← Book details Andizo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 75

Sashe 73

Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wayarsa ce ta ɗauki ruri ya duba ya ga Taufiƙ ne ke kira, ɗagawa ya yi kafin ma ya yi magana shi ya riga shi yin.
“Malam idan ba za ku zo ba sai ka sanar da ni, ka shanye mu kamar kayan wanki kuma kasan gobe ne za a fara buga wasa kana sanya yankin gara.”
Hannu ya sa aljihu ya nisa sannan ta ce “Mayar da wuƙaƙen gamu nan fita madam ce ta ɓata mana lokaci.” Yana faɗin haka ya ɗauke wayar daga kunnensa ya sa a aljihu, kallon ta ya yi sai wani basarwa take tana hararar shi ta gefen ido, gaba ya yi yana mata alama da a biyo shi ba muso ta bi bayan shi suka yo harabar gidan.

Har suka isa babu wanda ya cewa wani ƙala, shi kam ya shiga damuwa na wannan ɗaukan Allah gangamon da ta yi da shi alhalin ba ta tsaya ta bincika ta gano gaskiyar lamari ba, a palo suka same su ko zama Sultan bai yi ba Taufiƙ ya kalli agogo ya ce “Oya muje.”
Kallon Limat ya yi gaba ta biyo shi, a bakin mota suka tsaya ya dube ta da yanayi tausayi ya ce “Ƙanwata don Allah ki taimaki yayanki, Khadija yau sati uku kenan ba ta mini magana komai da kika sani na mata da miji ba ta yi, na rasa gane kanta wani lokacin sai na ga kamar aljannun da suka shiga jikinta ne suka dawo.”
Da mamaki ta kalle shi har da riƙe baki domin yadda suke waya da ita tana fallasa mata sirrin zuciyarta irin son da take mishi sai ta ji maganar tashi ta mata banbarakwai, gyara tsayuwa ta yi ta kalli Taufiƙ da ya juya musu baya ya yi kamar ba ya jin me suke faɗa, kallon Sultan ta yi ta ce “Bro ka tabbata babu abin da ka yi mata? Anya Khadija za ta kwashe kusan wata ɗaya tana fushi da kai ba tare da wani ƙwaƙƙwaran dalili ba? Ka dai faɗa mini abin da ka mata ta hakan ne zan samu damar shayi kanta ta sauko, idan kuma ba ka faɗa ba ni ba zan iya ba gaskiya.”

“Madam shi ne da lefi ba Khadija ba, wannan fitinanniyar yarinyar ce take son dawowa cikin rayuwarsa, shi ne ta gano abin da ke faru hae hka ta faru amma ki same ta ku yi magana.” Taufiƙ ya ƙarashe maganar yana shige da wa mota.
Zaro ido Limat ta yi sai kuma ta juya tana faɗin “Bro ka kwantar da hankali zan shayo kanta.”
Jiki a sanyaye ya shiga motar suka bar gidan.

A inda ta zauna a nan ta same ta, zama ta yi ta kira mai musu aiki ta sa aka kawo mata lemo mai sanyi da cake, babu abin da ta taɓa sai murmushin yaƙe da take har Limat ta gama shirya yaranta suka fita za a kaisu wajen wasa, bayan ta dawo ne ta dube ta ce “Khadija wai lafiya na ga kin rame shima ya rame kamar kuna shan ruwan zafi? Me ke faruwa?”
Hawaye ne suka zubo mata ta sa hannu ta goge Limat ta matso kusa da ita ta dafa ta cikin nuna kulawa ta ce “A tunanina na zama 'yar'uwarki uwa ɗaya uba ɗaya duk abin da ya ke damun ki za ki zo ki sanar da ni, ashe ke ba ki ɗauke ni a matsayin yayarki ba shi ya sa kike ɓoye mini abin da yake damun ki.”
Kuka take sosai har da ja numfashi Limat ta zuba mata ido duk sai ta ba ta tausayi, sai da ta yi mai isar ta sannan ta riƙe hannunta ta ce “Ki sanar da ni abin da ya sa kika rame.”
Baki na rawa ta fara magana “Anty ina jin kishin sa kamar na mutu, Wallahi ba zan juri na ga wata mace a, waje tana bibiyar shi ba in dai ba auren ta zai yi ba, amma a kan kullum za take kiran shi ba dare ba rana text message ya fi a lissafa wanda take mishi a kodayaushe, wai har ce mishi take ta yi kewar kwana a jikinsa da ƙamshin turaren da ya saka wa yaushe zai zo su gaisa? Wata kalmar ta yi mini girma ba zan iya faɗa miki ba ni ba zan iya zama ba gara ya mayar da ni ƙasarmu.” Kuka ta kuma sakawa Limat ta girgiza kai tana dariya, jin hakan ya sa ta tsayar da kukan tana kallon ta cike da mamaki, gyara zama ta yi ta fuskance ta ta ce “Ba ki san waye Sultan ba har yanzu Khadija, shi mutum idan ya ce ya bar abu to fa ya bar shi har abada ba zai ƙara waiwayar wannan abin ba, da ta dinga turo mishi da message kin taɓa gani ya mata reply ko da sau ɗaya ne?”
Girgiza kai ta yi ita kuma ta ɗora, “To ki farka daga nannauyan baccin da kike ki dawo haiyacinki, ke za ki dage ki kwace mijinki ki zame mishi mace guda ɗaya tilo a zuciyarsa, wannan fushin da kike duk ba shi zai sa Jennifer ta rabu da Sultan ba, shi ya rabu da ita tun lokacin da kika shigo rayuwarsa ya watsar da duk wani abu marar kyau ya koma makarantar addinin islama neman ilimi.”
Ji ta yi kaso tamanin bisa ɗari ta gamsu da bayanin ta, a hankali ta buɗe baki kamar mai koyon magana ta ce “Anty dama can tun asali yana neman mata? Ko kuwa da ya dawo nan ƙasar ne ya buɗe ido da su?”
Girgiza mata kai ta yi sannan ta ce “Sultan ya taso cikin gata da sangarta irin na wasu 'ya'yan masu kuɗi, mahaifinsa ba ya son ganin ɓacin ransa shi ya sa yake lallaɓa shi tamkar shi kaɗai ne ɗan da ya samu bayan akwai wani namiji kafin shi, kasancewar sunan mahaifinsa aka sa mishi sai ya fifita shi a kan yayansa Rudwan, bayan shi kuma aka haifi su Doctor Rahama nasan kin gansu. Kwanci tashi har suka zama samari baba ya haɗa su lokaci ɗaya ya musu aure da matan da suke so, tun ya taso yake da burin yin kwallon ƙafa baba ya goya masa baya duk da Mom ta nuna ba ta so, haka ya dinga ƙoƙarin cika mafarkinsa. Bayan shekara da aurensu ya zama shahararre a fanni kwallon ƙafa in da ya dawo nan London da zama, mata dayawa sun kawo kansu gare shi amma shi sam ba sa gaban shi ta matarsa yake har Allah ya sa ta samu ciki ta haifi 'yarta mace wato Farrah, sosai muka yi murna da samun ƙaruwa suka dawo gida aka ci gaba da kulawa da matarsa da jaririya, wata uku da haihuwar Farrah wata ranar Lahadi da ba za mu taɓa mantawa da ita ba wadda familynmu ke kira baƙar rana, sun shiga jirgi su duka za su zo wajen aurena suka yi hatsari wasu suka mutu wasu suka jikkata haka aka yi asibiti da su. Waɗanda suka mutu sun haɗa da Rudwan da matarsa, Baba, mahaifiyar Farrah, su kuma su Sultan su ne suka ji ciwo. Kowa sai da ya tashi aka bar Sultan a doguwar suma har na tsayin wata ɗaya, bayan ya farfaɗo aka sanar da shi mutuwar matarsa ranar sai da aka kulle shi a ɗaki, domin hauka tuburan ya dinga yi yana fashe-fashen kaya ya ce shi matarsa da su baba ba su mutu ba, sai da aka kusa shekara sannan ya dawo cikin nutsuwarsa ya dangana. Shi yake kula fa Farrah tare suke kwana duk abin da uwa take wa ɗa shi yake yi mata, Mom ta yi faɗan ya bari ita ta ci gaba da kula da ita amma sam ya ƙi dole ta rabu da shi, Farrah ta cika shekara biyu amma kullum in ya duba wani abu na mamanta sai ya shiga kunci dole ta sa ya dawo nan London gabaɗaya da zama..
A cikin wannan yanayin ne ƙaddara ta haɗa shi da Jennifer, wata rana ya fito zai zo nan gidan ya buge ta da mota sai ya kai ta asibiti, bayan ta farfaɗo sai ya nemi sanin gidansu ta faɗa mishi ya ɗauke ta suka tafi. To da kaɗan-kaɗan yana zuwa ya zubo ta ko ya sa yaransa su kai mata kayan abinci kasancewar iyayen Jennifer ba masu ƙarfi ba ne talakawa ne, shi ya sa yake jin tausayin ta har ta samu ya ba ta number shi suke gaisawa idan ya samu time, ƙarshe dai suka kulla soyayya har ya faɗa mata matarsa ta rasu, ta tausaya mishi sosai ta dinga ba shi kulawa da kyautata mishi iya iyawarta, bayan ta samu shiga sai ta nemi kusanci da shi sosai ƙarshe dai suka zama kamar miji da mata, na yi baƙin ciki ganin ɗan'uwana ya zama mazinaci amma babu yadda na iya. Ita ta canja mishi rayuwa a baya da iya kwaya yake sha a gida sai ya zamana duk wani nau'i na kayan maye babu wanda ba ya sha, ita koya mishi zuwa club iri-iri da dare ba shi da aiki daga zuwa yawon banza sai buga kwallo, komai nashi ya canja har Mom ta gano ɗanta ya zama rikakken ɗan shaye-shaye, ke in taƙaice miki Jennifer ba ƙaramar makira ba ce kaɗan ya rage Sultan ya bar musulunci saboda da ita, sai Allah ya shigo da ke cikin shafin rayuwarsa daga nan ne ya dinga neman ta yadda zai ɗauko ki. Labarin auren ki da ya ji a nan ya yi jiyar jikinsa a cikin gidan nan ko buga kwallo ba ya zuwa ya ɗauki hutun sati biyu, da kyar ya dawo daidai a lokacin ya yanke alaƙarsa da Jennifer.” Ta ƙarasa faɗa mata yadda suka rabu da yadda ta dinga bin hanyoyi wajen ganin ya dawo gareta, a ɗago suka haɗa ido da ita ta ce “Wannan shi ne ɗan taƙaitaccan tarihin Sultan, shi ne za ki bari mijinki ya ƙara faɗa wa tarkon waccen sheɗaniyar?”
Chapter 73 · 0% Book details