← Book details Andizo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 75

Sashe 27

Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da ta tabbatar ya samu nutsuwar da yake buƙata sannan suka yi wanka a tare ta shirya shima ya shirya sannan suka fito palo. Zama ya yi yana kallon ta tana ƙoƙarin kunna tv, yau duk sai ya ji ta canja masa da irin tararrayar da ta nuna mishi ta ba shi kulawa kamar wata babbar mace, tagumi ya yi yana murmushi duk inda ta motsa bin ta yake da kallo yana ƙara gode wa Allah da matar tasa ta yi soma nutsuwa. Ɗagowa ta yi ta harare shi ta ce “Malam ya da kallo na haka ko na canja maka ne?”
Girgiza kai ya yi bai ce mata komai, har za ta yi magana sai ga Farrah ta fito sanye da hijabi hannunta da waya tana faɗin “Mom Wallahi muka yi girki ni da Khadija bari ma ki ganta da mijinta sun sha kyau ga su nan a zaune a Palo.” Ta miƙa wa Andizo wayar, amsa ta yi tana gyara zama ta ce “Mom yau dai gani ga Farrah, ya gida ya Nigeria?”

Dariya Mom ta yi tana zaune a katafaran palon ta ana mata tausa ta ce “Ma sha Allah, ai dama cewa ta yi ba dai sister na za ta je Niamey ba kawai gidanki za ta je har su gama hutu, ina Maigidan naki yake?”

Matsowa ta yi kusa da Salim ta ce “Ga shi nan Mom.”

Hannu Salim ya ɗaga wa Mom ya ce “Ina wuni? Ya gida ya yara?”

“Lafiya lau mai hankali shirin Allah.” Cewar Mom tana dariya. Shima dariyar ya yi ya kalli Andizo ta ce “Kin dai ganshi dama ba ki taɓa ganin shi ba Farrah ce ta ganshi lokacin da aka kawo ni nan..”

“Ai kuwa dai na ganshi, to ayi ta haƙuri dai Salim ita yarinya ce dole sai ka kawar da kai a kan wasu abubuwan da za ta dinga maka, ga kuma ƙarin abokiyar rashin ji nan kun samu ta ce sai ta muku sati za ta dawo.”
Murmushi Salim ya yi yana faɗin “Haba Mom ai yanzu Khadija ta nutsu sanin da kika mata a da yanzu ba haka take ba, ai naji daɗin zuwan Farrah saboda kullum a ƙaramin kashi ta mini hirar ta sau bakwai, kuma naji daɗi da ta kawo mana ziyara Allah ya ƙara ƙarfin zuminci a tsakaninmu..”
Amin Mom ta ce suka yi sallama ta kashe kiran, Farrah ta samu waje ta zauna ta ce “Amma dai za kuke kaini wajen shan iska ko? Domin ina son na ga gari..”

“Ba ki da matsala gobe in sha Allah zan sa Ahmad ya kaiku koda ni ban samu damar kaiku ba.”

Wayar Andizo ce ta ɗauki ringing ta tashi ta ɗauko, ganin me kiran sai ta yi saurin ɗauka ta kara a kunne, shuru ta yi tana sauraron abin da ake faɗa mata, can ta ce “E Adda ga shi ɗazu ya dawo daga aiki, to bari na sa.” Ta faɗa tana buɗe speaker wayar, daga can ɓangaren Aminatou ta ce “Mijina yau zan maka albishir da abin da ba ka taɓa zato ba.”
Saurin matsowa ya yi kusa da Andizo ya ce “A haba dai? To ina jinki kin dawo ne?”

“A a ban dawo ba gani dai a hanya, na kasa daurewa ne na zo, gidan shi ya sa na ce bari na kira ku na muku albishir mai daɗi.” Ta faɗa tana zubar da hawaye sannan tana murmushi.
Andizo da ta ƙagara ta ji wannan labari ta ce “Adda ki sanar da mu Wallahi na zaƙu naji.”

Dariya mai sauti Aminatou ta yi ta ce “Ƙanwata ina muku albishir da ina ɗauke da cikin wata biyu a jikina.”
Wani irin tsalle Andizo ta yi ta sa kuwa tana dira a kan kujera, ta juyo ta kalli Farrah tana dariya ta rungume Salim tana faɗin “Alhamdu Lillah addu'ar da muke ta karbu, wow za yi mini takwara kai waiyo daɗi don Allah da gaske kike Adda?”

Cikin muryar kuka ta ce “Da gaske ne Khadija nima zan ga gudan jinina a duniya gani nan na ƙaraso gida, na so ma na wuce gidanmu dan na fara yiwa Ummi wannan albishir ɗin amma na tuna ban nemi izinin shi ba.”

“Kai gaskiya naji daɗi sosai Adda kuka ya ƙare, Allah ya inganta ya sa ki haifo mana yan huɗu maza biyu mata biyu..”
Dariya Aminatou ta yi tana yin packing ta ce “To Khadija Allah ya kawo su lafiya..”

Amin ta ce tana dariya ta kalli Salim da ya zama kamar gunki, sai da ta kashe wayar ta taɓa shi ya firgita yana kallon ta ya ce “Don Allah da gaske ne abin da Aminatou take faɗa?”
Far ta yi da idanu ta ce “Sosai ma kawai ku tashi muje mu taro ta ta ƙaraso.”
Zamowa ya yi daga kan kujera ya yi sujjadar godiya ga Allah yana yi wa Ubangiji kirari tare da gode masa da wannan gagarumar kyauta da ba su ka a lokacin da suke tsananin buƙatar ta, yana dagowa ya tashi suka bi bayan shi.

Ta fito daga motar tana shirin rufewa ta ji an rungume ta ta baya ta yi dariya ta juyo, Andizo ta kai hannu ta taɓa cikin Aminatou ta ce “Adda sannu.”
Murmushi ta yi tana kallon Salim da ya harɗe hannaye yana kallon ta cikin wani kalar yanayi na farin ciki har ma ya rasa me za ce mata, hannu ta miƙa mishi ya ƙaraso ya haɗa su ya rungume suna ta murna.
Part ɗin ta suka nufa Andizo ta shiga kitchen ta ɗauko mata lemo mai sanyi na kwalba ta miƙa mata ta ce “To ki sha wannan ko kin ji sanyi.”

Amsa ta yi tana mata godiya ta buɗe ta sha, kallon su take ganin yadda suke farin ciki da samun cikin sai ta ji sun ƙara shiga ransa, sosai ta ƙara yarda da Andizo tana kuma gode wa Allah da ya ta gane gaskiya tun guri kafin guri ya ƙure mata, da ta ci gaba da tafiya a kan keken beran da Sabrin ta dora da yanzu ba sa jituwa da abokiyar zaman ta..

Ranar har dare suna part ɗin ta Andizo ta ce ta faɗi mai take so za ta girka mata, ta ce ɗanwake take so Andizo ta ce “A abu mai sauki Adda ai yanzu zan yo miki shi tun a Ƙauye Hajja ta koya mini shi, sannan Mamma ta koya mini wani sabo daban..” Ta faɗa tana shigewa kitchen.

Sai kusan karfe goma na dare suka bar ɓangaren ta ita da Farrah ta ce ta yafe sauran kwanan ta ɗaya ya haɗa wa Aminatou ya yi kwana uku a ɗakinta albarkacin cikin aka samu za a mata takwara.
Da kallo Aminatou ta bi Andizo tana jinjina lamarin yarinyar, in ta yi wani abin har mamaki take ba ta, ta tabbata ba lalle ba ne in da Andizo ce ta samu ciki ta haƙura da kwananta ta bar mata, idanuwanta ne suka ciko da hawaye ta yi saurin mayar da su tana murmushi.
Salim ya kalle ta ganin yadda ta bi Andizo da kallo, kamo hannunta ya yi ya ce “Kin gani ko Aminatou, dama na faɗa miki Khadija ba ta da wata matsala ko kaɗan, saboda son da take wa cikin jikinki har ta bar miki kwana duk dan na kula ..

“Gaskiya na yarda Khadija ta daban ce a cikin mata ina mamakin yadda take wasu abubuwan kamar ba ta jin kishin ka, duba fa kwanaki a ɗakinta kake da za ka yi tafiya ta ce sai dai ni na bi ka ba za ta bar Islamiyar ta ba ta je ta yi sati a wani wajen, Allah ya ƙara haɗa kanmu ya kare mu da duk wani wanda yake son ganin ya raba kawunanmu..” Ta faɗa tana kwanto kanta kafaɗarsa.
Amin ya ce mata sai ga kiran Ummi ya shigo wayarta ta ɗaga, sai da suak yi way gabaɗaya da 'yan gidansu kowa yana taya ta murna amma ban da Abida da ta ce ita fushi take da ita babu ruwan ta da wani sabon cikin da ta yi. Ba Ta ji daɗin abin da ta faɗa mata ba amma ta share ta ce to kar Allah ya sa ta mata barka mana ko haihuwa ta yi in ta ga dama ta zo in ba ta gani ba kar ta zo...

Suna shiga ɗaki Farrah ta shige ɗakinta har za ta rufe sai kuma ta juyo ta ce “To amma ai za ki zo mu kwana tare ko?”

“Sosai ma yanzu zan canja kaya na zo gani nan.” Ta faɗa tana shigewa ɗaki ta rufo har da datse ƙofa.
Kan gado ta faɗa ta cuta kanta a jikin pilo ta fashe da kuka mai tsuma zuciya, sam ba ta son yin bacci ba tare da shi ba amma dole ta bar wa Aminatou kwananta, saboda yadda ta ga Aminatoun na buƙatar Salim a kusa da ita. Tashi ta yi zaune ta yi tagumi ji take kamar ta ce ta fasa ba da kwanan amma wani sashe na zuciyarta na tausar ta, hannu ta sa ta goge hawaye ta ce “Allah ka da kishin shi ya sa na kasa kyautata wa abokiyar zama na, ya Allah ka rage mini kishin da nake ji a kan Adda Aminatou.”
Zuciyarta ce ta dinga mata saƙie-saƙe ta miƙe tana a'uziya ta shiga banɗaki ta ɗauro alwala, Sallar shafa'i da wutiri ta gabatar sannan ta zauna tana karanto addu'ar yayewar ƙuncin zuciya, hannu ta ɗaga sama tana karantawa kamar haka:
” لاَ إلَهَ إِلاَّ اللَّهُ الْعَظِيمُ الْحَلِيمْ، لآ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ رَبُّ العَرْشِ العَظِيمِ، لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهْ رَبُّ السَّمَوَّاتِ ورّبُّ الأَرْضِ ورَبُّ العَرْشِ الْكَرِيمُ.“

Sai da ta ji ta samu nutsuwa da kyau sannan ta tashi ta canja kaya ta nufi ɗakin Farrah. A zaune ta same ta tana rubutu, ganin waya a aje sai ta gane waya take, zama ta yi a ɗaya gefen ta ce “Ke kuma da wa kike waya da daren nan?”
Chapter 27 · 0% Book details