← Book details Andizo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 75

Sashe 12

Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kama hannunta ya yi da nufin su tafi amma fir ta ce ita fa ta gaji ya ɗauke ta, dariya ya yi ya ce “Abu mai sauƙi matar Salim ai ko goyaki sai na yi ba ɗauka ba.”
To ta ce ya ɗauke cak suka yi ciki..
Sai da ya zo tsakiyar palon ya aje ta yana faɗin “Hassana ga ta nan ki yi sauki ki shirya mini ita nima zan shiga wanka.”
To ta ce tana dariya ganin yadda yayan nata yake ranar jiki a kan Andizo, ya juya zai tafi Andizo ta kamo rigarsa tana saɓa baki ta ce “To ni dai karka mini wayo ka tafi ka barni.”
Duƙawa ya yi daidai tsayinta ya dafa kafaɗunta ya ce “Wanka kawai zan yi kema za a miki kwalliya ne mu tafi can gida wajen shagalin..”
Jin bin da ya faɗa sai ta sake shi Hassana na kallon su cike da birgewa, hannunta ta kama suka nufi wata ƙofa shima ya nufi wata daban..

Ruwan wanka Hassana ta haɗa mata ta nuna mata yadda za ta yi amfani da komai na banɗaki sannan ta fita. Da yake ba wannan ba ne karon farko na ganin bahon wanka sai ta shige ciki tana lumshe ido jin wani ƙamshi na tashi a ruwan wankan. Bayan ta gama ta ɗaura towel ta fito suka haɗu a bakin kofa ta kama hannunta suka nufi ɗaki, ƙananan abin buƙata ta ba ta ta saka haɗi da wata doguwar riga sannan ta fara tsara mata special kwalliya irin ta manyan mata. Bayan ta gama ta ba ta rigar amare daidai ita mai masifar kyau pink colour ta ce ta sa, kasa sawa ta yi sai da ta taimaka mata ta sa aka ɗaura mata ɗaurin ɗankwali, ta ɗauko ƴar karamar jaka da takalmi masu tsini ta sa mata, ita dai sai kallon takalmin take tana tunanin ta yadda mutum za iya tafiya da wannan abin ɗonono a sama. Bayan an gama mata ta ce ta tashi ta gwada tafiya, a hankali ta tashi ta soma tafiya a hankali gudun kar ta faɗi sai abin ya birge Hassana ta tafa hannu ta “Très bien matar yaya kin iya tafiyar..”
Daɗi ne ya lulluɓe zuciyar Andizo ta mata godiya, kama hannunta ta yi suka fito waje inda suka samu Salim tuni ya gama shirin sa su yake jira.

Baki buɗe yake kallon ta ganin yadda ta yi masa kyau fiye da kowacce rana sai ma sha Allah yake furtawa, hannunta ya kama suka fita a tare har Hassana suka shiga mota zuwa gidansu..

Tun kafin su ƙaraso gidan suke jiyo sautin kiɗan da yake tashi, suna shigowa gidan MC ya ce “A dakata ango da amarya sun zo kowa ya je ya zauna.”
Masu yin rawa kowacce ta koma wajen zaman ta tana son ganin fuskar amarya. Sai da suka ɗauki kunsan minti goma sannan Salim ya fito daga cikin motar ya zagaya ya buɗe mata, ita kuwa ta wani kame kamar babbar mace tana shan ƙamshi, duk wannan tsarin Hassana ne ita ta nuna mata yadda ake yanga in ana tafiya da ango in za a shiga fili, kallon ta ya yi zuciyarsa na ƙara narkewa da so da ƙaunarta, sosai ya ji daɗin ganin ta yi duk abin da aka koya mata kamar dama can ta iya, hannu ya miƙa tare da sunkuyawa ya manna mata kiss a kumatu ta bige masa kafaɗa ta ce “Ban son haka Nurul qalbi mu je mana.”
Sumar wucin gadi ya yi jin sunan da ta kira shi da shi, jinjina ya mata da hannu yana mai faɗin “Ma femme kin biya ni ɗari bisa ɗari ko yanzu, taso mu isa mana ga su Ɗahare can na jiran mu.”
A yangance ta miƙa masa hannu ya kama ya fito da ita, har za su fara tafiya sai ga Hussaina ta iso da sauri ta kama hannun Andizo ya yi saurin kallon ta.
“Yaya Mamma ta ce sai amarya ta fara fitowa da yayyunta tukun za ta fito da ango, kawo ta mu je a canja mata kaya..”
Ba haka ya so ba amma dole ya haƙura saboda ba ya taɓa muso da maganar Mamma ko da kuwa zai cutu ne, haka ya saki hannunta yana mata murmushi, ita kuwa har da ɗaga masa hannu ta yi hakan ya yi daidai da paka motar Aminatou ita da Sabrin..

Saurin kallon su Sabrin ta yi ta ce “Wai waccan ba ita ba ce amaryar?”
Shuru Aminatou ta yi tana ƙare wa Andizo kallo ganin yadda suke sakar wa juna murmushi, Salim ta kalla ta ga ya ɗaga hannu ya juya ya rufe mota ya nufi ɓangaren Mamma in da aka yi da Andizo. Wani irin zafi zuciyarta ke yi sai huci take, dafa ta Sabrin ta yi ta ce “Ke fa wani lokacin hankalinki gushewa yake a kan wancan mijin naki marar amfani, ki nutsu kar su gano wani abu a yi taron nan lafiya a gama, hakan zai ba mu damar cimma burinmu a kansu..”
Wasu zafafan hawaye ne suka zubo mata shar ta goge a hankali dan kar ta ɓata kwalliyar, fita suka yi tana dannar zuciyarta suka iso wajen 'yan gidansu da suka zo mata suka tarar ba ta gidan. Kallon ta mahaifiyarta ta yi ta nuna mata kusa da ita tana yi wa Sabrin wani irin kallo, sam ba ta son abotar ƴarta da Sabrin saboda hankalinta bai kwanta da ita ba, amma ita Aminatou ta nuna wa mamanta Sabrin ba ta da wata matsala.. Dafa ta ta yi ta ce “Aminatou ce a'uzu billahi minan sheɗani rashin sau uku, ki ƙara da cewa Hasbunallahu wa ni'imal wakil.”
Sunkuyar da kai ta yi saboda kukan da ya zo mata, gabaɗaya ta rasa inda za ta saka kanta ta ji sanyi, Andizo da Salim kawai take gani a idanun zuci suna yi wa juna kallon soyayya, da kyar ta haɗiye kukan dalilin addu'ar da Ummin nata ke karanto mata tana mata nasiha ta umarce ta da ta dinga nanata, jin zuciyarta za ta yi bindiga ya sa ta dinga nanata addu'ar da Ummi ta faɗa mata, sai da ta ɗauki minti biyar tana yi sannan ta ji zuciyarta ta samu nutsuwa sai sauke numfashi take zuba na tsatsafo mata a goshi, jin ta samu sauki sai Ummi ta ce ta dinga karantawa ko mijinta ta gani ya fito da amarya kar ta bari sheɗan ya yi nasara a kanta zafin kishi ne take ji. To ta ce tana lumshe idanu..

Bayan an shirya amarya aka canja mata wasu kayan doguwar rigar shadda irin ta su Umar yellow, ɗakin da suke Husaina ta kai ta ta ce su taso. Andizo ta kalle su ta yi murmushi ta yi kyau matuƙa sai wani maƙale hannu take ɗayan hannu kuma jaka ce irin kalar shaddar. Hussaina ta ce “Kuna ji, mutum biyu za su tsaya a gefe su riƙe hannunta sauran su jeru, sai ku fito a haka.”
To Umar ya ce yana gyara zaman hularsa, Buba da Giɗaɗo ne suka tsaya a gefen ta, har Giɗaɗo ya miƙa hannu zai riƙe nata ya yi saurin ja baya ya ce da Aliyu ya tsaya a gefen ta, shi da Umar da Iro suka tsaya a baya. Ana faɗin zuwan su aka sa musu waƙa, dukkan 'yan wajan kowa su ya zubo wa idanu sai cewa suke ma sha Allah lalle Salim ya auro ƴar Auta kuma ƙanwar maza biyar.

Ahmad da Adoul tare da abokansu suna zaune suna kallon su cike da birgewa, ana tsayar da ita Ahmad ya zaro kudi sabbin kar ya shiga filin ya dinga liƙa musu yana murmushi, ita kuwa Andizo sai murmushi take tana ƙara riƙe hannun Aliyu.. Su Ɗahare da sauran waɗanda suka zo suma sun sha ankon atamfa suka ta so suka zo filin suna yi wa Andizo liƙi wasu na rawa.
Aminatou tun da ta ƙura musu idanu sai da Ummi ta dafa ta sannan ta zabura ta ce “Ummi zan je na yi wa amarya liƙi ko na bari sai sun fito da ango?”
'Yan'uwanta suka ce ta bari ango ya fito tukun ta ce to.

Bayan sun gama aka mayar da amarya aka sake yi mata canjin kaya tare da gyara mata kwalliyar sannan aka kira Salim ya zo, suna haɗa idanu ya ɗauke cak ya yi sama da ita yana juyi a palon suna ta dariya, Hassana ta ce “Don Allah Yaya ka sauke ta ku fita Mamma sai kira na take waya.”
Sauke ta ya yi ya kama hannunta suka fita.
Suna tunkaro wajen wasu mata suka tashi ana ta zuba musu fure aka sa musu waƙar share hawayen amarya ta Umar M Sharif.
Chapter 12 · 0% Book details