Sashe 43
Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kamar wadda kwai ya fashewa a ciki haka take tafiya, nan da nan ta ji zazzaɓi mai ƙarfi yana neman yi mata rufdugu, a bakin kofar ta tsaya jin jiri na neman ɗaukar ta. Sai da ta jima sannan ta sa kai cikin palon bakin ɗauke da sallama.
Amsa mata suka yi Ahmad ya tashi da sauri ya amshi kayan yana faɗin “Sannu da ƙoƙari.”
Murmushi yaƙe ta mishi ta durƙusa ta zuba musu ruwa da lemo gabaɗaya jikin sai wani kyarma yake sakamakon ƙamshin turaren da ta shaƙa, da kyar ta gama zuba musu ta ɗago kai a hankali ta dube gefen baƙon ta ce “Sannu da zuwa, ya hanya?”
Saurin janye wayar ya yi suka haɗa ido, zaro ido ya yi sai kuma ya kalli Ahmad ya ce “Abokina anya kuwa ban haukace ba?”
Da mamaki Ahmad ya ce “Ban gane ka haukace ba?”
“Ahmad tsananin son da nake mata ya sa har fuskarta da muryarta naje gani da ji a jikin wata macen, Kahdijata fa nake gani tana mini gizo..”
Itama tun da ta ƙura mishi ido jikinta ya ba ta kamar ta san shi, sai da ta daɗe tana kallon shi sannan ta gane shi ne, ajiyar zuciya ta sauke ta ce “Ni ce Khadijar da kake nema ba gizo ba ne nake maka.”
Miƙewa ya yi ya iso gaban ta ya rasa me zai ce mata kawai ya miƙar da ita tsaye, kasa tsayuwa ta yi saboda ba ta da ƙarfi ga jiri na son kayar da ita. Wani irin duhu ta ga ya mamaye mata ganinta ta yi baya luu....
_Maman Nusaiba ce🤙🏻_
[6/23, 1:16 AM] Ummu Amjad: _*AREWABOOKS@SARATALKASUM88*_
38
Ta kusa kaiwa ƙasa ya yi saurin taro ta ta faɗo jikinsa sai ga su sun zube a kan kujera, ƙoƙarin tashi take yi amma ya hana ta. Tsananin mamaki ne ya hana Ahmad tashi ya ƙame a kan kujera kamar sojan da ke filin fareti, a wannan lokacin zuciyarsa ce kawai take bugawa amma ban da gangar jikinsa. Sai da yi second fiye da arba'in sannan ya ja dogon numfashi yana kallon su, sam ya kasa gane inda abokin nasa ya dosa dama macen da yake yawan ba shi labari a kanta ashe Khadijar da yake son aura ce? To taya ma suka haɗu har suka san juna bayan shi ba mazauni ba ne? Sannan ita Khadija ba ta taɓa fita wata ƙasar ba ballantana a ce can suka haɗu har suka ƙulla soyayya? Girgiza kai ya yi ya runtse idanu ganin yadda yake share mata hawayen da ke fareti kan fuskarta.
“Sweetheart dama a nan gidan kike? Aka ce an miki aure ko dama Mom ta faɗi haka ne dan ta saka ni à damuwa? Kin san kalar tashin hankalin da na shiga lokacin da Farrah ta sanar da ni ta je gidanki hutu tana ba ni labarin yadda mijinki yake kula da ke? Har fa kwanciya na yi a gadon asibiti a can London wannan karon sai da aka buga bal sau biyu ban da ni. Yanzu tun da na ganki nasan ƙarya ce Farrah take ba a miki aure ba.” Ya ƙarashe maganar yana ɗago hannunta ya ɗora a kan fuskarsa, ji yake kamar ya mayar da ita ciki saboda tsananin kewar ta da ya yi, so yake ya rungume ta ya ji ɗumin jikinta amma ganin yadda take yatsine fuska ya sa ya haƙura. Hannu ya sa ya ɗago fuskarta ya ce “Ki yi magana mana.”
Buɗe idanunta ta yi a kan fuskarsa tana ƙare mishi kallo, a hankali ta ce “Hali zanen dutse, shi ya sa Hausawa ke cewa idan ka jima ba ka ga mutum karka tambaye shi labari tambaye shi halinsa, ke ko yaushe za ka canja hali Daddyn Farrah? Sannan meye haɗin ka da Amira da na ganka a gidansu? Duk da naji tana ce maka Uncle.”
Murmushi ya yi ya kalli Ahmad da ya yi shuru yana kallon ikon Allah, shi maganar ma ta gagare shi sai ido kawai, tun da yake da Sultan bai taba jin ya furta wa wata 'ya mace kalmar so ba sai a kan Khadija, jinjina kai ya yi ya yi gyaran murya ya ce “Wai Mr J ban fahimci inda kuka dosa ba dama ka san Khadija ne?”
Kallon ta ya yi ya dawo da kallon shi kan Ahmad ya ce “Ni kuwa nasan Khadija fiye da kai kanka, domin duk wani motsin ta a tafin hannuna yake, ko makaranta ta je ana bin mini diddigin ta.”
Baki Ahmad ya saki yana juya magana can ya tuno ranar da wata mota ta biyo su, da sauri ya kalli Sultan ya ce “Dama yaranka ne can baya suka taɓa biyo mu naje ɗaukan Khadija zan kai ta wajen Yaya Salim?”
Gyaɗa kai ya yi yana murmushi tare da cewa “Tabbas haka ne, amma ban taɓa tunanin Khadija tana tare da kai ba, na fasa bibiyar rayuwarta ne sakamakon Mom da ta mini katanga da ita, kai har fushi Mom ta yi ta daina amsa gaisuwa ta dole na haƙura na koma London na fasa bin duk wani motsin ta, amma a zuciyata ina cutuwa domin ban yarda Khadija aure aka mata ba tunanina ya fi ba ni danginta ne suka ɗauke ta ta dawo birni da zama.”
Kishi ne ya rufe Ahmad amma ya danne yana rarrashin zuciyarsa kar ta tunzura shi ya ci mutumcin abokinsa da ya tashi tun daga wata ƙasa ya kawo mishi ziyara, sauke kai ƙasa ya yi ya ce “Abokina to ai Khadija ita ce matar Yayana Salim da ya rasu, kuma har suna da yara biyu a tsakanin su. Abu na gaba kuma yayana ya bar wasiyyar na aure su dan na kula mishi da yaransa, sai dai kuma dukkan su kowacce ta ce ba za ta taɓa yarda ta aure ni ba musamman ita wannan fitinanniyar mai bakin rashin kunya.”
Ya ƙarashe maganar yana nuna ta tare da kirkiro murmushin yaƙe dan ya kawar da abin da yake ji a zuciyarsa..
A hankali ta tashi tsaye tana riƙe kai ta ce “Ba ka ba ni amsa ba kuna da dangantaka da Amira ne?”
Cikin jin daɗi ya gyaɗa mata kai ya ce “Sosai ma, da mamar Amira da Mom uwa ɗaya uba ɗaya suke, ko lokacin da Farrah ta zo nan hutu ai gidanta ta fara zuwa ta ce ba za ta zauna ba wajen ki za ta zo, dalilin zuwana Niamey dan na sake binciko ki na san a wani hali kike ciki, idan na ganki na ɗauke ki mu bar ƙasar..”
Duk da tana jin ciwo amma sai da ta harare shi ta haɗe fuska ta ce “Tab wace ce za ta bar ƙasar ba dai ni Khadija ba?” Tana gama faɗin haka ta yi ta maza ta sa kai za ta wuce ta ji muryarsa yana faɗin “Shin da gaske ne wai kin haihu naji shima Ahmad ya faɗi?”
Kai kawai ta gyaɗa mishi ta yi gaba gabaɗaya ya cagula mata lissafi. Sai da ya ga ta rufo ƙofar sannan ya juyo kan Ahmad yana murmushi tare da matsowa kusa da shi yana riƙe hannunsa ya ce “Gaskiya naji daɗin ganin Khadija ta girma sosai, ashe zuwa na gidanku alkhairi ne.”
Ahmad dai sai yaƙe yake yana bin shi da eh ko a'a, sai da ya ci abinci sosai yana yaba daɗin girkin hakan ya ƙara ƙular da Ahmad. Bayan ya gama suka fito ya masa jagora ya shigo ciki suka gaisa da su Mamma, Hussaina ta kalli Sultan tana murmushi ta ce “Yaya wannan ne Mr J ɗin da muke ji kana ambata?”
Kallon ta Sultan ya yi ya ce “Ƙanwata ya kike?”
Da sauri ta amsa da “Lafiya lau ya ƙasar turai?”
Alhamdu Lillah ya ce mata sannan ya a je wa Mamma da Hajiya Babba leda guda-guda, da yake ba shi da ta ido kai tsaye juya ya yi wa Hussaina alama da hannu ta biyo shi, can harabar gidan suka fita ya tsaya yana sakar mata fuska ya ce “Yawwa please je ki kira mini Khadija ki ce Farrah ta ba da saƙo a ba ta.”
Kallon shi ta yi tana mai ci gaba da murmushi ta ce “Dama ka san Farrah ne?”
“she is my daughter.” Ya ba ta amsa.
Waro ido tana yi ashe dama yana da ɗiya kamar Farrah? Da sauri ta juya ta shige ciki dan kiran Andizo.
A bakin ƙofar ɗakinta ya tsaya bayan ya buɗe, ko kallon shi ba ta yi ba saboda ta kanta take sai da ta ga abin nashi ya wuce gona da iri ta ce “Don Allah ka rufe mini ƙofa ina son zan kwanta na gaji.”
Rufe ƙofar ya yi ya ƙaraso in da take zaune ya tsugunna fuska haɗe ya ce “Ki faɗa mini a ina kuka kula soyayya da abokina? Sannan dama ƴarsa da yake ba ni labari ita ce ta zo miki hutu a baya?”
Tsaki ta ja tana mishi kallon banza ta ce “To kai meye naka a ciki ɗan sa'ido? Da Duk zaman ka da shi ba ka taɓa ganin ƴar tasa ba dan ƙarya?”
Dafe kai ya yi ya rasa me ya sa take faɗa mishi magana son ranta ba, idanuwansa ne suka yi jajur ya ɗago ya kalle ta ya ce “Na rantse da Allah idan kika sake yin magana da shi sai na, saɓa miki.”
“To sannu Hamma Giɗaɗo ko Maigari ko kuma mamata, kai har ka isa ka hana na yi magana da baban ƙawata? Meye haɗin ka da ni?”