Sashe 2
Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
To ya ce da sauri ya shige ɗakin. Yana shiga ya zauna a kusa da shi a sanyaye ya ce “Ka kwantar hankalinka Yaya in sha Allah za a same ta.”
Runtse idanu ya yi yana jin zuciyarsa na masa ƙuna, da kyar ya iya cewa “Zan je na nemo ta da kaina.”
To Ahmad ya ce yana ƙara kwantar masa da hankali tare da tabbatar masa za a ganta. Sai da aka ba su dama duk suka shigo ɗaya bayan ɗaya, lokacin da Aminatou ta shigo kuka ta dinga yi tana jero Allah ya isa ga waɗanda suka sace Andizo, da kanta ta taimaka masa ya tashi ya zauna ta dube shi tana share hawaye ta ce “Mijina ka daina tayar da hankalinka, nasan ma kafin a ba ka sallama za a ganta. Ni kaina hankalina ya kasa kwanciya a kan sace mana amarya da aka yi, amma ba komai ko ma waye Allah zai tona masa asiri. Yanzu ka daina wannan surutan kar hankalin su Mamma ya tashi a ɗauka ko ka zare ne, kai fa jarumi ne sojana ka nuna jarumta mana.” Ta faɗa tana jan kincinsa.
Dogon numfashi ya ja yana jin sassauci ganin yadda Aminatou ta nuna damuwar ta a kan lamarin, albarka yasa mata ta amsa da amin tukun aka masa allurar bacci ko zai samu hutu..
Sai da ta tabbatar ya yi bacci ta fito ta samu su Mamma ta ce “An masa allurar bacci yanzu haka bacci yake, amma don Allah Mamma ki ba da cigiyar ta a ko'ina ko ya samu nutsuwa, babu abin da yake faɗa sai sunan Khadija..” Ta faɗa tana hararar Ahmad ta kasan idanu, sosai kishi ya turniƙe mata zuciya kawai ƙarfin hali take, wata muguwar tsanar Andizo ta ƙara samun gurbi a zuciyarta..
Tashi Ahmad ya yi ya dube su ya ce “To ku tafi gida ni zan tsaya a wajen shi in ya so gobe sai a kawo mana abinci.”
Ba dan sun so ba suka tafi dan har Mamma ta ce ya bar Aminatou ta zauna amma ya ce sam ba za ta zauna ba ta koma gida kawai, hakan ya ƙara ƙular da ita ta wuce fu ta shiga motarta..
Kiran wayar Sabrin ta yi sai hura hanci take, tana ɗauka ta soma faɗa a kan abin da Ahmad ya mata. Shuru Sabrin ta yi har sai da ta kai aya sannan ta ce “To kenan shi kuma ta nan ya ɓillo? To ki bari shima za mu yi maganin shi, na fa lura in ba ki tashi tsaye ba wannan kucakar ta shigo gidan za ta kwace miki fada. Shi ya sa na ce miki a kashe ta amma kika ce gara a mata kurciya ta shiga duniya, yanzu ga shi ba ki rabu da baƙin cikin ta ba tun da mijinki yana magana.”
Kwafa ta yi tana danna hon da ƙarfi, a kiɗime Maigadi ya fito daga banɗaki ya buɗe mata kofa, sosai mamaki ya kama shi ganin Aminatou ce mai wannan abin. Tana fitowa ta fice ciki suna ci gaba da tattaunawa da Sabrin har ta shigo palo, zama ta yi ta ƙure AC saboda ta haɗa zuba kamar wacce ta yi gudu a sahara lokacin zafi, ƙarshe ta tashi ta shige ɗaki tana ƙara jinjina kalar rashin mutumcin da za ta yi wa Ahmad da Khadija ko ta samu sassauci..
_NIGERIA_
Yau Monday hakan ya sa tun safe Andizo ba ta ga gilmawar Sultan ba, ta takure a waje ɗaya ga ɗakin ba shi da haske sosai, kuka ta ci ta ƙoshi sannan ta yi shuru ta ɗaga hannaye sama ta ce “Ya Allah ka kawo mini ɗauki na koma gida kar ka ba wa wannan mugun dama ya cutar da ni, nasan yanzu haka suna can ana cigiya ta ni kuwa gani a wata ƙasar.”
Haɗa kai da gwiwa ta yi ta yi shuru tana tuna yadda take gudanar da rayuwarta cikin jin daɗi kafin a kawo ta wannan waje da ta yi wa laƙabi da baƙin ɗaki..
Kamar daga sama ta ji kiran Sallah ta zabura tana kallon ko'ina na ɗakin, yawo ta dinga yi har ta zo saitin taga inda ta nan ne kiran sallar ke zuwar mata, dafa ƙirji ta yi tana murmushi ta miƙa hannu ta buɗe taga dan ta ƙara jin sautin kiran Sallar. Kai ta miƙa sai dai ta ga daga bayar an kange tagar da karafuna, da sauri ta iso jikin kujera ta dinga turawa har ta kai bakin tagar, haka ta hau ta leƙa waje ai ba shiri ta yo baya ganin wasu manyan-manyan garada a farfajiyar gidan suna tsaye, dafe ƙirji ta yi tana zare idanu ta ce, “Ƙudun uban can! Yo wannan duk ƙauyenmu babu babba kamar irin su.”
Shuru ta yi tana tunani can ta tashi tsaye ta kuma leƙawa, riƙe baki ta yi ganin yadda ta yi naisa sosai da ƙasa ta yi ƙuri tana kallon su wasu na kai-kawo wasu kuma suna nan tsaye kamar sojoji. Ƙaran motar da ta ji ta kallon bakin get tana son ganin wanda zai shigo, baƙar mota ce sabuwa dal ta sanyo kai ciki Maigadi sai gaishe da na ciki yake, Andizo ta taɓe baki ta ce “Tab ji wata lukutar masifar, ana gaishe da mutum amma ko ya tsaya ya amsa, ashe da gaske abin da muke gani a télévision yana faruwa a zahiri.” Ta faɗa tana kurawa motar idanu..
Wata hamshaƙiyar mata ce ta fito daga cikin motar, Sultan ma ya fito daga ɗayan gefen ya sha wankan ƙanana kaya sai wani shan ƙamshi yake, Andizo ta saki baki tana faɗin “Ji ɗan wahala kamar na Allah, ita wannan ɗin ko wace ce ita? Ƙila ma matarsa ce mugun.” Ta faɗa tana gyara zama.
Tun da ya fito daga mota yana ɗaga kai sama ya hango an buɗe tagar ɗakin da Andizo take, sosai ya yi mamakin hakan amma a fili bai nuna ba ya zagayo ya kama hannun matar suka yi ciki, Andizo na kallon su har suka shige sannan ta janye kanta ta ci gaba da zama a nan.
Zaman da ta yi a haka iska na fifitawa sai ta ji damuwar da take ciki tana gushewa, lumshe idanu ta yi tana shaƙar iskar, ƙaran buɗe kofa ta ji amma ba ta ɗago ba bare ta ji tsoron ya zo ya same ta a haka..
Da fito ya shigo ya daddana wasu lambobi ya kulle Ƙofar, yana juyowa suka haɗa idanu ya tsaya yana kallon ta ganin ta a can sama jikin taga, bai ce mata komai ba ya zauna a bakin gado sai ga mai kawo abinci ta shigo hannayenta ɗauke da faranti, itama ta yi mamakin ganin Andizo ta ɗane taga, haka ta aje tana wani kwarkwarsa ta kalli Sultan da yake ta daddana waya.
“Sir food is ready.” Ta faɗa tana ɗan ranƙwafowa ƙirjinta duka rabi a waje, kanta dama ba ɗankwali sai kitson gashin doki da aka mata suka zubo har gadon bayan ta.
“OK thanks.” Iya abin da ya faɗa bai ɗago ba bare ma ya ga abin da take masa. Yadda ya share ta sai ranta ya ɓaci, yatsarta ta tsoma a cikin cup mai ɗauke da black tea ɗin da ta haɗa masa ta kwashi ƙara tana yarfa hannu. Sororo Andizo ta yi tana kallon ta duk abin da ta yi tana gani, jin ƙaran da ta yi ya yi saurin ɗagowa ya kalle ta, ganin kalar shigar da ta yi sai ya shagala da kallon ta abin da ya faranta mata rai..
Ita dai Dijan ku ta gargajiya na kallon Ikon Allah, ta kawar da kai tana faɗin “Itama ashe ƴar iska ce.”
Bai ankara ba ya ji ta ta faɗo jikinsa, a zaton shi Andizo ce ya sa hannu ya rungume ta, Andizo ta juyo ta ga sun manne da juna ta ɗaura hannu biyu a ka.
“Inna lillahi wa inna laihin raji'un! Ihu kwartaye za su yi iskanci, jama'a ku zo na kama su.” Ta faɗa da iya ƙarfin ta tana dirowa daga taga..
A ruɗe ya buɗe idanuwansa ya kalle ta, wani irin hankaɗa ta ya yi ta faɗi ƙasa tim nan take goshinta ya fashe sai jini, a zuciye ya zare bel ɗin jikinsa ya shiga lafta mata tana kurma ihu, Andizo ta sheƙe da dariya ta ce “Shegiya gobe ma kike zuwa kina ɗanewa jikin ƙato, babu abin da ya dame ni ya miki dukan mutuwa ni dai burina na bar gidan nan.”
Sai da ya ga ba ta motsi sannan ya rabu da ita ya, jikin bangon ɗakin ya isa ya matsa wani abu sai ga maza biyu sun shigo, nuna musu ita ya yo ya ce “Ku fitar da ita daga part dina sai na neme ta.”
To suka ce tare da ɗaukan ta suka fita waje, ba a jima ba wani matashin saurayi ya shigo ya gyara wajen da jini ya ɓata, kayan abincin ya nuna masa cikin bada umarni ya ce “A canza mana abinci.”
Jiki na rawa ya ɗauke abincin ya je ya kawo musu wani ya fita shi kuma mayar da code ɗin kofar ya rufe..