Sashe 10
Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai da ta gama ya janyo hannunta da karfi sai ga ta yaraf a ƙasa ta yi zaman 'yan bori a gaban shi, kallon shi ta yi ganin yadda idanuwansa suka yi jajur kamar an watsa masa barkono, da kyar ya haɗiyi yawu ya ce “Surbajo ni kike faɗa wa magana a kan wani Saminu? To Allah ya ba ki haƙuri ba zan sake ba ai kin kusa daina gani na ki huta..”
Kwafa ta yi ta miƙe tsaye ba ta ce masa komai ba ta wuce fuu tana faɗa har ta bar ɓangarensu..
Abie da Abba suka zo suka yi zama na musamman a kan buƙatar Salim, amma fir Hajja ta kafe ta ce gaskiya sai bayan azumi da kyar Umar ya shayo kanta ta amince su dawo sati mai zuwa a ɗaura auren su tafi da amarya. Cike da farin ciki Abba ya fito da sadaki 50,000F jika ƙamshin ya aje sannan suka koma zuciyyoyinsu cike da farin ciki..
Ko da suka koma gida suka sanar da Salim ranar kwana ya yi yana Sallah yana miƙa godiyar sa ga Ubangiji, duk abin da yake Aminatou na kallon shi tana mishi dariyar mugunta, za ta ga ta yadda amaryar za ta shigo.
Ahmad kuwa cewa ya yi ranar da za a kawo amarya dole ne a harabar gidan ya haɗa gagarumar dinner ya gaiyato abokansa da na Salim a sha shagali, hakan ya ƙara kona zuciyar Aminatou dan ya gida ya zo ya sanar da Salim suna zaune a palo, in kuma ta tuna shirin da suka yi na musamman a kan Andizo sai ta ji wani sashe na zuciyarta ya yi fes, ƙarshe ma har baki ta sa a maganar amma Ahmad ya ƙi kula ta..
Ɗankwalinta a hannu ta isa wajen Maigari ta ce “Maigari ka ba ni wayarka zan kira Mom mu gaisa da Farrah ƙawata.”
Babu muso ya miƙa mata ta koma ciki da sauri, waje ta samu in da babu kowa ta ɗauko number ta saka ta danna kira. Sai da ta yi ringing ba a ɗauka ba ta kuma kira, wannan karon ta kusa katsewa aka ɗauka.
Murmushi ta yi ta ce “Mom ina wuni? Ya gida ina ƙawata Farrah? Ki ba ta za mu gaisa..”
Daga can ɓangaren Mom na zaune a palo masu aiki na mata tausa ta yi dariya, kallon gefe ta yi ta ga Farrah ba ta kusa ta ce“Lafiya lau Khadija ya su Maigari? Farrah ba ta kusa tana ɗakinta bari na ba da a kai mata karki kashe.”
“To Mom ai dama zan sanar mata aurena fa nan da kwana biyar ne, to ya kamata ta zo bikin tun da ta mini alƙawarin za ta zo a gaban ki aka yi haka ko?”
“Kwarai ma kuwa ni ce shaida, ashe bikin ya zo ma? To bari a kai mata.”
To Andizo ta ce Mom ta ba wa ɗaya daga cikin masu mata tausa ta kai wa Farrah.
A kwance ta same su ita da Sultan suna ta hira ta yi sallama ya juyo, kallon ta ya yi ta sunkuyar da kai ta ce “Ranka ya daɗe Mom ce ta ce kawo mata waya wata ce ta kira tana neman ta.”
Da sauri Farrah ta tashi ta duro daga kan gadon ta isa ta mashi wayar, a hankali ta ce “Hello wace ce?”
Dariya Andizo ta yi ta ce “Khadija ce Farrah, dama na kira ne in faɗa miki yaushe za ki zo wajen bikin nawa? Kin ga yanzu saura kwana biyar dan har yau Hajja ta mini wankan lalle kin ji yadda nake ƙamshi kuwa.”
Zaro idanu Farrah ta yi cike da murna ta ce “Wow nice one, Kenan Khadija auren naki har ya zo nan da kwana biyar? Ai kuwa za mu je ni da Mom k..”
Ba ta ƙarasa ba ta ji an warce wayar ta yi saurin kallon shi, kara wayar ya yi a kunne yana huci ya ce “My wife me kika ce za ki yi nan da kwana biyar.”
Jin muryarsa sai da gaban ta ya faɗi amma ta dake ta ce “Aurena mana ni da mai hankali za mu koma birni ni da Saminu.”
Cikin ƙaraji ya ce “Khadijaa! Na rantse da Allah in kika bari aka miki aure da wani ba ni ba sai na kashe shi, waye shi da zai shigo gonata? Wallashi suma tallahi zan kashe shi har lahira in dai ya kuskure ya aure ki, waye ubansa a Niger ɗin?” Ya faɗa yana yin jifa da wayar Allah ya sa ta faɗa kan gado...
*To fa jama'a Angon Andizo zai yi kisa🚶🏼♀️*
*Mun kusa gama promote littafi zai dawo kuɗinsa na farko N500 daga nan zuwa ranar Alhamis.*
_Maman Nusaiba ce🤙🏻_
[5/27, 10:20 PM] Ummu Amjad: _*AREWABOOKS@SARATALKASUM88*_
21
Kallon shi Farrah ta yi a tsorace ganin yadda jijiyoyin kansa suka tashi sun yi raɗa-raɗa, bakin gadon ta iso ta sa hannu ta ɗauki wayar ta ga har yanzu Andizo na kan kiran, a hankali ta kara a kunne ta ce “Khadija wai me ya sa kuke faɗa da Daddy ne?”
Tsaki Andizo ta yi tana murza idanu saboda firgita ta da y yi da karajin maganar da yake, sai da ta yi jim ta ce “Shi fa Daddy ce mini ya yi wai zai kashe duk wanda na aura, dama shi ɗan fashi ne ban sani ba? To alƙur'an ya shiga hankalinsa in yana tunanin zai iya rashin mutumci a Nigeria a kyale shi, to mu a nan Niger ya kashe mutum tsaf za a rataye banza ya mutu a wulaƙanci a kai shi a totse cikin ƙasa. To ma ni ina ruwana da shi? Ba kina ji ba Mom ta ce kar ya sake kulani?” Ta faɗa hawaye na zubo mata..
Zama Farrah ta yi ta yi shuru ita dai ba gane me Andizo ke nufi ba, dan haka ta kawar da maganar da cewa “Nan da kwana uku za mu je biki naki har da Abida mai kula da ni.”
Gyara zama ta yi ta ce “To shi kenan amma ki faɗa masa kar ya sake amsar waya ya mini magana in muna hira da ke.”
Dariya Farrah ta yi ta kalli Sultan da yake tsaye yana jin duk abin da suke faɗa dan speaker a buɗe take, hannu ya sa ya amshi wayar ya nufi ƙofar fita yana faɗin hirar ta isa haka zan kai na sa miki wayar a caji kin ji.” Ya faɗa yana wucewa.
Ba dan ta so ba haka ta haƙura ta rabu da shi ta koma ta kwanta sai murna take za ta je bikin ƙawarta..
Daret ɗakinsa ya nufa, a hanya duk wanda ya haɗu da shi a cikin ma'aikatan gidan ya masa barka da rana ko samun arzikin ɗaga hannun da yake musu ba sa yi, hakan ya sa suak gane cewa lalle yau fa akwai matsala a tattare da Ogan nasu. Yana shiga ɗaki ya sa key ya ƙulle ya nufi wani lungu sai ga shi a kafataran Palo ya sha ado, gaba ya yi ya tsaya jikin wata kofa mai glas ya danna wasu numbobi da ke jikin Ƙofar ta yi ƙara sannan aka ce “Welcome to the room Mr Sultan.”
Wani shan mur ya yi Kamar ya ga abin ƙi ya shige ciki, wani makeken gado ne a ɗakin royal an shifiɗe shi da kyakkyawan bedsheet fari tas sai adon dawisu da ke tsakiyar bedsheet ɗin. Zama ya yi yana huci ya kalli wayar ya ga ta kashe kiran, hanzari ya danna mata kira ta yi ringing ta gama ba a ɗaga ba ransa ya ƙara ɓaci, dafe kai ya yi ya sake danna kira ya ci sa'a an ɗauka. Dogon numfashi ya ja ya yi baya ya kwanta ya yi ɗaiɗai, ita kuwa can bayan dakunansu inda suke wasan tuwon kasa ta nufa a tunanin ta Farrah ce ta sake kira, ta samu waje ta zauna a ɗankaraminki na kayan wasa. Jin ba a ce komai ba ta ce “Ke Farrah wai ba za ki yi magana ba?”
Murmushi ya yi yana haske yadda take maganar tana turo baki, buɗe ido ya yi murya a, shaƙe ya ce “My Dija.”
Saurin ɗauke wayar ta yi daga kunnenta ta kalli wayar ta ga dai numéro ɗin da ta saka ne, mayar da wayar ta yi ta ce “Kai kuma me ya sa ka ɗauki wayar Mom? Dalla can Malam ka ba wa mai wayar abin ta ba na son kalan dangi, so kake na ce Farrah ta zo da kai bikina ko? To ba zan faɗi ba ka kuma ce mini my wife ɗin nan sai na faɗa wa Maigari duk abin da ka mini wanda na ɓoye..”
Girgiza kai ya yi ya ce “To ai babu wanda zai aure ki in ba ni ba Sultan, dan haka ki ma daina maganar za a miki aure da wani ba ni ba, ni ne nan mijinki in kuma wani ya yi ƙoƙarin shiga gonata zan iya komai dan na fitar da shi daga ciki. Yanzu Khadija har za ki iya auren wani bayan ni? Ba ka yadda nake sonki ba za ki zaɓi wani a kaina?” Ya faɗa yana dafe saitin zuciyarsa tare da runtse idanu da karfi, gabaɗaya ɗan kuzarin da yake ji ya neme shi ya rasa sakamakon maganar ta..
“Kai can ta matse maka Malam ko ba ni da saurayi ne zan yi da wanda ko yadda zai bautawa Ubangijinsa bai sani ba, ka koma makaranta ƙila ko ka iya gane ciwon haukan da ya same ka.” Ta faɗa tana jan tsaki ta kashe kiran..
Kallon wayar ya yi cike da mamakin kalamanta, “To me take nufi da hakan? An faɗa mata ban je school ba ne?” Ya faɗa yana aje wayar..
Shuru ya yi yana kallon samar ɗaki, dole ne ya yi wani in ba haka ba akwai matsala, a hanzari ya miƙe ya nufi jikin wani table mai ɗauke computers har guda 3, ɗaya daga ciki ya buɗe ya sa code sannan ya ɗauko wani number ya sa kira. Eapis ya sa a kunne yana jiran a ɗauka, ana ɗauka ya soma magana cikin zafin zuciya..
“Ashu where is Bansh?”