Sashe 47
Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Arma ne ya tare su yana ɓata rai ya ce “Ku kuma shi kenan sai ku shanya ni ina ta jiran ku, wai lafiya ? Tun karfe 7:30am Khadija ta ce mini ga ta nan za ta fito daga gida, amma yanzu kalli ki ga lokacin 8:30am ina kuka tsaya?”
Taɓe baki Amira ta yi ta ce “Ga wadda nan ta tsayar da mu tun ɗazu muka zo amma taƙi fitowa daga mota sai da aka rarrashe ta ta fito.”
Tsaki Andizo ta yi ta yi gaba ta samu waje ta zauna suma suka biyo ta, sai da suka zauna Andizo ta ce “Ina Sadiya?”
“Tana ciki ita ai ta riga mu zuwa.” Arma ya ba ta amsa yana kallon ta ganin yadda take wani ciccin magani..
Sai da malamin ya fito sannan suka samu damar shiga cikin classé ɗin, Andizo ta fara copy rubutu tana gamawa wani ya shigo sai suka ake. Bayan sun fito suka wuce restaurant suka sayi shawarma amma Andizo ta kasa ci, da ta shinshina bakinta sai ta ji ƙamshin jikinsa sai ta tofar da yawu tana jin kamar ta yi amai, ƙyanƙyamin shi da take ya sa ta kasa cin abincin ta ce ta goshi. Bayan sun tashi motar gidan su Amira ta zo ta ɗauke su aka kai ta har gida, tana shiga ɗakinta ta wuce banɗaki da gudu sai amai, iya ruwan da ta sha a wunin ranar shi ta amayo, tana gamawa ta yi brosh ya fi sau biyar sai da ta soma jin za ta faɗi saboda yunwa sannan ta haƙura ta watsa ta fito . Bayan ta fito kaya ta canja sannan ta fito ta wuce Denning table ta dibi shinkafa fara da miya ta dawo palo wajen Hajiya Babba ta zauna. Kin Kula ta Hajiya Babba ta yi har ta gama cin abincin ta kai kwanon ta a je ta sha ruwa sannan ta dawo, dariya ta yi zauna tare da kwanciya a cinyar Hajiya Babba ta ce “Haba Hajiya wai duk fushin ne kike ba ki huce ba?”
“A a uwaki ce nake.”
Dariya ta kuma yi sai kuma, ta tashi ta zauna ta ce “Yawwa wai ni ko Hajiya mene ne ya faru a gidan nan shekarun baya da suka wuce? Lokacin da Salim yana kwance a asibiti naji ya ce kar ta tuna da abin da ya far shekarun ba da suka wuce, shin wani mummunan abu ne ya faru?” Ta faɗa tana kallon Hajiya.
Jinjina kai Hajiya ta yi sai ga hawaye sun soma zarya hakan ya sa Andizo ta ce “Haba Hajiya ya da kuka?”
“Khadija gyara zama zan sanar da ke abin da ya faru shekarun baya har kika ji Salim na cewa kar mahaifiyarsa ta tuna.
A wata ranar asabar...”
Ƙaran banko ƙofar da aka yi ya sa Hajiya da Andizo suka ɗago da sauri, ganin shi duka yi kamar wani kumurcin maciji ya iso gaban Andizo rai ɓace ya ce “Uban waye wanda ya ɗauke ki a mota ?” Ya faɗa kamar zai kai mata duka duk da ya san wanda ya ɗauke ta.
Tsoro ne ya kama ta ta ja da baya tana ƙara mannewa da jikin kujera, hakan ya sa ya biyo ta tare da damƙar hannunta ya miƙar da ita tsaye, sunkuyawa ya yi ya mata ɗaukan akuya ta fasa ihu tana faɗin “Hajiya don Allah karki bari ya tafi da ni Wallahi dukana zai yi mugu ne mugunta zai mini, ki cece ni Hajiya waiyo Mamma zai ƙarya ni...”
*Maman Nusaiba ce*
[6/26, 11:10 PM] Ummu Amjad: _*AREWABOOKS@SARATALKASUM88*_
40
A tare Mamma da su Hassana suka fito a firgice jin ihun Andizo, ganin abin da yake faruwa sai sai suka zari ido suna kallon Ahmad da yake ƙoƙarin barin palon, ita kuwa sai ihun neman taimako take tana dukan shi a gadon baya amma ya yi kamar bai ji ba. Haɗe rai Mamma ta yi ta ce “Kai Ahmad ba na son hauka meye haka? Sauke ta na ce kafin na iso na zabga maka mari.”
Sauke ta ya yi yana huci kamar kumurcin maciji ya riƙe ƙugu ya ce “Mamma to kin san me ta yi ne kika hana na mata hukunci?”
To ko ma meye ta yi tun da ba kisan kai ta yi ba ko abin kunya ai bai kamata ka mata irin wannan ɗaukan ba.” Cewar Hajiya tana zaune da mamakin Ahmad ya hana ta tashi daga kan kujera. Tsaki ya ja ya dawo ya zauna a kusa da Andizo ta yi saurin matsawa tana kallon shi a tsorace, harara ya aika mata ya ce “Na rantse in kika sake matsawa sai na ɗauke ki ni na san abin da zan miki, ba dai dan na sa miki ido ba ne har kike yin duk abin da kika ga dama? To daga yau kin gama duk wani ɗan iskan da na sake gani ya tsaya da ke da kaina za zane ki, amanar ki Maigari ya ba mu ba zan zuba ido na ga kina kula tantiran 'yan iska ba na yi shuru amana ta ci mu. Saboda ba ki ɗauke ni mutum ba shi ya sa kika kama hanya kika fita har wani ƙato ya zo ya ɗauke ki, me ya faɗa miki da kika shiga motar?”
Duk maganar da yake mata murya can ƙasa yake yi ba mai ji daga ita sai shi, a hankali ta ɗago ta kalle shi baki na rawa ta kuma sunkuyar da kai sannan ta ce “Don Allah Yaya Ahmad ni ka rabu da ni na yi rayuwata cikin salama, kai ka takura mini shima Daddyn Farrah ya addabe ni so kuke ku haukata ni ne? Wallahi na ma fasa zama zan koma ƙauye na yi gaba da rayuwata kawai.” Ta faɗa wasu hawaye masu ɗumi suka silalo daga kwarmin idanuwanta. Kwafa ya yi cikin ba da umarni ya ce “Tashi ki tafi ɗaki zan je na same ki magana za mu yi, kuma idan kika kuskura wani ya ji maganar nan sai na yanka wuyanki da wuƙa.”
Saurin kallon shi ta yi tana zare ido, da hannu ya nuna mata hanya ta tashi sumaƙai kamar munafuka ta wuce. Da kallo suka bi ta Hajiya ta ce “Ni dai ina ga rayuwa a gidan nan, ban taɓa ganin jarababbe irin ka ba Ahmadu duk ka bi ka takura wa rayuwar yarinyar nan, ta ce za ta je ganin gida amma ka bi duk wata hanya ka hana ta tafiya ta haƙura, yanzu kuma ɗan karatun da take shima ba za ka bari ta yi cikin kwanciyar hankali ba? Ni fa ba ƙanwata ba ce ta yaye ni ballantana bari ka sa wa marainiyar Allah ciwon zuciya, a haka kake so ta so ka har a muku auren?”
Ci gaba ya yi da daddanna wayarsa yana jin ta ya yi shuru, hakan ya sa Hajiya ta ɗauki pillow ta buga mishi tana faɗin “Ɗan banza futsararre tashi ka ba mu guri.”
Sai lokacin ya ɗago kai ya kalle su, Mamma dai na zaune ta kawar da kai ko bi ta kanshi ba ta yi ba ta ci gaba da kallon tv, amma kuma hankalinta yana kan maganar da Hajiya ta yi. Dariya ya yi ya tashi tsaye ya ce “Hajiya wannan ɗiyar taki idan ba a sa mata ido ana tsawatar mata sai ta haɗu da abokan banza su ɓata mata rayuwa, kuma kinga dai amana ce a garemu bakiɗaya, idan wani abu ya same ta da mu Maigari zai yi kuka. Kuma aure ni da ita ai ba fashi ba ki ga mun daidai kanmu ba ne? Shi ya sa na hana ta kula kowa tun da ta amince za ta aure ni.” Yana gama faɗin haka ya juya ya wuce da sauri. Murmushi Hajiya ta yi ta ce “Aha ashe dai kishin ne ya motsa dan ka gata da wani ko?”
Juyowa ya yi ya sakar mata murmushi ya juya ya wuce, daƙuwa Hajiya ta yi wa bayansa tana faɗin “Ja'iri kawai.”