Sashe 8
Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sun ɗauki lokaci a haka ya ɗago ta yana murmushi ya manna mata kiss a ƙoshi ya kuma mayar da ita jikinsa ya rungume ta kamar za a kwace masa ita, ita ko jin ƙamshin jikinsa da ɗumi suka sa ta yi luf tana ƙara yi wa kanta masauki, buɗe idanu ta yi a hankali tana jin wani iri a zuciyarta sai kawai ta fashe da kuka mai ƙarfi..
Hankali tashe ya ɗago da ita ya zaunar da ita yana faɗin “Khadija me ya faru ? Wani abu suka miki da suka sace ki?”
Kasa magana ta yi sai kallon shi da take tana ci gaba da kuka, gabaɗaya ta ji wani irin yanayi na ratsa kowacce kusurwa ta jikinta wanda ta rasa mene ne shi, share mata hawayen yake yana rarrashin ta cikin wani kalar yanayi da yake jin shima ya tayata kukan. Sai da ta yi shuru ya sake tamayar ta, cikin muryar kuka ta ce “To ba kai ba ne ban ganka ba ina ta son na ganka.”
Lumshe idanu ya yi ya tallafo fuskarta suka tsura wa juna ido, a hankali ta kai hannu ta shafi gefen fuskarsa ta ce “Shin da aka sace ni ka yi kuka ko?” Ta faɗa a shagwaɓe.
Murmushi ya yi yana jin yadda take yawo da hannayenta a fuskarsa, murya a shaƙe ya ce “In da kuka ne ma ai mai sauƙi ne Khadija, har kwanciya na yi a gadon asibiti ban san wa ke kaina ba saboda ɓatan ki matata..”
Zaro idanu ta yi sai kuma ta kalle shi ta ce “Waiyo Allah.” Ta faɗa tana koma tana bubbuga mishi baya a hankali ta ci gaba da cewa “Ka yi hakuri mai hankali yanzu ba ga shi Mom ta dawo da ni ba?”
Sai a lokacin Andizo ta kalli kayan abincin ta kalle shi, “Mai hankali ba ka ci abinci ba ko?”
Girgiza mata kai ya yi ta ɓata fuska ta janyo abincin ta buɗe ta tura masa ta ce “Bismillah.”
Cikin nishaɗi ya ce “Sai dai in za mu ci tare.”
Maƙale kafaɗa ta yi ta cuno bakinta da ya sha janbaki, janye abincin ya yi ya ce “To na ƙoshi tun da ba za ki ci ba.”
Da hanzari ta sa hannu tana dariya ta ce “To mu ci.”
Da kanshi ya dinga ba ta a baki tana ci itama tana ba shi, idan suka kalli juna sai su saki murmushi da haka har suka gama. Da kanshi ya wanke mata hannu itama ta wanke masa tana dariyar wai ƙato da shi ta wanke masa hannu ya ce ya ji..
Bayan sun gama ta ba shi labarin yadda aka sace ta da rayuwar da ta yi da yadda Mom ta kawo ta gida, amma ba ta sanar da shi abubuwan da Sultan ya mata ba kawai ta ce ba wanda take gani da aka kai ta sai mai kawo mata abincin, sosai Salim ya yi mamaki yana jinjina lamarin ɓarawon da yake son raba shi da numfashinsa a daidai lokacin da yake son gina wata sabuwar rayuwar..
Sai bayan La'asar suka shirya komawa gida in da suka sanar da Maigari saƙon su Abie Maigari ya ce ba matsala, amma dai kawai za a ɗaura auren bayan Sallah ta tare. Ba haka Salim ya so ba amma ya yi ƙudirin yi wa Abie maganar da an ɗaura a ba shi matarsa kawai ba sai an yi wani biki ba, da wannan tunanin suka kama hanya zuciyarta cike da bigen abar ƙaunar sa..
Washegari Andizo da Hajaru suna yawo a gari suka zo saitin wani gida, Hajaru ta kalli gidan ta ce “Ƙawata wannan fa gidan Iliya ne, tafiyarki da kwana uku aka masa aure da wata ƴar fulani mai kawo fura da nono nan, wai shi ne matar ta kama rashin aka ce aljannu gareta, kuma fa na ƙarya ne dan zai ƙara aure ne, kullum sai an mata ruƙiya amma abin sai gaba yake.”
Dariya Andizo ta yi ta ce “Kenan dai na ƙarya ne? Ki bari da dare za mu zo mu mata ruƙiya.”
Dariya suka yi suna tafawa, Hajaru ta ce “Shegiya sai wahalar da mijin take ya fasa auren amma ba ta daina cutar shi ba, kuma fa ko an zo ruƙiyar sai a ce sai ya ba da kuɗi mai yawa da ya bayar sai su raba da mai ruƙiyar in mijin ya fita.”
Riƙe baki Andizo ta yi ta ce “Kut! Ka ji muguwa amma ke wa yake faɗa miki wannan labarin?”
“Hmm ai ni babu abin da ban sani ba a gidan nan ko kin manta mijin ɗan'uwanmu ne?”
Gyaɗa kai Hajaru ta yi suka yi gaba..
Da dare Andizo ta ɗauki wata babbar rigar Maigari fara sol guda biyu, a cikin kayan kwalliyar da Mom ta zubo mata har da farar fauda ta ɗauka ta zuba a leda ta ɓoye ta fita da sunan za su je dandali.
A hanya suka haɗu da Hajaru nan suka nufi gidan. Sunan isa suka same shi a tsaye suka ce masa su masu ruƙiya ne za su fitar da aljannun da ke jikin matar yau din nan, jin haka sai ya musu iso har ɗakin da aka kulle ta, Andizo ta ce ya fita ƙofar gida duk abin da ya ji kar ya shigo, jiki na rawa ya ce to dan shi zaton shi aljannu ne yan'uwan aljannun jikin matarsa suka zo za su taimake shi. Sai da suka rufe ko'ina sannan Andizo ta maƙale murya ta ce “Keee!”
Next Fage.
Littafin ANDIZO na kuɗi ne N300 ne, za ku turo kuɗinku ta wannan account ɗin.
Account number 0003187186
Name account, khadija Salisu
Name Bank, Ja'iz Bank.
Sai a turo shedar biya ta wannan number
🥏+966577675904
*Maman Nusaiba ce🤙🏻*
[5/26, 11:29 PM] Ummu Amjad: _*AREWABOOKS@SARATALKASUM88*_
20
Ƙin tashi ta yi sai ma gyara kwanciya da ta yi a zaton ta irin masu ruƙiyar da aka saba kawo mata ne, kallon juna Andizo da Hajaru suka yi ganin ba ta motsa ba, a fusace Andizo ta fito da bulalar da ta ɗauko tun daga gida, sai da ta taƙarƙare ta zabga mata. A firgice matar Iliya ta tashi tana fasa ihu idanuwanta ya sauka a kan su ta ja da baya, biyo ta Andizo ta yi tana zaro idanu ita kuma Hajaru tana haska fuskar Andizo da wayar Maigari rakani kashi, baki na rawa ta ce “Na shiga uku ni Laure ku kuke ganin mu ba mu muke ganin ku ba, don Allah ku yi haƙuri mutanen ɓoye karku kashe ni.”
Tsawa Andizo ta daka mata tana nuna ta da bulalar ta ce “Ai yau kin yi bankwana da duniya sai kwanan lahira, tun da kika zama azzalumar mace dole mu azabtar da ke kafin ki isa gaban Allah ki masa bayanin cutar da mijinki da kike yi ba dare ba rana, in kuma kina son zaman duniya to da sharaɗi.” Ta faɗa tana wani irin juya idanu.
Baki na rawa ta ce “Na. Na yarda ko ma meye kuke so in dai za ku rabu da ni.”
Dariyar basawa Hajaru ta yi ta matso kusa da ita ta ce “Buɗe kanki mu miki ƙwal a kwabo dan ubanki, kinga in aka ga haka sai a san aljanun gaskiya ne a kanki sun miki aski, tun da kika shiga gonarmu mu aljannu daga yau kin dinga ganin masifa da bala'i matuƙar ba ki faɗi gaskiya ba.” Ta faɗa tana wanka mata mare, saboda mugun haushin ta take na wahalar mata da ɗan'uwa da take yi duk ya bi ya rame sai tagumi duk in da ka ganshi..
“Waiyo Allah na shiga uku na lalace! Ku taimake ni karku aske mini gashina, duk abin da kuke so zan yi yanzu ma zan kira Iliya na sanar da shi duk abin da nake ƙarya ce ni na tsara..”
Kallon juna suka yi suka sa dariya da wata irin murya, riƙe kunne Andizo ta yi kamar mai sauraron wani abu can ta ce “E ina jinki yanzu, to ba damuwa kenan mu tafi da ita bangon duniya na arewa? To shi kenan da mun gama za mu zo da ita.” Ta faɗa tana sheƙewa da dariya, tana buɗe haƙoranta baƙi wuliƙ kamar da gaske haka suke, hakan ke ƙara sa matar Iliya ta tsorata da sun buɗe baki..
Durƙusawa ta yi a kan gwiwowinta tana kuka wiwi ta ce “Don Allah ku mini rai karku tafi da ni duniyar aljannu...”
“Yo wa ya ce miki mu aljannu ne? Mu fatalwowi ne daga ƙabari muka fito.” Cewar Hajaru..
Kwalalo idanu waje ta yi tana kyarma gabaɗaya jikinta ya yi sharkaf da zuba, da na sanin abin da ta dinga wa mijinta ta mamaye ta, a ruɗe ta Kuma cewa “Don Allah ku yi mini rai karku tafi da ni Wallahi ina son mijina, dama sharrin sheɗan ne ya sa nake masa haka, ku taimake ni kun ga yau ɗin nan na gano ina ƙaramin ciki ko dan darajar shi ku barni zan gyara halina.” Ta faɗa tana dafe mararta..
Shuru suka yi Andizo ta sa hannu ta rufe hasken wayar da suke haskawa, kamo hannun Hajaru ta yi suka fito waje ta matso kusa da kunnenta ta ce “Hajaru kina ganin mu rabu da ita kar mu zane ta?”
“Ƙila ma fa ƙarya take yi, amma dai in kin ce mu rabu da ita shi kenan mu ba ta kwana biyu mu gani idan ba ta canza ba ta haka za mu gane ƙarya ta mana..”