Sashe 28
Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dariya ta yi ta ce “Daddy ne sai yau ya ga damar kira na, ya ma ce na gaishe ki ko Daddy.” Ta faɗa tana kallon Sultan da ke zaune yana shan tea. Jinjina kai ya yi ya ce “E ina gaishe ta ko kuma tare n?” Ya tambaye ta saboda so yake ya ganta.
Juyo wayar ta yi ta ce “Ga ta nan ta juya baya ma, juyo Khadija Dad na miki magana.”
Gyara ɗankwali ta yi Sam ba ta son yin magana amma dan kar Farrah ta ga ta mata wulaƙanci ta juyo ta murmushi a fuskarta ya ce “Barka da dare Daddy.”
Waro idanu ya yi bai san ba lokacin da ya tashi tsaye ya ce “Wow Khadija ke ce kika zama babba haka?”
Kawar da kai ta yi ta sauka a gadon ta zauna a ƙasa, saboda yanzu ta san ciwon kanta ita matar wani ce magana da wani namijin haramun ce a gareta in ba ta zama dole ba.
Washegari ta shirya tsaf ta tafi ècole ita kuma Farrah ta tafi gidan sister Mom, yau ko Salim ba ta gani ba da idonta itama ta basar ta ci gaba da lamuran ta..
Da yamma gidan ya cika da dangin Aminatou sun zo taya ta murna, ko da wasa ba ta yi gigin zuwa ba duk da kuwa kiran ta da Aminatou take a waya amma ta ƙi ɗauka, gabaɗaya yau sukuku ta wuni ba ta son ganin kowa tana son ta keɓe kanta..
Bayan sati biyu da faruwar haka Andizo ta dinga ciwon kai mai tsanani har ya hana ta zuwa makaranta, kullum a ɓangaren ta Aminatou take tana zaune da ita har Salim ya dawo. Ganin abin ba na ƙarewa ba ne Hajiya Babba ta sa aka kira likitansu ya turo nurse ta zo har gida ta duba ta. Sai ta gama mata gwaji ta ce ta yo fitsari ta kawo mata, da kyar aka tashe ta saboda ko buɗe ido ba ta iya yi. Tana yi ta kawo mata ta musu Sallama ta ce gobe za ta zo da sakamakon duk abin da yake damun ta..
Washegari dai ta dawo ɗauke da takardar Andizo na da cikin wata biyu da sati biyu cif, murna sosai Hajiya Babba ta yi da samun ƙaruwa har biyu a lokaci ɗaya, ranar Salim kuɗi mai yawa ya dauko ya miƙa wa likitar ya ce goron albishir ne. Ita kanta Andizo ta ji daɗin samun cikin amma ciwon kan na damun ta.
Sai da ta yi sati sannan ta samu sauƙin ciwon kan ya tafi, Allah ya taimake ta ba ta yin laulayi mai wahala kawai kwadayi take ji ga cin abinci kamar gara, da ta ci abinci an jima za ta ci kamar an mata sata sai ta ƙara ci, hakan ya sa Salim ya jibgo musu sayayyar kayan maƙulashe ita da Aminatou. Gabaɗaya da gari ya waye sai su tafi part ɗin Mamma a can za su wuni sai lokacin girkin abincin dare ya yi su dawo..
Next Fage
_Maman Nusaiba ce_
[6/6, 11:43 PM] Ummu Amjad: _*AREWABOOKS@SARATALKASUM88*_
30
Sanye take da doguwar rigar abaya ta ɗora ɗankwalin a kan kafaɗarta, hannunta ɗaya riƙe da plate ɗin Indomie ta ciko shi taf har baki yayin da ɗayan hannun shi kuma gorar ruwa ce babba ta riƙe.
Kallon ta Aminatou ta yi ta girgiza kai, sai da ta aje a gaban ta ta ce “Adda za ki ci Indomie?”
Done hanci ta yi tana yi fifita da hannu, kallon Indomie ta yi ta miƙe da sauri ta nufi banɗaki, Andizo ta bi da kallon tausayi tana faɗin “Allah sarki Adda Allah ya ba ki lafiya ki daina aman nan.”
Sai da ta gama amayo duk abin da ta samu ya ɗan zauna a cikin sannan ta wanke bakinta ta fito tana nishi, baki ta buɗe kamar sakarya tana kallon Andizo da take shanye ruwan Indomie ta cinye tas, waje ta samu ta zauna tana huci ta ce “Gaskiya Khadija kin ji daɗin ki babu ruwan ki da amai irin nawa.”
Gyatsa ta yi ta ɗauki ruwa ta sha sosai sannan ta aje, murmushi ta yi ta kalle ta ta ce “Gaskiya ni kam ina tausayin ki sosai Adda, kalli fa ki ga yadda kika rame kamar ba ke ba kin ƙara koɗewa kamar ana miki wankan farar fauda, I'm ba dan ba ma shi ne da na ci kamar kuturu ai da sai ya bari ki tafi gida dan ki samu kulawa ta musamman, to yaƙi daɗi nima na yi kukan na gaji a kan ya kaini na ga gida amma ya ce ba za je ba wai sai na haihu, yanzu fisabilillahi sheraka ta biyu fa har da watanni a gidan nan ban taɓa zuwa garinmu ba, ko wani nawa babu wanda ya zo na ganshi naji daɗi, Farrah ce kawai ta kawo mini ziyara.” Ta faɗa tana goge hawayen da suka gangaro kan kuncinta, sam yanzu ta ji ba ta son zaman gidan duk ya ishe ta musamman cikin jikinta da ta iya bacci kusan a tsaye take kwana..
Dafa ta Aminatou ta yi ta ce “Karki damu Khadija duka saura wata nawa mu haihu ma, nan da wata uku fa duk mun haihu kinga sai ki tafi ki ga gida da ɗiyarki ko ɗanki gwanin sha'awa. Ni kaina da nake ciki garin kina gani dai yau wata na 4 da ɗoriya ban je gidanmu ba ya hana ni fita, kina ce y ce wai ba ya so a wahalar masa da yara kamar ba mu muke ɗauke da yaran nasa ba..”
“To shi kenan Adda amma dai ke ya kamata ki je gida ko kwana biyu ne ki yi dan Wallahi kina buƙatar kulawa ta musamman, shi ba a gida yake ba bare ya kula da ke kuma ya hana wani ya kula da ke, da a ce ni bani da komai sai na dinga kula da ke har ki haifo takwara ta..”
Murmushi ta yi ta ce “Zan sa Mamma ta mishi magana ko zai bari, Ian so na samu hutu sosai duk da a nan ɗin ma ba wani abu mai wahala muke ba iya girki ne.”
To Andizo ta ce mata suka ci gaba da tattaunawa domin samo hanyar da zai bar kowacce ta tafi gaban iyayenta a kula da ita...
Washegari Salim ya dawo daga wajen aiki bayan Sallar isha'i Mamma ta ce tana son ganin shi, sai da ya ci abinci ya huta sannan ya nufi part ɗin su. Da sallama ya shiga suka amsa shi Hassana ta yi dariya ta ce “A a ga Abban 'yan biyu.”
Murmushi ya yi yana shafa gemu in aka ce masa Abban 'yan biyu jin kansa yake a sama, zama ya yi yana gaishe su suka amsa da lafiya.
Mamma ce ta fito daga ɗaki ta kalle shi yana gaishe ta ta amsa tana tambayar shi wajen aiki ya ce Alhamdu Lillah, sai da suka yi hira sosai sannan Mamma ta kira sunanshi, hakan ya sa ya gyara zama ya tattara duk wata nutsuwar shi ya miƙa mata.
“Salim me ya sa ka hana Aminatou ta je gidansu ta yi kwana biyu? Haba wannan ai taushe haƙƙin ne wata nawa ba ta sa iyayenta a ido ba ka gana ta? Kuma gara ma ita a kan Khadija ita da tun da aka kawo ta ba ka taɓa cewa kai bari na kai Khadija ta je ta ga iyayenta da 'yan'uwanta ta sada zuminci, kawai ka kime su a gida kuma ba wanda ya kawo musu ziyara ai damuwar sai ta yi yawa. Ina so ka barsu su je su ga iyayensu, Aminatou ta je gobe ta ta yi kwana biyu saboda Umminta kullum sai ta kira ta tambaye ni ya jikin nata, ta ce tana so ta zo gida k hana ta ita kuma da ta faɗa mata ta ce ta haƙuri ta bi umarni mijinta za su dinga waya. Haka su Hajja da an yi kwana biyu sai Maigari ya kira yana tambayar ba dai matsalar komai a game da jikarsa? Na ce masa ba komai sannan ya kashe waya, wannan son kan naka ya yi yawa ka tausaya musu mana.” Ta faɗa tana kallon shi..
Sunkuyar da kai ya yi yana sosa ƙeya, shi fa ba ya son su matsa daga inda yake. Ɗagowa ya yi ya kalli Mamma ya ce “To Mamma in sha Allah gobe sai ta je ta musu kwana biyu ko uku ta dawo, ita kuma Khadija nan da sati ɗaya zan kai ta itama ta yi kwana biyu ko ukun naje na dawo da ita.”
“Kai na ci butar ubanka Salimu, yarinyar ta shekara biyu cir har da ɗoriya ka ce wai ka kaita ta yi kwana biyu ko uku ka ɗauko ta ba ka kirki ashe ban sani ba? To ba ka isa ba sati za ta yi ko sati biyu ko kai ka haifa musu ɗiyar da za ta yi kwana biyu ta dawo kamar wadda ake kora daga garin? To ba na son wannan rashin kunyar taku ta sojoji, kuma su kansu sun matsu su ganta ko da za ka auro ta ciniki aka yi suka sayar maka da ita?” Ta faɗa tana dungure mishi kai..
Dariya Hassana ta yi ta ce “Kuma fa haka ne Hajiya ai in da a ce ni ce a zaman Khadija Wallahi summa tallahi idan na dinga ma kuka da buri dole ka kaini na ga iyayena, yo ina zan iya shekara biyu gari ba wani nisa mai yawa ba ban ga dangi ba..”
Duka ya kai mata ta yi saurin komawa bayan Hajiya Babba, nuna ta ya yi ya ce “Idan manya suna magana kika ƙara sa baki sai na kakkarya ki.”
“Kai dallah gafara daga nan, ita ba mutum ba ce da za ka ce ba za ta sa baki a al'amuran da suka shafi rayuwarka ba?”
Shuru ya yi bai sake cewa komai ya ɗauki wayarsa ya miƙe ya musu sallama ya tafi.