← Book details Andizo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 75

Sashe 66

Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ƙarfe ɗaya daidai jirginsu ya sauka a airport ɗin Abuja, kallon yadda take fitar da numfashi tana zuƙowa yake, a hankali ya fara hura mata iska a kunne ta yi saurin buɗe ido tana kallon waje ta taga. Ji ta yi an miƙar da ita ba ta ce komai ba sai ma saki jiki da ta yi jin ta a jikinsa, ganin yana shirin fita da ita haka ta yi saurin faɗin “Daddyn Farrah ka sauke ni a nan mana zan fita da kaina.”
Dariya ya yi yana sauke ta kalle ta sai sunne kai take yi, mayafin ya gyara mata ya riƙe handbag suka nufi kofar fitowa. Tun kafin su ƙarasa saukowa ta hango wasu manyan mata su uku masu kama da shi sak kamar an tsaga kara, kowacce ta sha material tsadadde na gani na faɗa, kallon su ta sake yi sai ta ji jikinta ya yi sanyi, abin da take tunani a kan Sultan ya tabbata lalle ya fi ƙarfin ta, ita ɗin ba ta kai ta zama matarsa ba tana ɗiyar talakawa shi kuwa duk Africa ba wanda bai san shi ba a harkar kwallo. Taɓa ta ya yi ta ɗago kai ta kalle shi da sauri, fuska ɗauke da damuwa ya ce “Me kike tunani Wife? Tun ɗazu nake magana ba ki ji ba.”
Ajiyar zuciya ta sauke ta sake kallon mata ta ga suna mata murmushi si ta ji zuciyarta ta ɗan samu nutsuwa, a hankali ta miƙa masa hannunta ya kama suk ƙaraso wajen su.
“Welcome to Nigeria Khadija.” Cewar ƙaramar cikin su wadda tafi tsananin kama da Sultan. Sunkuyar da kai ta yi murya ƙasa ta ce “Thank you Anty.”
Dariya matar ta yi ta rungumi Sultan tana faɗin “Yaya ka faɗa wa matar nan taka mu fa ba ma son kunyar nan da take sunkuyar da kai, mu ƙannenka ne ba yayu ba ka sanar da ita ta saki jikinta Mom ta ƙagara ka kai mata ɗiyarta.”
Kuncin Andizo ya shafo ta yi murmushi mamaki fal ranta wai yanzu wannan manyan matan masu aji da class duk ƙannen mijinta ne? Ajiyar zuciya ta kuma saukewa ta saki fuska tana murmushi ta isa gaban sauran suka rungume ta, ɗaya ta ce “Ina miki murna da samun Yaya J a matsayin miji Allah ya ba ku zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba.”
A kunyace ta ce “Amin ya Rabbi.”
Daɗi sosai ya rufe Sultan ganin Andizo ta saki jiki da 'yan'uwansa, mota suka shiga aka nufi gidan Mom.
G R. A. Suka iso jikin wani babban get motar ta yi hon aka buɗe musu suka shiga, da sauri ɗaya daga cikin masu tsaron shi ya iso ya buɗe musu ƙofa, matan suka fara fitowa sannan shima ya fito ya zagaya ya buɗe mata ƙofa ta fito a kunyace. Ba ta lura da Mom ba sai da suka kusa isowa daf da ita ta ji saukar sautin muryarta.
“Barka da zuwa ɗiyata.”
Da sauri ta ɗago kai suka haɗa ido da Mom, fisge hannunta ta yi daga na Sultan ta nufi Mom ta sauri itama ta taro ta suka rungume juna, tafi suak sa Sultan ya kalli Mom ya ce “Yanzu abin ya zama na son kai ashe, an yasar da ni an kin ga ƴarki.”
Daƙuwa Mom ta mishi tana dariya ta ce “To dama wa kake tunanin zan tara? Ai 'yata na taro ba kai ba matsa ka ba mu guri mu wuce ciki.”
Dariya ya yi ya matsa Mom ta kamo hannun Andizo suka wuce ciki, wani tantsameman palo na alfarma suka shigo, faɗin tsaruwar palon ma ba ta lokaci ne, kujerun palon kansu abin kallo ne can gefe wani harɗaɗɗan dinner table ne babba Mai ɗauke da kujeru goma shabiyu, idan ka shigo da palon da photon Sultan za ka fara cin karo wanda aka manne a jikin bango, yana sanye da kayan bal hannnunsa riƙe da kofi ya ɗaga shi sama ya yi murmushi aka yi photon, ɗaya gefen na photon shi kuma dukkansu family ne har da mahaifina, can gaba kaɗan photon Farrah ne ita da shi ya goya ta suna dariya aka yi photon..

Sama aka haura da ita cikin wani ɗaki, zaunar da ita ta yi ta ce “Matar Yaya nan ne ɗakinsa ki yi wanka ki sauko mu ci abinci sai ku kwanta ku huta.”
Murmushi ta sakar mata ta ce “Don Allah ya sunanki?”
Har ta juya ta dawo ta zauna ta ce “Ni sunana doctor Rahama ni nake biyawa Sultan, sai ƙanwata wannan wadda ta fimu girman sunan ta Barrister Safna, sai Autarmu doctor Sultana.”
Waro ido ta yi tana yar dariya ta ce “To gaskiya ni Antys zan ke kiran ku tun da kun fini shekaru.” Ta faɗa tana yaye mayafin jikinta.
“Tab rufa mana asiri, so kike Yaya ya ce mun raina masa mata? Ki kira mu da sunan mu.”
Ɓata rai ta yi ta ce “Lalle ma, to ni kam gaskiya ba zan iya kiran ku da sunanku ba, ko ba komai ai kun girme ni naisa ba kusa ba zan dinga kiran ku da doctor's ita kuma Barrister ya yi ko?”
Kumatunta ta shafo ta ce “Yawwa beautiful ɗin Yaya hakan ya yi tun da kin ce ba za ki kira mu da sunanmu ba, bari na wuce kar ki yi wanka ki fito mu ci abinci.”
To ta ce tana kallon ta cike da birgewa ganin yadda ta saki jiki da ita kamar dama can sun taɓa zama da ita, tashi ta yi ta je ta kulle ƙofar ta dawo ta cire kaya ta nufi ƙofar da ta gani a cikin ɗakin. Tana buɗewa maimakon ta ga toilet sai ta ga saɓanin haka, wani babban ɗaki ne babu komai a ciki sai kayan motsa jiki kala-kala, riƙe baki ta yi ta mayar ta rufe ta rasa duba ko'ina amma ba ta ga wata ƙofar ba, buɗe handbag ta yi ta ɗauko waya ta lalibo number shi ta danna masa kira.
Yana ɗauka ta ce “Wanka nake son yi ka zo.”
Miƙewa ya yi tsaye ya ce “OK gani nan zuwa.”
Kallon shi Doctor Sultana ta yi ta ce “Yaya ina kuma za ka je daga zuwan ku?”
Mayar da wayar ya yi aljihu ya ce “My Wife ta ce tana son yin wanka na je, da alama ta gaji matuƙa zan je na gani.”
Dariya ta yi ta ce “To masoya sai an fito.”
Hararar ta ya yi ya yi gaba suna tsokanar shi ya ce zai rama idan ya dawo.
Ƙofar ya burda ya ji ta a kulle sai ya kwankwasa, da sauri ta tashi ta leƙa ta wata ƙaramar ƙofa da ke jikin ƙofar ta ga shi ne, buɗe mishi ta yi ta matsa ya shiga ta rufe ta kuyo da nufin mishi magana sai ji ta yi ya yi sama da ita yana juyi a tsakar ɗakin. Zaro ido ta yi ta ce “Sauke ni please hajijiya za ta kama ni yunwa fa nake ji.”
Saurin aje ta ya yi yana dariya ya kama zanin gadon da ta rufe jiki da shi ya yaye yana faɗin “Daga ni sai ke za kike rufe jiki.”
Make hannunsa ta yi tana turo baki gaba ta ce “Kai fa ba ka jin kunya.”
Dariya ya yi ya ce “Ai har yanzu ba ki ga rashin kunyata ba sai nan gaba, sai na mayar da ke kamar ni.”
Gum ta yi da bakinta ba ta kuma cewa komai ba, kayan jikinsa ya cire ya ɗauki towel ya sa idanuwanta a rufe, itama ɗauko mata ya yi ya fisge zanin gadon ya sa mata ya nufi wata ƙofa da ita.
Jin suna tafiya sai ta buɗe ido tana kallon wajen, sai da suka bar ɗakin kamar za su shiga wani bangare sannan ta ga ya buɗe wata ƙofa sai ga su a toilet. Wanka ya mata sannan shima ya yi suka yo alwala suka fito, bai tsaya ɓata musu lokaci ba shirya ta ya yi cikin wata riga da sket na shidda kamfala, sosai ta yi mamakin ganin kaya a jere tun daga sama har ƙasa kaya ne kala-kala ba mace da na namiji, tunani ta yi ƙila ko na maman Farrah ne sai kawai ta tsaya turus tana kallon shi. Kallon ta ya yi da alamun tambaya ta juya mishi baya tana kumbura baki, ta ya ma zai sa mata kayan matarsa da ta mutu? Dafa ta ya yi ya ce “My wife Mom fa na jiran mu ki zo mu fita kar ta dinga kira, yanzu ta kira ta ce na sauko da ke ki ci abinci kar na bari ki yi bacci.”
Kamar za ta fashe da kuka ta juyo ta kalle shi a hankali ta nuna mishi kayan jikinta ta ce “To amma wannan ɗin kayan waye ka ba ni na saka?”
Shuru ya yi yana jinjina lamarin ta, shi ya sa ta yi kicin-kicin da fuska dan ta ga kayan mace a jikin wardrobe ɗinsa? Hannunta ya ruƙo ya ce “Ki daina tunanin kowacce mace a cikin rayuwata in ba ke ba my wife, wannan ba kayan kowa ba ne naki ne wanda nake saya ina ajewa.”
Ji ta yi zuciyarta ta samu nutsuwa ta saki fuska ya kalle ta cikin tsona ya ce “Wannan matar tawa akwai kishi.”
Murguɗa mishi baki ta yi, darduma ya shinfiɗa suka gabatar da Sallar da ke kansu sannan suka fita..
Chapter 66 · 0% Book details