← Book details Andizo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 75

Sashe 62

Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwanakin da aka ƙara na biki sakamakon rashin lafiyar amarya sun karato ya rage saura sati ɗaya, a ranar dangin aka kawo lefin Andizo tare da su Hassana da ƙawayen Mamma da 'yan'uwanta, ranar mata har gida suke zuwa suna ganin kayan lefen da aka kawo wa Andizo a karo na biyu, wasu cewa suke wannan lefen ya fi ma na auren farko yawa akwati goma sha biyu cif a jere kowacce cike da kaya na alfarma.
A kawo kaya da kwana ɗaya Amira ta kira Andizo a waya tun daga sallamar ta gane ƙawar tata a fusace take, can ta shige ƙuryar ɗaki ta zauna a bakin gado sannan ta ce “Ƙawata ya dai naji ki haka me ya faru?”

Daga can ɓangaren Amira ta hayayyaƙo mata kamar za ta fito daga wayar ta rufe ta da duka.
“Ai ko me ya faru ke ce sila Khadija, na ɗauka ke ɗin ƙawa ce ta amana ashe ba haka ba ne, yanzu Khadija kin zaɓi Ahmad a kan Uncle? To ba komai kin kyauta kuma na gode kin ji Khadija, amma ina so ki sani ba ke kaɗai ba ce 'ya mace a duniya akwai mata bil'adadin da suke bin kan Uncle ya aure su amma ya kafe ya ce ke yake so, sai ga shi kin ƙi shi kin zaɓi wani a kansa. Khadija ina so ki sani ni Amira in sha Allah zan auri Uncle kuma na zame mata komai a rayuwa, zan nuna mishi soyayya da tattali da kulawa saboda da shi ɗin jinjina né shi ba zan sake bari ya ambaci sunanki ba balle har ya ji ba daɗi a ransa, dan haka sai an jima dama abin na kira ki na sanar da ke an sa mana aure da shi sai an jima.”

Wayar ta bi da kallo tana nanata sa rana, shuru ta yo tana kallon gefe. Can Farrah ta faɗo mata a rai ta tuna yadda suke son juna da yadda yarinyar ke nuna sha'awar ta zama matar mahaifinta, amma ita kuma ta ji ba za ta iya zama da shi ba a matsayin miji saboda ba ya Sallah, haka dai ta karaci tunaninta ƙarshe ta kawar da komai tana maƙe a fili ta furta “To ni ina ruwana dan za ta aure shi? Ita ta ga za ta iya sai ta runguma.” Fita ta yi daga ɗakin ta nufi cikin yan matan da suka zo mata zaman wuni har da wadda za ta mata lalle da kitso a cikinsu. Zama ta yi aka fara yi mata suna mata waƙa ita kuma tana dariya..

Biki ya kankama ana ta hidima yau ta kasance saura kwana ɗaya ɗaurin aure, Ahmad ya kira ta a waya bayan sun gaisa ya ce “Khadija na tura miki saƙo ta whatsapp ban ga kin ɗaga ba, kayan fitar gobe nake so ki zaɓa mana a cikin waɗanda na tura miki.”
Lomar da ta sa a baki ta haɗiye sannan ta ce “To bari yanzu zan shiga na duba ban gani ba ne duk na shiga hidima ne.”
“Hidimar ai daga ta gobe ta gama, sannan dama ina so na faɗa miki daga nan daret Diffa za a wuce da ke, ni gobe idan aka gama ɗaura aure da su Abdoul za mu huce can mu zauna.” Ya faɗa yana buɗe dinkin shadda blue ya sha zubin zare.

“Allah sarki Yaya Abdoul na kwana biyu rabon da mu gaisa, zan nuna maka wadda na zaɓa yanzu sai an jima.” To ya ce sannan ya kashe, daret ta shiga whatsapp ba ta tsaya buɗe saƙon kowa ba ta zarce kan nashi duk da kuwa sakonnin da ta gani rututu, bayan ta ɗaga ta duba kayan can dai ta nuna mishi farar shaddar ita za su saka gobe ya amsa da cewa “To shi kenan Allah ya kaimu lokacin.”
Amin ta faɗa sannan ta aje wayar.

Masu iya magana na cewa rana ba ta ƙarya sai dai uwar ɗiya ta ji kunya, a yau ne aka cika a babban masallacin juma'a da ke ƙauyen aka zauna domin ɗaura auren mutum uku, bayan Andizo akwai wasu yan mata biyu da bikin masu ya rana ɗaya, hakan ya sa aka haɗa ɗaurin auren a waje ɗaya. Sai da aka ɗaura auren Andizo sannan aka ɗaura na sauran, duk in da ka nufa a garin baƙi ne wasu daga Niamey wasu maƙotan ƙaiyukan da suka gaiyato har ma da fulanin yankin duk Maigari ya gaiyato su, su sauran amaren da yake duk Maradi za a kaisu mutanen Maradi dayawa sun halarci ɗaurin auren, kasancewar ɗaya daga cikin yan matan ɗan mai kuɗi ne ta aura babansa ɗan kasuwa ne sananne, ga kuma na su Ahmad suma Daddy ya gaiyato mutane manya-manyan yan kasuwa. Tun daga farkon titin da zai sada ka da masallaci har kofar gidan Maigari motoci ne sun fi ashirin, su Ahmad sun kawo motar kusan goma yayin da ɗan mai kudi ya kawo motoci fiye da goma, ɗayar amaryar ce aka zo da mota uku..
Bayan an gama ɗaurin aure aka fara shirin kai amarya gidanta. Wankan turare Andizo ta fesa duk in ta ta ɗaga a jikinta ƙamshi yake, sosai aka tsantsara mata kwalliya ta gani ta faɗa, ita kanta ta san chocolate ɗin fatarta ta haska sai sulɓi take ga ƙamshi na tashi daga jiki. Ana yin Sallar La'asar Andizo ta ce sai ta wanke kwalliya ta yi Sallah, Ɗahare ta ce ba za ta wanke ba tun da ta yi alwala kawai ta yi Sallah, amma ta ce ita fa sam sai ta wanke kwalliyar nan dama ba ta ce a yi mata kwalliya ba a bari a yi La'asar su ne suka matsa mata ta yo alwala a yi in an gama ta yi Sallah. Ba yadda suka iya dole suka rabu da ita ta shiga banɗaki ta sa sabulu ta wanke tas ta ƙara watsa ruwa sannan ta yi alwala ta fito ta gabatar da Sallah, bayan ta gama Ɗahare ta dube ta ce “Sai ki zo a sake Angonki dai shi zai yi biya biyu ai.”
Baki ta murguɗa ta ce “Tab! Wace ce za a yi wa kwalliya? To ba dai ni ba fauda kawai za ta sa mini na sa kwalli ni ba na son kwalliyar nan, kafin ma mu je ai ta lalace.”
Kyale ta Ɗahare ta yi ta wuce mai kwalliya ta mata simple kwalliya Sosai ta yo kyau, haka dai aka shirya aka yi mata nasiha sosai tana kuka wiwi da kyar aka banbare ta daga jikin Maigari aka sa ta mota, sauran masu rakiya suka shiga aka kama hanya.
Maimakon ta ga an kama hanyar Diffa sai ta ga sun kama hanyar Niamey ta yi shuru tana kallon gefe, da an jima Ahmad sai ya kira ta yana tambayar a in suke ta sanar da shi. Suna isa daret airport suka nufa ta bi wajen da kallo karo na biyu kenan da ta taɓa zuwa airport, ba su fi minti arba'in da zuwa ba jirgin da zai kaisu Diffa ya sauka nan suka fito suka nufi inda zai sada su da jirgin. Bayan sun shiga sun zauna da yan mintoci jirgi ya cika suka tashi..

Zuwa cikin dare suka yi inda Abdoul da wasu matasa guda uku shi na huɗu suka zo da motoci manya suka kwashe su zuwa gidan amarya. A wani katafaren gida suka fara hon maigadi ya zo ya buɗe musu get suka kutsa kai ciki, babbar harabar gidan duk da dare ne amma an ƙawata ta da shukokin flowers masu kyau, gidan hawa huɗu ne. Bayan an fito da amarya suka wuce ciki, faɗin tsaruwa da girman palon ɓata baki ne, ya rakiyar amarya kowa sai kallon gida yake yana faɗin “Ma sha Allah gaskiya gidan nan ba dai tsaruwa ba.”
Wasu mata suka zo suka musu sannu da zuwa da gabatar musu da abinci da in da za su kwanta haƙarƙarinsu su huta, sosai suka yaba da kirkin matan suak wuce ciki, Ɗahare da Andizo da babar Hajaru su ku za su kwana a ɗaki ɗaya, sauran kuma suma suka shiga dakuna uku suka rabu, Sallah suka rama magariba da isha'i suka ci abinci sannan suka bi lafiyar gado. Andizo kasa bacci ta yi sai juyi take tana kallon gefe, a hankali ta janyo wauarta ta shiga whatsapp ta yi wa Ahmad saƙo. Ba a jima ba sai ga kira ta yo saurin danne ƙaran ta ɗaga ta ƙara a kunne tana sauke ajiyar zuciya. A hankali ya ce “Khadija duk gajiyar ce ta sa kika kasa bacci? Ki je ki yi wanka za ki ji daɗin jikinki, idan kuma wani abu kike buƙata ki sanar da ni.”
Ƙasa-kasa ta yi da murya sannan ta ce “Yaya shi ne ko ka zo na ganka ka ɓoye kamar kai ne amaryar?”
Ƴar dariya ya yi ya ce “Ba ɓuya na yi ba, nima ina son ganin ki to kinga akwai mutane a tare da ke shi ya sa ban ko leƙa b sai gobe da safe za mu je mu gaisa mu raka su su tafi gida.”
Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce “Shi kenan sai an jima.”
To ya ce mata sannan suka aje waya, ba ta ɗauki lokaci ba bacci ya yi gaba da ita..
Chapter 62 · 0% Book details