← Book details Andizo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 75

Sashe 57

Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wasa-wasa Andizo ta shafe sama da sati uku amma babu abin da ya canja sai ma ƙaruwa da ya yi, ba ta iya cin abinci sai dai a yi koko a ba ta shima da kyar take sha, saboda ƙurajen bakin da wasu sun mutu wasu za su kuma kadowa maganar ma da kyar take, kwana take tana kuka tana faɗin jikinta zafi yake, maganin gargajiya Ahmad ya dinga amso mata ana mata amma kamar ƙara mata ciwon ake, wani magani da ya amso yau da kwana biyu a kasuwa da yaji ana tallar sa ya kawo aka mata wanka da shi gabaɗaya jikinta ya ƙara rikicewa, ƙuraje ƙanana kamar na zafi suka kaɗo mata ta dinga kuka tana sosawa, ranar babu wanda ya yi bacci a cikin su a kanta suka kwana suna tofa mata addu'a har asuba tukun ta samu bacci ɓarawo ya yi sace ta. Ganin lamarin na ƙara girmama Hajiya ta kira su Maigari ta sanar da su duk abin da ke faruwa, hankali tashe Maigari ya ce ga su nan zuwa garin..

Da safe suka sauka, suna shigowa gidan ya yi daidai da ta kaɗo a guje daga ciki sun biyo ta, da wani irin tashin hankali Giɗaɗo ya taro ta yana kiran sunanta amma tana zuwa saitin shi ta kauce ta yi gaba. Zari uku ya yi ya damƙo ta ta dinga ƙoƙarin kwacewa amma ya riƙe ta gam. Da kyar ya iya riƙe ta suka shiga har cikin palon Hajja sai kuka take tana salati.
Zama duk suka yi Giɗaɗo ya kalli jikin Andizo ya ga duk ta yi baƙi ta koma ƴar ficiciya kamar ba ita ba, cike da tausayin ta ya ɗago ya kalli su Hajiya ya ce “Wai tun yaushe ta fara wannan rashin lafiyar ba mu sani ba?”
Cire tagumi Hajiya ta yi tana share hawayen da suka zubo mata ta ce “Gaskiya ta kusa wata ɗaya tun bayan sa bikinsu da sati ɗaya ta soma wani irin zazzaɓi mai zafin gaske, to muna kaita asibiti. Nan dai ta kwashe komai ta faɗa.”
Sake kallon ta Giɗaɗo ya yi ya girgiza kai ya ce “Wannan fa ba ciwon asibiti ba ne Hajiya.” Ya ƙarashe maganar a sanyaye.
“Ai tun da muka gane haka muka dinga nema mata na Hausa, duk inda muka ji magani sai mun amso an yi mata amma Wallahi ga ta nan kamar ƙara mata ciwon ake duk safiya. Ni kunyar haɗa ido nake da ku kun ba mu amana amma ga abin da ya faru yarinya kar ku ga kamar mun yi sakaci ne da ruƙon ta.” Hajiya ta faɗa tana share hawaye.
Maigari ya ce “Haba Hajiya sai ka ce mu ba musulmai ba ne za mu ce kun kasa riƙe amanar uwata? Ai duk abin da ya faru da bawa muƙaddari ne daga Allah, nasan kun riƙe da kyau fiye ma da yadda mu za mu riƙe ta Allah dai ya bar zumunci.”
Tashi tsaye Giɗaɗo ya yi ya sunkuya ya ɗauke ta ya saɓa ta a kafaɗa ya ce “Za mu tafi da ita gida a nema mata magani a can ko Allah zai sa a dace, ku shiga ku ɗauko mata tufafinta ko da kala uku ne.”

“Haba ɗan nan daga zuwan ku sai ka ce ku tafi da ranar nan? Ku zauna a shirya mata kayanta ku ɗan huta sai ku tafi an jima kaɗan.” Cewar Mamma tana kama Andizo ya sauke ta suka kwantar da ita ba dan ya so ba..

Ahmad duk ya kasa nutsuwa ko magana ya kasa yi jin sun ce za su ɗauke mishi ita su tafi ƙauye. Da kyar suka bari aka yi La'asar aka haɗa wa Andizo kayanta suka raka su direban gidan tare da Ahmad suka yi mota biyu suka nufi ƙauye..
Suna tafiya a hanya wayar Andizo da ke hannun Giɗaɗo ta yi ringing ya kalli wayar, ganin an rubuta Amira sai ya ɗaga kiran, sautin kuka ya masa sallama a kunne ya yi shuru yana jiran jin me za a faɗa, sai da ta dan ɗauki sakanni sannan aka fara magana. “Hello Khadija yanzu kin kyauta kenan ? Wallahi abin da kika faɗa wa Uncle kin ganshi nan yanzu ma an sake shiga emergency room da shi da ya farfaɗo sunanki ne kawai a bakinsa, yanzu haka ba na tunanin yana raye saboda yadda ya dinga aman jini ba lalle ba ya rayu, ni yanzu ban san me ya kamata na yi ba Khadija.” Ta faɗa tana ƙara fashewa da kuka mai tsuma rai..

Ajiyar zuciya ya sauke ya kalli Andizo ya ce “Ki yi haƙuri na ga an sa Amira ko? To itama kanta Khadijar ga ta nan rai a hannun Allah mun je mun ɗauko ta za mu koma ƙauye..” Ya kashe kiran yana tunanin me ya faru tsakanin Uncle ɗin Amira da Khadija har take ce mata abin da ta yi ta kyauta?...

*Maman Nusaiba ce*
[7/4, 3:15 PM] Ummu Amjad: ADZ

44

Sake kira Amira ta yi Giɗaɗo yaƙi ɗauka yana kallo har ta yi ringing ta katse, ba a fi minti ɗaya ba ta sake kira ya girgiza yana ɗaukan wayar tare da faɗin “Hello baiwar Allah ba ki ji ba abin da na faɗa miki?”
Kukan da take ne ya ci ƙarfinta ta kasa magana shi kuwa Giɗaɗo sai ya yi shuru yana sauraron ta, tabbas duk wanda ya ji kukan Amira ya san tana cikin tashin hankali musamman yadda take kiran sunan Khadija, sai da ta tsagaita sannan ta ce “Bawan Allah don Allah kai waye? Kuma ina Khadijata take da Yaya Ahmad? Na kasa yarda da abin da ka faɗa mini.”
Shuru ya yi bai ba ta amsa a take ba sai da ya ɗauki second goma sannan ya kalli Andizo da take daf da shi ya kai hannu ya gyara mata zaman hular kanta ya ce “Ni yayan Khadija ne yau muka zo daga ƙauye muka tafi da ita ba ta lafiya ga ta nan ba ta gane wa ke kanta, idan kuma ba ki yarda ba ki kira ta caméra sai na nuna miki ita ki ga zahiri.”
Baki na rawa ta ce “To amma ai Khadija tana da yayu har biyar amma tafi ambaton Hamma Giɗaɗo kai wanne ne daga cikin su?” Ta faɗa tana sharce majina.
Numfashi ya ja saboda duk ya ji ta takura mishi da tambaya, gefe ya kalla ya ce “Hamma Giɗaɗo be.”
“To nuna mini ita Wallahi hankalina a tashe yake da naji abin da ka ce, nan Uncle ga shi can ya mutu ba ko yana da rai Allah masani kaima ka ce mini ƙawata na kwance ba lafiya.”
Gyara wayar ya yi ya nuna mata Andizo a kwance fuskar nan ta yi baƙi ƙananan ƙurajen da suka fito mata sun mutu dai fuskar ta yi wata kala kamar an shafa mata gawayi, zaro ido Amira ta yi ta nufi wajen Mom tana kuka wiwi ta ce “Mom kalli itama Khadijar halin da take ciki.”
Mom ya gani nan take ya gane ta amma bai ce komai ba yana kallon yadda itama take kuka tana salati, da ya gaji ya yi gyaran murya ya ce “To zan kashe sai an jima.”
To suka ce suna ta jero mata addu'ar samun lafiya yana amsawa da amin har ya kashe..
Tagumi ya yi yana hasko fuskar Mom a zuciyarsa sosai ya ga matar tana cikin matsananciyar damuwa, janye tagumin ya yi ganin sun iso ƙofar gidansu.
Sauka duk suka yi ya rage saura shi da ita, shima ya sauka ya ɗauko ta yana ƙara lulluɓe mata jiki ta hijabin da aka sa mata ya yi saurin shigewa gida, yaran da suka fara tsayawa sai duk suka bi Giɗaɗo da kallo ganin ya ɗauko mace a lulluɓe ya shige ciki sai suka bi bayan shi.
A rumfa ya kwantar da ita shima ya zauna ya ɗago yana kallon yaran da suka yi tsaye suna son ganin fuskar wadda aka rufe, wani yaro daga cikin su ya ce “Giɗaɗo wannan ɗin waye ya mutu?”
Haɗe rai ya yi ya nuna musu hanyar fita da hannu ya ce “Maza kowa ya fita ba mutuwa aka yi ba ba ta da lafiya ne uwar masu gari ce.”
Gabaɗaya yaran sai suka kalli Giɗaɗo da mamaki ba wanda ya ce ƙala har suka fita daga gidan, kowanne yaro gidansu yake nufa a guje ya je ya kai labarin an kawo Andizo tana nan kamar ta mutu ma, tuni gari ya ɗauka Andizo ba lafiya matan aure duk suka nufi gidan Maigari ana zuwa ganin ta amma ba wanda aka yarda ya ganta suka sa ta ɗaki.
Ahmad ya sa aka kira mishi Giɗaɗo ya zo, kallon shi Giɗaɗo ya yi ya ce “Yaro ya ce kana kirana?”
Gyara tsayuwa ya yi yana fuskantar shi ya ce “E ina so ka ba ni wayar Khadija zan tafi da ita.”
Girgiza kai Giɗaɗo ya yi ya kalli wayar da ke hannunsa sai ma ya saka ta a aljihu ya ce “A a ba zai yiyu ba na ba ka wayar Surbajo, nasan ƙawata da sauran abokanta na makaranta za su kira ta idan wayar ba ta kusa da ita ai ba za su san halin da take ciki ba, ɗazu muna mota ma wata Amira ta kira ba ta san ba ta lafiya ba sai da n sanar mata, da farko taƙi yarda sai da ta kira caméra ta gani da idanuwanta sannan ta yarda, nan dai ya kwashe labarin komai ya faɗa masa.”
Zaro ido Ahmad ya yi yana faɗin “Inna lillahi wa inna laihin raji'un! Shima Sultan ɗin ba shi da lafiya har da aman jini? Subhanallah! To shi kenan bari mu koma za dawo jibi in sha Allah.” Ya faɗa yana shiga mota shima direban ya shiga ɗayar suka bar wajen, shi ne Giɗaɗo da ido ya bi shi ganin yadda shi ɗin ma ya firgice da ya faɗa masa wancan ba lafiya, tunani ya yi ko sun san juna ya juya ya koma ciki..

_NIGERIA_
Chapter 57 · 0% Book details