Sashe 63
Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Washegari da safe bayan sun tashi a kawo musu abinci sun karya su Ahmad suka shigo da abokansa suak gaishe su, bayan an gaisa suka tafi ce su shirya jirgin ƙarfe ƙarfe 6 na yamma za su bi suka ce ba matsala. Haka suka wuni a gidan Andizo ta ji daɗin ganin 'yan'uwa da abokan arziki sun cika gidanta sai ta ji kamar kar su tafi. Ƙarfe 5:30pm suka gama shiryawa manyan suka ƙara yi mata nasiha sannan suka fito, tana tsaye suka fara shiga mota sai ta ji zuciyarta ta karye ta sa musu kuka ita sai ta bi su, hararar ta Ɗahare ta yi tana faɗin “Uwar kilbibin tsiya jiya fa ina ji kike cewa ya ƙi zuwa shi ne dan kin raina mana hankali har kike kuka sai kin bi mu ? Matsa ki ba ni hanya na shiga kafin na bangaje ki angonki ya ga baƙina.”
Dariya suka sa har ita ta goge hawayen tana ɗaga musu hannu har suka fita sannan ta juya ta koma. Ji ta yi gidan ya mata girma amma tana jin maganar wasu daga sama kamar yara, murmushi ta yi da ta tabbatar yara ne sai ta tuna su Nour, zama ta yi a kan kujera ta ce “Allah sarki yarana, ai kuwa wannan maƙociyar tawa zan sa yaya Ahmad yake kawo mini yaranta suna ɗebe mini kewa.”
Bayan Sallah isha'i ta yi wanka ta ɗan yi kwalliya ta zauna, har tsoro y fara kama ta sai ta ji maganar su Ahmad suna doso ciki, gyara zama ta yi ta janyo mayafi ta rufe fuska tana jiran zuwansu. Sun Kai su goma suka shigo duk suka zauna a palo, Ahmad ya leƙa ɗakin yana murmushi ya ce “Khadija fito mana an zo yi mana nasiha.” Ya faɗa yana washe baki. Murmushi ta yi ta sauko a hankali ta biyo bayan shi ta samo waje ta zauna a ƙasa kusa da ƙafafuwansa, gaisawa suka yi da yan rakiyar ango suak dora da nasiha, bayan sun gama Ahmad ya ce ta koma ciki zai raka su yanzu zai dawo ta ce to ta shige ɗaki. Tana jin yadda yake rufe ƙofar palo ya kashe wuta ya ɗauki ledar da ya zo da ita ya nufo ɗakin, kwankwasawa ya yi sannan ya murɗa a hankali bakinsa ɗauke da sallama ya shigo, ta sauri juya baya ta yi kafin ya ƙarasa shigowa tana amsa sallama. Tana ji ya cire babbar rigarsa da hula ya aje a gefe sannan ya hayo gadon ya ƙaraso inda take ya sa hannu daga baya ya yaye nayafin, hannu ya sa ya juyo da ita fuskarsa ɗauke da murmushi ya ce “Amaryata ai kuma kunya ni da ke ta ƙare tun da muka zama miji da mata, ɗago ki kalli mijinki ke kaɗai Allah ya mallakawa.” Ya faɗa yana ɗago da fuskarta..
Runtse ido ta yi jikinta ya ɗauki rawa, murmushi ya yi a karo na barkatai ya ƙara matso da ita daf da shi, buɗe ido ta yi karaf suka haɗa ido sai kawai ta ɗora hannu biyu a ka ta fashe da kuka tana riƙe hannnunsa...”
*Ku ji ni kwana biyu shuru Wallahi ina cikin damuwa ne Yayuna da ke Libiya a zaune aka kwashe su yanzu haka babu wanda ake samu a, waya. Da kyar aka samu mutum ɗaya shi ne ma har na samu nutsuwar yin rubutu. Don Allah ku taya mu da addu'a Allah ya fito mana da su daga hannun mugayen nan🤲🏻*
_Maman Nusaiba ce_
[7/12, 2:55 AM] Ummu Amjad: ADZ
47
Baki ya saki yana kallon ta kamar yadda itama shi take kallo, matsowa ya yi ta yi saurin yin baya sai da ta haɗa da ƙarshen gado ta takure a waje ɗaya tana bin shi da kallon tsoro ƙarara a kan fuskarta. Girgiza kai ya yi ya cire hula ya gyara zama sannan ya ce “Nasan hakan za ta faru Khadija, ki matso ki zauna a kusa da ni zan sanar da ke abin da ya faru.” Ya faɗa yana janyo kafarta. Ihu ta sa tana faɗin “Nan ɗin ma ka biyo ni ne dan ka sace ni kamar yadda ka saba? Ina mijina yake? Me ka mishi har ka samu damar shigo mini har cikin uwar ɗaka? Ka sake mini ƙafa ko na yi maka ihu ɓarawo.”
Ƙin sakin ta ya yi har sai da ya dangana ta da jikinsa, ta taƙarƙare ta gatsa mishi ciwo a ƙirji dan ya sake ta amma sai ji ta yi ya ce “Na gode Khadija ki ci gaba da cizo na in dai za ki bari na rungume ki.”
Ganin dai taƙi tsayawa sai ya sake ta ta zabura ta sauka a gadon, da mugun gudu ta isa bakin ƙofar ɗakin ta buɗe ta fita duk yana zaune ko motsi bai yi ba yana kallon ta. Tunawa ta yi da wayarta tana son komawa amma tana tsoron shiga, gabaɗaya jikinta rawa yake sai safa da marwa take a palon, ta juya za ta koma ta ganshi a bayan ta ya miƙo mata wayar ya ce “Ki kira abokina.”
Wartar wayar ta yi tana hararar shi, kawar da kai gefe ya yi yana isa bakin kujera ya zauna. Kiran number Ahmad ta yi ringing ɗaya ya ɗauka tana jin ya ce hello ta fashe da kuka tana faɗin “Yaya Ahmad ina kake ka ganshi nan ya shigo mini gida, kawai daga cewa za ka raka abokanka kuma sai na ga ƙato ya shigo saɓanin kai.”
Sautin dariyarsa ta ji hakan ya sa ta tsayar da kuka tana hura hanci ta ce “Dariya ma na ba ka ? Ka yi maza ka zo ka ganshi kar ya sace ni.”
Ahmad da ya yi tsaye a tsakiyar ɗaki ya ce “Gani nan zuwa Khadija yanzu.”
To ta ce sannan ta kashe kiran ta isa bakin ƙofa tana jiran ta ji ya kwankwasa.