← Book details Andizo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 75

Sashe 16

Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A firgice Sabrin ta juyo jin muryar wanda duk cikin maza shi kaɗai take jin tsoro, wani irin kallo ya watsa mata yana takowa ya ƙaraso tsakiyar palon, a wulaƙance yake kallon ta har ya samu waje ya zauna. Ƙafafuwanta ne ta ji suna neman kasa ɗaukar nauyinta ta ja su a hankali ta matsa daga kusan Andizo jikinta na rawa, yadda take tsoron shi ko iyayenta ba ta musu kalar tsoron da take masa, baki na rawa ta ce “Babu abin da na mata kawai magana muke.”
Baƙin glass ɗin sa ya cire ya kalli Andizo ya ce “Khadija Allah ya miki albarka tun da har kika san cewa ɗakin kwanan ku ke da mijinki sirrinku ne ba wanda yake da ikon shiga daga ke sai Yaya Salim, ke kuma ballagazar mata a tunaninki kowacce mace ma irin ki ce mai barin ƙawa tana shiga ɗakin baccinta? Wallahi duk iskancin da kuke ji zan sauke muku shi matuƙar kuka ce za ku shiga rayuwar Khadija ku takura mata, zai zo shi yaya Salim ɗin ko shi kansa sai na masa gargadi na kuma gindaya masa sharruɗa a Khadija, idan ya bari wannan banzan hannun naki ko na karuwar ƙawarki ya taɓa jikinta sai na kakkarya ku daga ke har ita, ke ko shi Salim ɗin ba zan bar shi ba sai na masa rashin mutumci..” Ya faɗa yana nuna su da tsaya..

Andizo da ta yi tsaye tana kallon su ya yafito ta da hannu ta yi saurin isowa kusan shi ta zauna a ƙasa, cikin ladabi ta ce “Ina kwana Yaya Ahmad? Ya makaranta?”
Murmushi ya sakar mata ya ce “Lafiya ƙalau matar Yaya, tashi mu tafi mijinki ya ce na kaiki office ɗinsa ba zai dawo ba yau da wuri, kuma ba ya so ya yi naisa da ke.”
'Yar dariya ta yi tana tashi tsaye ta riƙe ƙugu ta ce “Kasan Allah dama ina so naga inda mai hankali yake aiki, bari na ɗauki mayafina sabon mu tafi, amma ni dai ka faɗa wa waccan ƙatuwar matar kar ta kuskure tsautsayi ya sa ta shigar mini ɗakin da muke bacci ni da mai hankali, domin Hajiya Babba ta ce ko ƙawa na yi kar na bari ta shigan mini ɗakin bacci, ballantana ita da ban san daga inda ta fito ba. Adda Aminatou tana ganin ta za ta wuce amma taƙi hana ta.” Ta faɗa tana kallon Aminatou da baƙin cikin gasa mata magana da Ahmad ya yi ya hana ta cewa komai, tsare ta ta yi da kallo tun daga sama har ƙasa, ta matso kuma da ita tana ƙanƙance idanu masifar ta taso ta ce “Amma ai tun da na zo gidan nan da muka je ɓangarenki sai da na faɗa miki abin da Hajja ta faɗa mini ko? To yanzu kin ɓata mini rai sau ɗaya ba komai, idan kika sake barin wannan ta zo in da nake zan daina miki biyayyar da aka ce na dinga miki tun da kin girme ni..”
Wani abu ta ji ya tsaya mata a maƙoshi da kyar ta haɗiye ta kalli Sabrin ta juya da sauri itama ta mara mata biya suka fita fuu kamar za su tashi sama. Tsaki Ahmad ya yi yana cewa “Makira kawai in ba ki yi hankali ba sai ta kaiki ta baro banza kawai.”

Ɗaki ta nufa da gudu ta ɗauko mayafi ta yafa, ganin yadda ta yi ya yi dariya ya ce “Nan fa ba ƙauye ba ne Khadija, Salim ya ce ki saka hijabi ba ya son kowa yake kallon masa matarsa..”
Turo baki ta yi ta koma ta sako hijabi ya miƙe ya kashe wutar palon ya ce ta koma ɗaki ta kashe hasken ciki, kasancewar Salim ya kowa mata da gudu ta koma tana murna yau za ta ga gari ta kashe ta dawo suka tafi..

A fusace Aminatou ta shiga part ɗinta tana huci, Sabrin na isowa ta kalle ta cike da ɓacin rai ta ce “Haba Sabrin ya za ki ɓata mana shiri? Kawai daga zuwa sai ki ce mata za ki ga ɗaki yanzu ga shi za ki ja ganin girmana da take ya ragu a idanunta, Khadija fa mai sauƙin kai ce musamman in kika ja ta hira sai da na faɗa miki amma kika kwaɓa mana aiki,. Wallahi na tabbata da da hira kika ja ta babu abin da zai hana ta kaimu ɗakin mu gama abin da muke ba ta sani..” Ta faɗa tana zama tare da dafe kai ta sake ɗagowa ta dora da cewa “Nasan sai ta sanar da Salim abin da kika mata, ga shi yana ɗaukar maganarta da muhimmanci saboda ya ce ita ba ta ƙarya duk abin da za ta faɗa to an yi shi..”

Maƙale kafaɗa Sabrin ta yi tana gyara zaman mayafinta ta ce “Ke kinga kar fa daga na zo na taimake ki ki mini rashin hankali, tun da haka ne daga yau na daina zuwa gidanki ki nemi wanda zai ci gaba da nema miki magani ba dai ni ba..”
Tana gama, faɗin haka ta juya da sauri ta wuce. Tsaki Aminatou ta ja ta miƙe tsaye tana zarya, sam ba ta son Salim ya gano ba ta son Andizo saboda yardar da ya yi da ita ɗari bisa ɗari, ɗaki ta shige ta rufe kofar tare da dannawa Salim kira..

Yana ɗauka ta sa kukan ƙarya ya shiga tambayar ta, “Lafiya kike kuka? Ko wani abu ya faru bayan na fito?”
Zama ta yi a bakin gado ta ce “Mijina ban san wani tsautsayi ya sa naje ɓangaren Khadija da Sabrin ba, shi ne fa suka samu matsala..”
Da mamaki ya ce “Sabrin kuma? To ita me zai haɗa ta da Khadija daga zuwa?”

“Kasan Khadija yarinya ce babu ruwan ta da ko mutum ya girme ta in ta yi niyar magana ba mai hana ta kaima kasan da haka, ita Sabrin ta dage sai mun je ta yi wa Khadija Allah sanya alheri na ce ta bari ka fita sai ka dawo, da ta takura dai muka shiga. Shi ne fa ta ce tv palona ya fi na Khadija kyau da komai nata, to shi ne fa Khadija ta fusata Allah ya kawo Ahmad ya ɗauke ta, ya ce mini wai ba za ka dawo da wuri ba yau kuna da aiki har dare..”

Ajiyar zuciya ya sauke ya ce “Wallahi har kin tayar mini da hankali, yanzu saboda wannan abin ne kike zubar da hawayenki? Zan nuna mata in an zo ganin gida kar ta yi faɗa da kowa, amma itama ta ya za ta ce mata kayanki ya fi nata kyau a gaban ta? Wannan ai neman tada zaune tsaye ne, ba ƙaramin aikin Khadija ba ne yanzu da sun zo ta birkice ta ce sai na canja mata kayan palo na mata irin naki. Sai an jima ga Ahmad yana kirana ki kula da kanki..”

Murmushin samun nasara ta yi ta ce “To mijina ina sonka sosai Allah ya tsare sai kun dawo..”
To ya ce yana dariya ta kashe wayar, hamdala ta yi ta kwanta...

Tun da suka fita Andizo da ta yi baya ta kwanta jikin kujera ba ta ce uffan ba, saboda Salim ya ce mata ko wane ne in dai namiji ne kar ta kuskura ta dinga magana da shi ko da kuwa Ahmad ne ta yi shuru. Kallon ta Ahmad ya yi cike da mamaki ganin ba ta ce komai ba, tunani ya yi ko dai akwai abin da suka faɗa mata wanda ya mata ciwo shi ya sa ta yi shuru, gyaran murya ya yi ya ce “Matar Yaya lafiya kika shuru?”

Turo baki ta yi tana hararar shi ta ce “So kake na karya alƙawari?”

Da mamaki ya ce “Wani, irin alƙawari kuma Khadija?”

“Mai hankali ya ce kar na kuskura ko da kaine nake hira da kai rahamun ne tun da ni matar ce, dan haka ka rabu da ni kar ka ƙara yi mini magana, idan kuma kana son yin magana da ni to ka kira shi a telephone idan ya amince sai na yi magana da kai.”

Dariya ya yi ya miƙa hannu ya ɗauki waya ya danna wa Salim kira, yana ɗauka ya ci gaba da dariya yana faɗin “Mai hankali shirin Allah Angon Andizo uwar masu gari.”

Murmushi Salim ya yi yana gyara tsayuwar shi ya ce “Gani ba saƙo ba, da wa kuka yi gardama a raba muku? Ina Khadijar tawa take?”

“Ga ta nan tana cika tana batsewa kamar fulawa, kai ka ce mata kar ta yi magana da kowa in dai mutum namiji ne? To a ba ni izini na tambaye ta abin da take son ci na sayo muku..”

Shafa sajensa ya yi ya ja numfashi ya ce “To na ba ka, izini ka yi magana da ita, amma kar ta yi yawa dan ba na son kowa yake jiye mini muryar matata.”

Kallon ta Ahmad ya yi yana cewa “To yaya sai mun ƙaraso.”
To ya ce masa sannan ya kashe kiran..

“To matar yaya ya ce ya ba ni izini na yi magana da ke, me kike son ci?”

“Ni marmarin masa da miya nake.”
Zaro ido Ahmad ya yi yana yin packing a bakin Restaurant, kallon ta ya yi ya ce “Khadija nan fa ba ƙauye ba ne, ina za mu samu masa a nan.”

“To sayo mini duk abin da ka gani.”
To ya ce mata ya fita sai kuma ya buɗe mata ya ce ta fito su shiga ta ga yadda cikin yake, da sauri ta fito dama ranta na son ganin abin da yake ciki.
Shawarma da kaza ya sayo musu, Andizo ta soma kalle-kalle Ahmad ya sunkuya a hankali ya ce “Karki dinga kalle-kalle a sace ki.”
Da sauri ta dawo gefen shi tana kallon wani matashin saurayi, tun da ta sanyo kai cikin restaurant ɗin ya kafe da kallo, kalaman Ahmad ya sa ta ji tana tsoron wannan matashi.
Yana gama biyan kuɗin ya yi gaba ta biyo shi da sauri suka fito, kafin ya isa ta riga shi ta buɗe motar ta shiga tana dafe ƙirji. Dariya ya yi ya ce “Matsoraciya kawai.”
Murguda masa baki ta yi suka wuce..
Chapter 16 · 0% Book details