Sashe 61
Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hajja ba ta zarce ko'ina da Andizo ba sai ɗakin Maigari wanda suke tare da Ahmad. Tun da ta sako ƙafa yake kallon ta cike da tsananin tausayin ta, tuna ya sadaukar da soyayyar da yake mata sai ya ji zuciyarsa ta ƙara karaya nan da nan idanuwansa suka cika taf da ruwa ya yi saurin sunkuyar da kai yana dafe saitin zuciyarsa, ita kanta sai ta ga Ahmad ɗin ya rame sosai sai ta danganta hakan da rashin lafiyar da ta kwanta, zaunar da ita Hajja ta yi itama ta samu waje ta zauna Maigari yana mata sannu ta sunkuyar da kai ƙasa ta ce “Yaya sannu da zuwa, dama tare kuka zo da su Amira?”
Murmushi ya sakar mata ya amsa, “Yawwa Khadija ya jikin naki? Tare muka zo da su.”
Maigari ya gyara zama ya kalli Andizo ya ce “Uwata waye Sultan?”
Saurin ɗago kai ta yi ta kalli Maigari sai kuma ta juya akalar kallon mata ga Ahmad idanuwanta suna mishi kallon ya aka yi Maigari ya san Sultan, alama ya mata da ta amsa mishi kawai ya kawar da kai gefe yana jin wani kalar zafi da raɗaɗi na sukan heart ɗin sa. Sai da Maigari ya sake tambayar sannan ta ita ba shi amsa a sanyaye, “Maigari shi ne mahaifin Farrah ƙawata kuma ɗa ga Mom.”
Da mamaki Maigari ya ce “To ikon Allah! Wai dama ɗan hajiya ne?” Gyaɗa mishi kai ta yi shi kuma ya ci gaba da magana, “Ahmad ne ya zo da maganar ya janye maganar auren ki ya haƙura.”
Saurin kallon Ahmad ta yi cike da mamakin abin da ya sa Ahmad ya janye maganar auren nasu, ta san yana matuƙar son ta ita ce dai ba ta jin son shi kamar yadda shi yake nuna mata, ajiyar zuciya ta sauke ta yi ƙasa da kai saboda da wani sanyin daɗi da ya mamaye zuciyarta, amma duk da haka ta ji babu daɗi saboda yanzu ta fara son shi tun lokacin da ta danni zuciyarta ta ba ta haƙuri musamman yanzu sai ta ga ya ƙara mata kyau da kwarjini a idanu duk da ya ɗan rame. Maigari ya ƙare musu kallo sannan ya kwashe duk maganar da Ahmad ya sanar da shi ya faɗa mata, sannan ya ƙara da cewa “Na tabbata Ahmad ba zai bari wani wanda ba mutumin kirki ba ya aure ki, kuma mahaifiyarsa tana da kirki za ta riƙe ki kamar ɗiyar da ta haifa. Yanzu ke ya kika gani kina son shi ɗan nata kin amince na sa a ƙara mini bincike da kansa duk da bayanin da Ahmad ya ba ni game da shi? Za ki aure shi uwata? Yanzu haka yana can kwance a gadon asibiti rai a hannun Allah, Ahmadu ya ce mini shi kaɗai ne ɗanta namiji sai mace ɗaya.”
Hankalin Andizo ya tashi matuƙa duk saboda da ita ne ya kwanta a gadon asibiti, amma da ta tuna ɗabi'u da halayensa sai ta haɗe rai tana kumbura baki ta kalli Ahmad suka haɗa ido, tausayi ya ba ta ta gammace gara farin cikin wannan ahali da nata farin ciki, za ta sadaukar da soyayyarta saboda da su domin sun yi mata halaccin da ba kowanni ɗan'adam ba ne zai iya yi.
Maigari ya gyara babbar rigarsa ya ce “Uwata ba ki komai ba shin kina son shi ko kuwa ba ki son shi? Ki ba mu amsa ɗaya mu ba za mu yi miki dole sai kin aure shi ba.”
Shuru ya ratsa ɗakin na wajen sakan talatin duk sun zuba mata ido suna jiran jin abin da za ta faɗa, ita kuma maganar ta ke kan harshenta take son faɗa amma zuciyarta na gargaɗin ta a kan kalmar da take son fitarwa, runtse ido ta yi da ɗan ƙarfin da ya rage mata ta cije lip ɗin ta na ƙasa sannan ta ce “Ku ɗin kun kasance bango abin jingina a gareni Maigari, matuƙar akwai abin da zan yi na saka ku cikin farin ciki to komin wahalar shi in dai bai saɓa wa shari'a ba to zan yi muku shi, Salim shi ne fitilar da ya haske rayuwata ta zamo ingantacciya, duk wani abu na rayuwa in dai ya shafi ilimi zai kaini na koya ko kuma shi ya kowa mini har na iya.” Ta ɗago ta kalle su ta ga duk sun zuba mata ido baki sake, sharce majina ta yi tana zubar da hawaye zuciyarta na ƙara limka ciwon da take ji har numfashi in ta ja sai ta ji kamar za ta kurma ihu, amma ta daure ta cije tana huci ta ɗora da cewa, “Yanzu kuna ganin wannan mutumin ya cancanci na ƙi duk wani wanda ya haɗa alaƙar jini da shi? Shi ne fa wanda ya kashe maƙudan kuɗi ya saka ni à makaranta da rayuwata gaba ta zama mai kyau, yanzu kuma babu shi sai na nuna ba zan auri ɗan'uwansa ba? A da ciwon mutuwarsa ya sa na tsani maganar aure, sannan yadda muka zama abokan faɗa ni da Yaya Ahmad ya sa naji ba na so shi, amma yanzu ni yaya Ahmad nake son ƙarashe rayuwata da shi ba Sultan ba, dukkan ku ba ku san waye Sultan ba shi ya sa kuke ƙoƙarin ba ni shi a matsayin abokin rayuwa, ba ya Sallah, ba shi da tausayi, duk wani abu da ya shafi addini Sultan bai sani ba a haka kuke so na zauna da shi? Shin kun san wani irin lefi ya aikata mini? Wannan ni kaɗai na bar wa kaina sani sai kuma shi da ya yi abin, amma tun da na ga kuna jin tausayin shi yau zan faɗa muku abin ya haɗa ni da shi.” Ta sake ɗagowa tana kallon su a karo na biyu.. Baki buɗe Ahmad ke kallon Andizo zuciyarsa na mugun bugawa da ƙarfi har sai da ya sa hannu ya dafe, tabbas ya san in me Khadija ta faɗa shi ne sila tun da ya faɗa mata aibun Sultan har sai da ya ga tsoro a idanuwanta sannan ya rabu da ita, yanzu kuma ga shi an zo lokacin da yake son su haɗu su ceto rayuwar abokin nasa amma ya ga wankin hula na neman kaishi dare.
Maigari ya sauke ajiyar zuciya ya ce “To ke wani mugun abu ya miki haka da kike aibata shi? Ko kin manta shi ɗa ne ga hajiyar nan da ta ceto rayuwarki daga hannun mutanen da suka sace ki?”
Goge fuskarta ta yi ta ce “To ai shi ne mug..” “Surbajo ya isa haka! Tashi ki tafi tun da dai Ahmad kika zaɓa ba mai miki dole.” Suka jiyo muryar Giɗaɗo daga bakin ƙofa duk suka bi shi da kallo har ya iso cikin ɗakin ya zauna. Kallon ta ya yi ya nuna mata hanya da hannu ya ce “Je ki kwanta ki huta kin ji, so samu ma ki yi bacci ko kin ƙara jin ƙarfin jikinki.”
Duk da tana jin jikinta wani iri amma hakan bai hana ta hararar shi ba tukun ta yunƙura za ta tashi Maigari ya dakatar da ita ya ce “Idan kin je ki kira mini Innarki.”
Kai kawai ta gyaɗa ta ɗago suka haɗa ido da shi, murmushin yaƙe wanda ya fi kuka ciwo ya yi ya ce “Na gode Khadija idan kin je ki kira Mama.”
A hankali ta tashi Hajja ta ce “Ko na raka ki?”
Girgiza kai ta yi ta fita ɗakin tana goge hawayen da suka zubo mata, kicibus suka yi da Umar ta kalle shi ganin yadda idanuwansa suka yi jajur, a hankali ta ce “Hamma za ka shiga ciki ne?”
E kawai ya ce mata ya yi gaba ya shige ciki itama ta wuce. Tana isa ɗaki ta sanar da Mama Maigari na son ganin ta ta tashi da hanzari ta fita, bayan ta fita ne suka dasa hira da Amira in da take sanar da ita irin yadda Sultan yake ambaton sunanta yana son ganin ta, ita dai murmushi kawai take tana faɗin “Allah sarki Daddyn Farrah Allah ya ba shi lafiya.” Amira sai ta amsa da amin har Mama ta dawo ta same su, Mama ta ƙara yi mata Allah ya ba da lafiya sannan ta ce da Amira ta tashi su tafi Ahmad yana bakin mota. Gabaɗaya suka fito har Andizo suka iso bakin motar ta yi wa su Mama godiya sannan ta matso kusa da Ahmad ta turo baki gaba ta ce “Shi ne ko ka ce mini ya jiki?”
Ƴar dariya ya yi ya ce “Haba ji ne dai ba ki yi ba, amma na faɗa a ɗakin Maigari yanzu kuma sai ranar biki za ki dawo birni?”
Kai ta gyaɗa mishi ya ɗaga hannu ya juya ya shige mota, tana tsaye sai da suka bar wajen sannan ta juya ta koma ciki. Zama ta yi a cikin ɗaki tana karanta wasiƙar jaki har bacci ya ɗauke ta.
Sai da Andizo ta yi sati ɗaya tana shan rubutun da Malam yake aiko mata kafin ta samu kuzarin ta ya soma dawowa, sosai Inna ke kula da ita tana jiƙa mata wani tsumi ta haɗa mata da zuma ta ba ta ta shanye, idan za ta kwanta ta tafasa bagaruwa da lalle da ganyan magarya ta shiga ciki ta zauna har sai ya huce sannan ya fito, gyara na musamman irin na gargajiya Inna ke yi wa Andizo, kaji da zabo kuwa kullum sai an dafa mata su ta ci nan da nan ta maida jikinta hasken fatarta ya fara dawowa. Tana cika kwana goma aka daina ba ta komai sai kanumfari da ake jiƙa mata shi Inna ta ce ta mayar da shi ruwan shan ta zai taimaka mata sosai, da farko sam ƙin shan ta yi sai da Inna ta zaunar da ita ta faɗa mata kanumfari shi kaɗai gayya ne yana maganin infection, basir, ɗaurewar marar yayin al'ada, wanke ciki, da sauransu. Bayan ta ji wannan bayani game da kanumfari sai ta dinga sha kamar ba gobe..