Sashe 23
Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Ko ma me ya faru Abida ke kika ja mini, yau in dai Salim ya kora ni gidanmu ke ce sila da ba ki da kimtsin magana kin faɗi abin da ya fusata shi ga shi yau wai har ni Salim yake yi wa tsawa, ki maza ki tashi muje ya ce yana son ganin ki..”
Tsaki ta ja tana tashi dan ita ba ta ga wani abin tayar da hankali ba dan ta ce wa Khadija ba ta uba, tana zuwa ta samu waje ta zauna ya ɗago ya kalle ta, kamar za ta saki fitsari ta ji ganin yadda Salim ya koma.
Rai ɓace ya ce “Ke waye ya ce miki Khadija ba ta da uba? Sannan ma wa ya ba ki izinin shiga hurumin gidana ke ba matar gida ba? Kinga ina miki wasa da na fuskanci ke ba ki da kunya? To yau in ba ki faɗa mini wanda ya sanar da ke wannan maganar ba in kuma ke kika tsara kika faɗa sai kin kwana barikin sojoji, ita kuma 'yar'uwar taki da kike tinƙaho in ta bar mini gida sai na ga ta inda za ki zo har cikin gida ki faɗa wa matata maganar da za ta firgita mata lissafi..”
A ruɗe Aminatou ta durƙusa ta ce “Don Allah Salim karka hukunta ni da barin gidanka, Wallahi ina sonka ba zan iya zama wajen da babu kai ba, ni iya gaskiyata nake faɗa maka ban san a ina ta ji wannan maganar ba, da ta faɗa ma sai da na yi ta mata faɗan me ya sa ta faɗa mata haka..”
Kallon hadarin kaji ta musu Salim ya daka mata tsawa sai ga ta ta takure a waje ɗaya.
“Za ki faɗa ko ba za ki faɗa ba?”
“Wallahi nima a wajen Anty Sabrin naji tana faɗi, ita ta ce ta sa an bibiyan mata duk wani abin da ya shafi rayuwar Khadija an tabbatar mata ba ta da uba wasu mutane ne 'yan gudun hijira suka tsince ta, shi ne suka zo wannan ƙauye Maigari garin ya ba su mafak..”
Tun kafin ya ƙarasa ma sai jin saukar mari ta yi tas! Tas! Aminatou ta wanke ta da maruka masu zafi, ƙafa ta sa ta yi bal da ita tana huci ta ce “To kenan so kuke ku kashe mini aure na dawo gida mu zauna ake lissafa mu ko? Ita Sabrin ɗin uban wa ya ba ta izinin yin hakan? Wallahi kika yi sanadin kawo saɓani tsakanina da mijina sai na illata ki ta yadda ba za ki moru ba..”
Kuka Abida ta sa tana shafa kuncinta ta miƙe tsaye cike da rashin kunya ya ce “Saboda wannan juyan mijin naki ne kika mare ni ? Wallahi sai na rama ta in da ba ki tsammani ba tun da kika mare ni dan an taɓa waccan kucakar ya..” Sake ɗauke ta ta yi da mari za ta ƙara mata Salim ya ruƙo ta ya ja ta ya zaunar, hanyar waje ya nuna mata ya fita palo ki bamu guri..”
“Kar ta kuskura ta zauna mini a gida tun da ita ta zama tawatsa watsa gida tana son ta watsa mini rayuwa, maza ki fita direba ya kaiki kar ma ya tafi gida zan zo gobe gidan daga ke har Sabrin ɗin sai na muku iyaka da gidana..” Ta faɗa tana huci..
“Gidan banza gareki ai nima ba daga sama na faɗo ba daɗin ta ma muna da gida, aikin banza da kina da 'ya'ya ne za ki yi tinƙaho da gidan, ke da ko kashi mai tauri ba ki taɓa yi ba shi ne kike fifita mijinki a kan ƙanwarki? To ki yi zaman duniya a gidan mijin ki gani juya kawai..” Tana gama faɗin haka ta fita fuu ta bar gidan..
Kuka sosai Aminatou ke yi kamar za ta shiɗe, sosai take jin raɗaɗi da azabar zafin gorin haihuwa da Abida ta mata, wai yau ita ce ƙanwarta take cewa juya to idan wani ya ce mata juya a gaban ta ai ba za ta ce komai ba.. Ruwa mai sanyi Salim ya ɗauko mata ya ba ta ta sha, ajiyar zuciya ta dinga saukewa ta rasa ma da me za ta ji ba ta so Salim ya ga lefin ta a kan wannan lamarin, durƙusawa ta yi har ƙasa ta riƙe ƙafafuwansa wasu hawayen na bin kuncinta ta ce “Don Allah mijina ka yafe mini kar ka ga lefina a wannan lamarin, Wallahi ban san me ya sa Sabrin ta sa aka mata wannan binciken ba..”
Tausayi ta ba shi amma ya danne ya ce “Duk ke kika jayo komai ya faru, da da kike riƙe sirrinmu wa ya taɓa miki gorin haihuwa daga dangina har mutanen da kike hulɗa da su? Ke kika fara fitar da sirrin gidan aurenki shi ya sa har suka samu damar yin hakan kuma suke son dagula wa ƙaramar yarinya hankali da ba ta gama sanin rayuwa ba, idan kinga dama ki ci gaba da buɗe sirrin aurenki matsalar ke za ta shafa, ni dai ba za ki jefa ni cikin damuwa ba na rasa da wanne zan ji, in kin yi hankali daga yau sai ki gyara kuskuren ki..”
Yana gama faɗin haka ya tashi zai wuce ta yi saurin tashi, da hanzari ta rungume shi ta baya kuma sa kuka tana roƙon shi.
“Don Allah mijina karka hora ni da lefin da ba ni na aikata maka ba, Wallahi ba zan sake faɗin sirrin aurenmu ka yi haƙuri fushinka zai ƙara saka ni a cikin wani hali..”
Ya so ya share ta amma yadda yake jin jikinta na rawa sai ya fasa ya juyo ya rungume ta yana bubbuga bayan ta, sai da ta yi shuru sannan ya ce “Ba komai ya wuce, kin san dama ai ba zan taɓa yin fushi da ke ba kawai dai raina ya yi matuƙar ɓaci, yanzu haka saboda abin da Abida ta faɗa wa Khadija ta ci kuka har zazzaɓi ya rufe ta tana can na baro ta na ce sai na zo naji dalilin faɗa mata wannan muguwar kalmar..”
Ɗagowa ta yi daga jikinsa tana share hawaye ta ce “Inna lillahi wa inna laihin raji'un! Don Allah mu je na ga jikin nata, dama da ta shigo ta ce abincin da muka ba ta ƙamshin shi ya buwaye ta kamar za ta yi amai, muje ina so na nemi yafiya ta a kan abin da Abida ta mata..”
Jinjina kai ya yi ya ce “Ki kasance a Aminatoun da na sanki matata, ka da ki bari zugar ƙawaye ko ta dangi ta sa ki canja daga mutuniyar kirki zuwa ta banza..”
“In sha Allahu mijina na tuba ba zan sake biye musu ba su kaini su baro.”
Fita suka yi a tare har part ɗin Andizo.
A palo suka same ta ta rafka tagumi hannu bibiyu ta ƙura wa tv ido, kana kallon ta za ka san ta lula duniyar tunani Salim ya nuna mata ita da hannu ya ce “ Kin gani ko abin da nake faɗa miki, ba ta taɓa shiga damuwa da tashin hankali ba irin na yau..”
Saurin isowa Aminatou ta yi ta zauna a kusa da ita, hannu ta sa ta janye mata tagumin ta yi firgigit za ta tashi ta ruƙo ta, kallon ta ta yi sai kuma ta janye hannunta da ke cikin na Aminatou ta tsaya tana kallon ta.
“Khadija don Allah ki yi haƙuri kin ji, na zo ne na nemi yafiyar ki a kan abin da ƙanwata ta miki..”
Dawowa ta yi ta zauna tana kumbura baki ta kalli Salim ta ce “Mai hankali ka faɗa mata ni ba 'yar tsuntuwa ba ce da ubana da uwata auren sunna aka yi aka haife ni, 'yan bindiga ne suka kashe mini su, itama ta kuka da kanta wani zai rama mini abin da ta faɗa a kaina..”
Kamo hannunta ya yi ya zaunar da ita kusa da Aminatou, Aminatou ta ji ba daɗi ta kalli Salim ta ce “Da gaske 'yan bindiga suka kashe mata iyaye?”
“Tabbas haka ne su suka kai wa garinsu farmaki. Labarin komai ya faɗa mata.”
Sosai ta tausayawa Andizo ta kalle ta ta ce “Ki yi haƙuri Khadija ki dinga musu addu'a Allah ya musu rahama, in sha Allah hakan ba za ta sake faruwa ba..”
Jinjina kai ta yi ta ce “To na yafe muku.”
“Yawwa ƙanwata na gode ya jikin naki yanzu akwai zazzabin?” Ta faɗa tana taɓa gefen wuyanta, har yanzu akwai zafi ta kalli Salim ta ce “Ko mu kai ta asibiti ne?”
“Nima dai haka nake tunani amma mu bari zuwa gobe in bai sauka ba sai na kaita..”
“To shi kenan Allah ya ba ta lafiya bari ni in tafi na kwanta sai da safen ku..”
Tashi ya yi ya raka ta suka shiga har ɗakin bacci, har za ta kwanta ya ce ta yo alwala tukun ta kwanta. Bayan ta fito ta zauna ta yi addu'ar kwanciya bacci ta kwanta ya lulluɓe ta tare da kissing ɗin goshinta sannan ya fito..
A ɗaki ya samu Andizo za ta kabbara Sallah ya kalle ta cike da birgewa ya ce “Matar tsaya na yo alwala nima mu yi Sallar tare..”
To ta ce mishi ta zauna a baki gado, bayan ya fito suka yi Sallar shafa'i da wutiri sannan suka bi lafiyar gado.
Yau yadda ya zo mata da wani sabon salon ƙauna sai ta samu damar ba shi goyan baya ɗari bisa ɗari, sosai hakan ya faranta masa rai ganin yadda ta saki jiki da shi ba kuka ba rakin da ta saba mishi in hakan ta haɗo su, itama a nata ɓangaren ta ji yau ba ta wahala ba kamar kodayaushe sai zuciyarta ta yi sanyi, wani abu take ji game da mijin nata wanda ba ta san ya za ta musalta shi ba kawai sai ta shige jikinsa. Kyakkyawar tarba ya mata yana murmushi ya ce “Yau dai a jarumta aka zo.”
Duka ta kai mishi ya riƙe hannun yana dariya itama tana yi, ganin za ta yi bacci ya ɗauke ta suka yi wanka sannan suka koma bacci..