cewa “Don Allah ka ji tausayin Uncle ɗina Yaya Ahmad har ita kanta Khadija ka musu rai kar ta dalilin ka a yi gawa biyu a lokaci ɗaya, Khadija tana matuƙar son Uncle nasan kaine ka hure mata kunne ta fasa kula shi har aka kai ga sa muku rana, idan da za ka ga halin da Uncle Sultan yake ciki Wallahi ko wata irin ƙiyayya kake mishi dole ka tausaya mishi. Abin da ya kawo ni wajen ka ina so ka janye maganar auren ka da Khadija ka bar wa Uncle ita don Allah, ni ban san da wata kalma zan yi amfani ba wajen fahimtar da kai irin raɗaɗin da zuciyar Uncle take ciki ba tun ranar da ta sanar da shi an sa muku rana kar ya sake kiran ta, tun daga lokacin ba a kuma gane kanshi ba ko da ya farfaɗo sunan Khadija ne a bakinsa yana mai roƙon ta kar ta rabu da shi, sanin da ta mishi a da daban ne yanzu ya dawo mutum kamar kowa ta dalilin wa'azin da take mishi, ka yi hakuri don Allah ka je can ƙauye ka ce musu ka janye auren ka da ita shi zai aure ta..”
Baki Ahmad ya saki yana kallon Amira jin abin da take faɗa masa, ta ya zai ce ya fasa auren Khadija a yayin da take cikin matsananciyar rashin lafiya? Dogon numfashi ya ja yana kaɗa kai ba ya ji akwai abin da zai sa shi ya fasa auren ta, idan kuma ya tuna irin halaccin da Sultan ta mishi a rayuwa sai ya ji gwiwarsa ta yi sanyi, ɗago kai ya yi zai yi magana Amira ta yi saurin tarar numfashinsa ta ce “Ina so ka kalli wannan photuna da video ka ga halin da yake ciki, idan har ka kalla ba ka tausaya mishi ba ka mishi sadaukarwa, to ba zan sake bibiyar ka ba a kan wannan maganar zan ce mishi ya haƙura idan kuma ya mutu To Allah ya jiƙan shi..”
Jiki ba kwari ya amshi wayar da Amira take miƙo mishi, a hankali ya kunna video nan take Sultan ya bayyana a video, an sa mishi na'urori hanci da hannu da saitin zuciyarsa ya rame sosai fuskarsa hanci kawai kake gani a miƙe, cikinsa ya faɗa kamar na macen karya yadda kasan ba a taɓa zuba mishi wani abu mai suna abinci ba haka yake, magana yake amma ba a ji sai ya ga Amira ta iso kusa da shi tana mishi magana tana shafa kansa hawaye na bin kuncinta. Ɗayan vidéo ya kunna in da ya ganshi a zaune Mom na ba shi shayi yana sha da kyar, Amira ta amshi shayin Mom ta fita ya kalle ta ya ce “Thank you Meera.”
Girgiza kai ta yi ba ta ce mishi komai ba ya ɗora da cewa “Amira ki je ki kawo mini Khadijata kin ji, ni nasan ƙarya ta faɗa mini kawai dan ta ga na dame ta da kira ne ta ce an sa mata rana da abokina, shi fa da kansa ya ce ta ce ba za ta taɓa auren shi ba tun da ya kasance ƙanen mijinta, yanzu kuma sai ta ce wai shi ne za ta aura ba ni ba? Nasan Khadija tana sona.” Ya ƙarashe maganar yana dafe ƙirji Amira ta yi saurin miƙa mishi ruwa, sai da ya sha ya kuma ce mata ta je ta gano masa Khadija kuma su dawo tare, to ta ce ta taimaka mishi ya koma ya kwanta, har ta miƙe tsaye ya ce “Idan kuma da gaske abokina ne zai aure ta bai kyauta mini ba, domin na ɗauki shekaru ina sanar da shi irin son da nake mata shi kansa a lokacin kallon mahaukaci ya dinga mini, har cewa yake wa ya sani ba ko Khadijar tawa aljana ce na ce naji watarana zan kawo mishi ita ya ganta ashe ma a gidansu take rayuwa, bayan ya san ita ce me ya sa ai mini haka?” Ya faɗa yana juyar da kai gefe, haƙuri Amira ta ba shi tana kuka ta sanar mishi za ta tafi ta zo mishi da Khadija har cikin asibiti sai ya saki murmushi yana kallon ta daga nan vidéo ya ƙare.
Ɗago da kai ya yi idanuwansa sun yi jajur ya kalli Amira da ta sunkuyar da kai ƙasa tana jira ya gama ta ji me zai faɗa a kan ɗan'uwanta, idan har wannan video bai sa ya ji tausayin shi ba ta yi alƙawarin ba za ta kuma zuwa gidansu ba abotar ma da Khadija za ta daina ta koma ta ci gaba da rarrashin ɗan'uwanta.

“Amira in dai saboda da maganar an sa bikinmu ne abokina ya shiga wannan halin na janye auren Khadija na bar mishi ita, Wallahi ban san abin ya kai har haka ba da ba za akai wannan lokacin Sultan bai auri Khadija ba, zan sanar da kowa na fasa auren Khadija na sadaukarwa mishi da ita har abada tashi muje.”
Wani irin matsanancin farin ciki ne ya lulluɓe zuciyar Amira ta ɗago da sauri tana dariyar murna hawaye na zubo mata, kafafuwansa ta dafa kamar wata zautacciya ta ce “Da gaske kake yaya Ahmad ka bar wa Uncle Khadija? Kai waiyo Allah Alhamdu Lillah, na gode sosai yaya Ahmad Allah ya saka maka da alheri lalle ka cika abokin kwarai.”
Murmushi ya yi ya ce “Da gaske ne mana tashi mu tafi.”
Tashi ya yi ta miƙe ta bi bayan shi bakinta ya ƙi rufuwa, a palo suka samu Hajiya ta mata sallama suka fita waje. Har bakin mota ya raka ta ya sanar da ita gobe ta zo su tafi ƙauyen su Khadija ta ganta, cike da farin ciki ta amsa da to ta ja mota ta wuce, da kallo ya bi motar yana girgiza kai har ta fita sannan ya dawo..
Chapter 59 · 0% Book details