← Book details Andizo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 75

Sashe 11

Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga can ɓangaren muryar mace ta amsa da cewa “Bansh is at Dubai, Oga what happing?”

Tsaki ya ja yana faɗin “Ɗan iska shi ba zai dawo daga Dubai din nan ba? To ki sanar da shi akwai problem ne mai girma, idan kun yi waya ki sanar da shi zan tafi Germany yau da yamma, akwai wata kadarata da nake so ya luran mini da ita kafin mu gama buga bal ɗin can zan dawo, ko da ba a gama ba zan sa shi ya kawo mini ita in da nake.”

“OK sir, amma naji kana cewa za ka sa a ka maka ita nan wace ce ita? Dama kana yin soyayya ne.”

“Ke ban son hauka ki yi abin da na ce, kin je na ce miki mace ce? Idan har aka samu matsala a lamarin nan kin san hukuncin ki daga ke har shi ba sai na maimaita miki ba..”

A ɗan tsorace ta ce “Yes sir na sani.”

Katse kiran ya yi ya rufe computer ta tashi toilet ya nufa ya sakar wa kansa ruwa ko zai ji sanyi, mamaki da kalmomin da take faɗa masa sun hana shi sukoni, bai taɓa tunanin za ta ba shi matala ba ganin ita ba wata babba ba ce, ga shi yanzu sai wahalar da zuciyarsa take kuma tana ambaton za ta auri wani bayan da aurensa a kanta. Ajiyar zuciya y sauke ya kashe ruwan ya fito kamar marar lafiya.. Kaya ya saka ya fesa turare kaɗan ya fita, direba ya taso da sauri zai buɗe masa mota ya ɗaga masa hannu alamar yau ba ya son a raka shi. Komawa ya yi yana tambayar kansa ko mene ne ya sa Ogan nasu zam silent? Dan bai taɓa ganin shi a cikin irin wannan yanayin ba. Shiga ya yi ya ja motar a matsiyacin gudu ya bar gidan..

Andizo wunin ranar kalaman Sultan ne ke mata yawo a rai, ko da duka tafi Islamiya kasa samun nutsuwar ɗaukan karatu ta yi da an jima sai ta ja, numfashi ta tafka tagumi. Da dare ma kasa cin abincin kirki ta yi sai ta samu waje ta kwanta ta rufe ido kamar mai barci, tana jin Hajaru ta zo su tafi wasa amma ta yi ƙememe ta ce ita ba za ta fita ba yau ba ta jin ƙarfi a jikinta, dole ta haƙura ta rabu da ita ta koma gidansu...

Kwanaki na ta tafiya bikin Andizo ya kankama, yayin da ita kuma ta tsage sai murna take za ta tafi birni tuni ta manta da shafin Sultan da kwana biyu da maganar su tunanin maganar shi duk ta hana ta sakat, amma da Salim ya zo ya ɗauke ta duka fita bayan gari ya yi ta lallaba ta yana sanar da ita irin makarantar da zai saka ta mai kyau ya dinga kai ta wajen wasa, hakan ya ƙara mata zumuɗi son auren...

Ana ya gobe ɗaurin aure sai ga babbar mota ta faka a kofar gidan Maigari, Farrah ce ta fito sanye da riga da wando kanta ya sha gyara ga wani lalle da aka mata mai kyau baƙi da ja, fitowa direban ya yi ya tare wani yaro ya ce “Yaro nan ne gidan su Khadija amarya ko?”

Gyada kai ya yi ya ce “E bari ma na kira maka ita yanzu aka gama waƙe suka shiga ciki.” Kafin ya ba shi amsa ya nufi gidan a guje.
Bai fi sakan ashirin ba sai ga su a tare, hango wadda ke tsaye ya, sa Andizo sa ihun murna ta zo da gudu suka haɗe suka rungume juna suna dariya, ganin haka direban ya dauko mata akwatinta ya miƙa wa Andizo da take taɓa gashin Farrah. Amsa ta yi tana juya akwatin ta ce “Gaskiya naji daɗin zuwan ki ƙawata, muje ciki ki huta.”
Dariya Farrah ta yo suka nufi gidan, har za su shiga direba ya mata kira ta dawo ya miƙa mata wayarta da ta manta...

Washe gari aka ɗaura aure da safe ƙarfe goma da rabi, sosai kofar gidan Maigari ta cika taf ta al'umma, wasu daga makotan kauyukansu wasu daga ruga, ga kuma tawagar ango da iyayensa. Sai washe baki Salim yake ana ba shi hannu ana masa barka..
Bayan an yi Sallar Azuhar Ahmad shi da Abdoul suka ce suna son a ba su amarya tafi da ita da duk wanda zai je ganin gidan amarya, Maigari ya ce Hajja ta ce ba za a tafi da amarya ba sai gobe su zo da safe ko rana sannan sun gama komai. ..
Suna barin wajen Ahmad ya dinga dariya yana kallon Salim da yake zaman jiran su, ganin dariya da suke Salim ya ce “Kai ba son hauka fa, lafiya la tafo kana dariya ?”
Shiga ya yi ya zauna sannan ya ce “Hajiya Hajja ikon Allah ta ce ba za a ɗauki yau ba sai gobe.”
Murmushi ya yi ya ce “To ai an yi mai wahalar dai ku jira ni naje mu gaisa sai mu tafi? Tsokanar shi suak dinga yi yana murmushi ya fi ɗakin da aka ba su ya zauna yana jiran zuwan ta..

R
Takalmanta a hannu ta shiga,
[5/28, 11:38 PM] Ummu Amjad: _*AREWABOOKS@SARATALKASUM88*_

22

Ko rabin tafiyar ba su yi ba Andizo tana ta surutu bacci ya yi gaba da ita, ba ta farka ba sai da aka shigo cikin gari Ɗahare ta tashe ta tana faɗin “Surbajon Hamma tashi mun zo garin su mai hankali.”
Idanuwanta ta buɗe ta soma murza su tana kallon ko'ina, kallon direba ta yi ta ce “Kai buɗe mini madubi mana.”
Har zai yi magana sai kuma ya tuna kashedin da Salim ya masa, ya ce masa duk abin da ta ce tana so a yi mata su lallaɓa a zo lafiya kar ya bari ta yi kuka. Buɗe mata madubin ya yi hakan ya yi daidai da danger ta tsaida su, kanta ta miƙo waje tana ƴar dariya ta ce “Oh ni gyatumar masu gari, alƙur'an yau mai hankali zai ga samfurin jin daɗin kawo ni birni da ya yi, kalli ka ga wasu igiyoyin shanya da aka sa a kowanni titi ko ta ya ma za a shanya kayan?” Ta taɓe baki tana kallon su. Motar kusa da su ta kalla ai kuwa suka haɗa ido da wata kyakkyawar budurwa ta sha kwalliya har da glass, murmushi ta sakar wa Andizo tare da ɗaga mata hannu, itama ta ɗaga mata ta ƙara zuro kanta ta ce “Daga ina kike? Ni aure ni aka mini ga shi nan za su kai ni gidan mai hankali mutumin kirki, ke ina za ki je?”
Dariya budurwar ta yi itama ta ƙara miƙo kai ta ce “Ni makaranta zan tafi, ke yanzu aure ne aka miki ko dai karatu ne kika zo yi?”
Taɓe baki Andizo ta yi ta ce “A to ni dai daga gida aure aka mini, mai hankali ne ya ce zai saka ni a ècole ni da Saminu, ni suna na Khadija.”
Jinjina kai ta yi tana shirin mata magana aka ba da hannu sai ɗaga mata hannu ta yi, itama Andizo ta ɗaga mata tana cewa “Kema da alama za ki yi kirki.”

Janyo ta ciki Ɗahare ta yi ta ce “Haba meye haka? Kawai daga ganin mata sai ki dinga mata magana haka ake yi? To nan dai ba garinmu ba ne kina yiwa kowa magana za a sace ki.”
Ɓata rai ta yi ta ce “Yo to kurma zan zama kawai dan na zo birni? Alƙur'an duk wanda ya mini magana sai na mishi.” Ta faɗa tana harɗe hannayenta..
Ba ta sake ce mata komai ba suka ci gaba da tafiya..

Sun shigo cikin gari sosai a jikin wani gida motar su Andizo ta tsaya direban ya kalli su Ɗahare ya ce “Hajiya a nan ku za ku sauka na tafi da amarya in da ango yake, daga can za su iso wajen dinner da ake yi..”
Sanin an musu bayanin komai sai suka sauka wata mota ta zo da ban ta ɗauke su, ita kuma Andizo na kallon su ko motsi ba ta yi ba sai ma shafa warwaron da aka sa mata take tana yaba kyan shi. Sai da suka yi tafiyar minti goma sha biyar sannan suka iso wani madaidaicin gida mai kyau, hon ya yi aka buɗe masa ƙofa ya shiga harabar gidan. Yana gama packing ya fito daga motar ya zagayo saitin Andizo ya dan rusuna ya ce “Madam ki zauna karki fito Oga ne zai zo ya fitar da ke..”
To ta ce masa ya juya ya fice a wajen..

Tun da suka yi hon yake tsaye jikin taga yana kallon motar ransa fes, ganin direban ya tafi ya nufi hanyar fita da sassarfa, sai da ya iso bakin ƙofa ya tsaya ya nutsu da kyau.
Cikin takunsa irin na zaratan maza yake takowa fuskarsa kamar gonar auduga, yana isowa ya buɗe mata motar ya ɗan ja da baya yana jiran fitowar ta. Murmushi ta sakar masa sannan ta fito tana ƙare masa kallo, baki ta riƙe tana faɗin “Kai ma sha Allah, tubuli wayukulufullahu ta'ala, ka ga yadda ka yi kyau? Alƙur'an kayan ma irin nawa ne.” Ta faɗa tana zagaye shi.
Hannu ya buɗe mata ya ce “Zo naji ɗumin matata.”
Ba muso ta iso ya sanya ta a jikinsa ta yi luf kamar mage, cikin nuna zallar farin ciki ya ce “Alhamdu Lillah Khadija kin zama halaliyata matar aurena, Allah ya bar mu har gidan aljanna..”
Shuru ta yi ba ta ce masa komai ba dan har wani bacci-bacci ta ji na son kama ta dama ta gaji, jin ba ta ce komai ba ya ɗago ta yana kallon yadda ta rufe idanu, a hankali ya hura mata iskar bakinsa. Turo baki ta yi ta ce “Babu kyau dai ina jin bacci kake busa mini iska a fuska.” Ta faɗa tana buɗe idanuwanta.
Chapter 11 · 0% Book details