Sashe 52
Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Tana miƙa wa Hajiya turaren da Sultan ya ba ta ya iso ya tsaya a kanta ƙerere, kallon shi ta yi ba ta ce mishi komai dan ta lura sam ba shi da tausayi, a wannan halin da take ciki ma sai ya ƙuntata mata. Dogon numfashi ta ja ta miƙe tana yatsina fuska ta ce “Mamma zan je na kwanta idan Umma ta kira ku ce mata ina gaishe su an jima zan kira ta na ga su Khadija.” Ta faɗa tana yin gaba Mamma ta amsa da cewa “To kar dai ki kwanta da ba ki son cin abinci in ba ki da lafiya yanzu zan sa a kawo miki abinci, sannan ai kin ji me Sultan ya faɗa miki bayanin likita dai ko?”
Gyara kai ta yi tana runtse ido har yanzu kafar zafi take mata ta yi gaba, da kallo ya bi ta sai kuma ya ɗauki ledar maganinta da ta manta ya ce “Bari na kai mata kinga har ta fara halin nata, gara na je na sake jadadda mata shan magani a kan lokaci kar ta yi wannan sakarcin nta da ta saba.”
Ba wanda ya ce mishi kalzil har ya bar palon domin Hajiya ta ce kar wanda ya sake shiga sabgar su wata ƙila ta hakan sai Allah ya sa wa Khadija son Ahmad, shi ya sa kowa ya bi shi da kallo. A hanya suka haɗu ya ce “Ina za ki je?”
“Maganin ne fa na manta zan je na ɗauko.” Ta faɗa tana kallon maganin da ke hannunsa.
“Mu je ciki ki sha na yamma kuma ban da sakaci dan na san halinki.”
Turo baki ta yi kamar za ta yi kuka ta ce “Yaya Ahmad maganin ne akwai ɗaci fa.”
Murmushi ya sakar mata wanda rabon da ta ga ya mata irin wannan murmushi har ta manta, hanya ya nuna mata ta juya ya bi bayan ta har ɗaki, zama ta yi tana maida numfashi ya kalle ta yana dariya ya ce “Raguwa kawai wannan ƴar tafiyar da kika yi ai ne har kike huci kamar wata ƙatuwar mace wadda take tashi da kyar zama da kyar.”
Sunkuyar da kai ta yi ta ce “To ai ƙafata ce ta riƙe ciwon har cikin ƙwaƙwalwarta nake ji, ba ni maganin na sha zan kwanta ko ciwon ya ragu.”
Duk da ya ji tausayin ta amma bai nuna ba maganin kawai ya ba ta ya dawo kitchen ya ɗibi ruwa ya kawo mata ta sha maganin, sai da ta kwanta sannan ta ce “Merci.”
Tun da yake da ita bai taɓa mata abun arziƙi ta ce mishi ta gode ba sai abin ya ɗan ba shi mamaki, amma tuna shirinsa a kanta sai ya yi murmushi ya kai hannu ya shafa kumatunta duka biyun ya ce “Meye na godiya kuma Khadija? Ni ba na son muke yin faɗa da ke ya kamata mu shirya muke girmama juna.”
Ɗago kai ta yi ta kalle shi ya kanne mata ido ɗaya ta kumbura baki, sai da ya sake kiran sunanta sannan ta ce “To ai dama kaine kake zalin ta ta ni me nake maka wanda yake cutar da kai?”
Jim abin da ta faɗa sai ya samu gefen gadon ya zauna ya ce “Khadija kina so mu daina faɗa?”
Kai ta gyaɗa mishi ya gyara zama ya ce “To inda kina so mu fasa faɗa sai dai ki yi wani abu ɗaya wanda zai kashe duk wata rigimar da ke tsakani na da ke.”
Kallon shi ta yi sai kuma ta ce “In dai za ka daina mini mugunta zan yi matuƙar bai saɓa wa addini da al'adata ba.” Ta faɗa a sanyaye kallon shi domin ta gaji da cutar da ita da yake yi a kullum kamar jikan Fir'auna.
Kallon ta ya yi sai kuma ya kalli gefe ya yi murmushin da shi kaɗai ya bar wa kansa sani sannan ya ce “Ina so ki daina kula Sultan idan ya zo zai ɗauke ki, ke gabaɗaya ma ko magana ba na so ta shiga tsakanin ku dan bai cika sharruɗan mijin aure ba, musamman idan kika duba yadda mata suke bin shi yan iska rikakku ke har turawa kansu Sultan bai bari ba sheƙe ayarsu suke, kinga kuwa ai ba abin ki tsaya kina sauraron shi ba ne ni fa ba ni da tabbacin Sultan yana yin Sallah, kayan maye kuwa babu abin da ba ya sha me za ki yi da irin wannan namijin?”
Zaro ido Andizo ta yi cike da al'ajabi ta ce “Dama har neman mata yake ashe? Ashe ɗan iska ne? Ni dai nasan yana shaye-shaye a gaban idona ya sha giya ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba, amma yanzu ya ce mini duk ya tuba yana Sallah ya rage shan kayan maye..”
Haushi Ahmad ya ji a zuciyarsa da Sultan ya sanar da Andizo ya tuba, amma a fili sai ya daddage ya nuna mata sam bai daina ba ya ce kuma in ta yarda yana taɓa jikinta wata rana zai iya cutar ita ya mata faɗe, tsoro ya kama Andizo ta ce ta daina kula shi har abada. Murmushi ya yi ya ce “Yawwa ba na son wani ya cutar da ke kinga ke amana ce a wajen mu ki tayamu ruƙon amanar ki don Allah Khadija.”
Kamar wata ƙadangaruwa ta gyaɗa mishi kai ta ce “To in sha Allah.” Ta faɗa tana kwanciya shi kuma ya fita ya bar ɗakin ransa fes tun ya samo lagon ta zai raba su cikin ruwan sanyi..
_Maman Nusaiba ce_
[6/30, 12:13 AM] Ummu Amjad: ADZ
42
Sai da ta tabbatar ya fita sannan ta tashi zaune ta tafka tagumi hannu biyu, tunani ta dinga yi yadda Sultan ya dinga kula da ita a wannan 'yan kwanakin, sannan tun da suke haɗuwa ba ta taɓa ganin alamar har yanzu yana shan kayan maye ba, ajiyar zuciya ta sauke ta kalli zoben da ya saka mata. Har ta kusa cire zuben sai kuma ta fasa amma sam hankalinta ya kasa kwanciya game da maganar da Ahmad ya faɗa a kan Sultan ɗin, girgiza kai ta yi ta ce “Zan tambayi Amira naji idan har na tabbatar bai daina ɗabi'ar da na sanshi da ita ba to zan yanke duk wata alaƙar da za ta haɗa ni da shi har abada, ba zan yarda ya cutar da ni ba.” Komawa ta yi ta kwanta tana ta saƙe-saƙe har bacci ya yi gaba da ita.