← Book details Andizo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 75

Sashe 48

Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kuka sosai ta ci da ta shiga ɗaki ta rasa me ya sa suka takura wa rayuwarta musamman ma shi Ahmad da duk wani motsi in ta yi sai ya samu abin da ya ce ta yi, jin ƙaran takun tafiyarsa ta yi saurin tashi ta sa wa kofar ɗakin makulli ta kulle. Banɗaki ta shiga ta gyara jikinta sannan ta fito, tana ji yana mata magana amma taƙi buɗe kofar, kan gado ta zauna ta buɗe jakar makarantar ta ta fito da takardu ta fara dubawa. Bayan ta gama ta buɗe za ta mayar sai ta ga wata leda fara mai kyau a ciki, da mamaki ta ɗauko ledar ta buɗe, zaro ido ta yi ganin sabuwar waya iPhone 15pro, juya wayar ta dinga yi tana mai nuna al'ajabin yadda aka yi waya ta zo cikin jakarta, buɗewa ta yi kalar wayar ya tafi ta imaninta pink color. Murmushi ta yi ta kunna har da layi a ciki Artel ta sake juya waya, sai ta jima tana dudduba cikin wayar abin da ya ba ta mamaki photunanta ne sun fi ɗari a ciki lokacin tana ƙarama, gyara zama ta yi ta sake duba wani photo da ta ga ba nata ba ne, Farrah ta gani da Sultan da ita ta yi tsai tana tuna yaushe suka yi wannan photon kuma? Ajiyar zuciya ta sauke tana ƙare wa photon kallon, in ta kalli Farrah sai ta kalli Sultan saboda yadda suke kama kamar ya yi kaki ya tofar, hannu ta kai ta shafa fuskar Farrah ta ce “Ma belle chérie.”
Lumshe ido ta yi tana jin wani matsanancin farin ciki na mamaye lungu da kusurwar zucyarta, ji ta yi duk wani haushin sa da take yana raguwa ta sake kallon photon, yadda ya yi mata wani kalar kallon love a photon har sai da ta yi tagumi tana faɗin “Marar kunya shi ko a photon ma sai ya nuna ko yaushe aka yi wannan photon?” Ta yi murmushi tana ƙare wa surar jikinsa kallo. Tabbas Sultan ya cika duk wani mataki da ake buƙata a miji, ga shi ɗan gayu mai ji da izza kamar jinin sarauta , ga kuɗi ga iya soyayya, ga kyau ga class Ko takun tafiyarsa abin kallo ne, dogo fari kyakkyawa zubin jaruman maza. Ɓata rai ta yi ta ce “Sai dai kuma ai ɗan iska ne ga shaye-shaye, wa ya sani ba ko mayaudari yan yaudarar 'yanmata da kyan da Allah ya ba shi da kuma kuɗi.” Ta sake kallon shi sai kuma ƙara da cewa “To duk da haka dai na ji daɗi da ya saya mini wayar nan tun da shi wancan mugun ya kwace tawa ya ƙi ba ni.”
Har ta gyara za ta kwanta ta ji shigowar saƙo ta yi saurin ɗaukan wayar ta shiga text message.

_“My wife ina fatan Kim buɗe wayar kuma kin ga kalar ta yi miki? Idan kuma ba ta birge ki ba gobe idan za ki tafi makaranta sai ki zo da ita ki faɗi kalar da kike do sai a sayo miki, I love you so much my darling. Please Idan kinga saƙona ki daure ki dawo mini da reply duk da nasan da wahala ki kula saƙon ma bare ki ba ni amsa, nasan ni mai lefi ne a gareki amma ki yi haƙuri ki yafe mini mu yi aure zan ba ki kulawa fiye da wadda kika samu a wajen Salim ina mai tabbatar miki, ke kanki kin san tsananin son da nake miki ne ya sa har na sato ki aka ɗaura mana aure a shekarun baya, ki daure ki ce kina so na ko da sau ɗaya ne Khadijata, yanzu haka Farrah na sanar mata da abin da yake tsakaninmu da ke ba ki ga yadda take murna ba har da kuka ta yi na farin cikin za ki zama matar mahaifinta..”_

Tagumi ta yi tana sake bin text ɗin tana ƙara karantawa, murmushi ta yi ta aje wayar tana jinjina son da ƙawarta ta take mata, tana ta tunane-tunane har bacci ya ɗauke ta..

Washegari ta shirya ta fito palo inda ta ga duk sun hallara ita suke jira ta gaishe da Mamma da Abba da Hajiya, hararar inda Ahmad yake ta yi suka gaisa da su Hassana, kasancewar tana kusa da shi ya miƙa ƙafa ya take mata 'yan yatsu. Da sauri ta kalle shi suka haɗa ido ya sakar mata da murmushin mugunta ya ƙara danna yatsun, ƙara ta sa jin wani mugun zafi har tsakiyar kanta. Hajiya ta kalle su ta ce “To kin fara ko gari ya waye? To kin ji da shi babu wanda zai kula ku tun da kun zama 'yan drama.”
Idanuwan Andizo ne ya ciko taf da hawaye amma ganin yana mata dariya ƙasa-ƙasa sai ta daure taƙi bai wa hawayen damar zubowa, ɗayar ƙafa ya kai ya sake murza yatsun ta kuma yin ƙara tana faɗin “Mamma ƙi masa magana zai karya mini yatsun ƙafa dan mugunta.” Ta faɗa tana sakin wani kalar kuka gwanin ban tausayi saboda zafin da yatsotsinta suke mata kamar ba a jikinta suke ba, ganin hawayen ta sai ya yi dariya ya janye ƙafafuwansa ta yi saurin ɗago ƙafar da kyar. Kuka ta sa tana faɗin “Mugu azzalumi sai Allah ya saka mini cuta ta da kake yi yi.”
Abba ya kalli Ahmad ya ce “Kai tashi ka ba mu guri kafin na saɓa maka, wacce irin mugunta ce haka za ka dinga take mata 'yan yatsu dan rashin imani?”
Daure fuska ya yi ya ce “Ƙarya ce fa take Abba babu wani take mata ƙafa da na yi, ita ce ma ta take mini tawa ƙafar Allah ya sa ina da takalmi ƙafa ciki.”
Da hannu ya nuna mishi hanya ya ce “Da wasu ne waɗanda ba 'yan gidan ba in la faɗa musu za su yarda ba mu da muke ganin artabon da kuke kamar za ku ga hanjin juna.”
Andizo ta ɗago ƙafar ta ce “Ƙarya ce yake Abba shi ne ya take min ƙafa da wannan takalmin nashi mai tauri, kalli ki ga har jini suke yatsun nawa.” Ta faɗa wasu hawayen na zubo mata.
Salati Hajiya Babba ta ɗauka tana taɓa ƙafar, a fusace ta kalli Ahmad da ya yi kitsin-kitsin da fuska ya tsare gida yana harare-harare ta ce “Anya kuwa Ahmadu za ka ga daidai a rayuwarka? Yanzu saboda Allah sai ka illata mata ƙafa dan kafi ƙarfinta? To Wallahisai na ci ubanka Musalle ga shi nan a zaune, ni za ka mayar tsohuwar banza? To bari Saddiƙu ya zo zan haɗa mata kayanta ta koma can ƙasar waje ta ci gaba da karatu tun da kai so kake ka kashe ta. Kai kuma Musalle idan ba ka yi masa kashedi ba a kanka zan fanshe duk iskancin da yake mini.”
Abba ya ɗan sunkuyar da kai ya ce “In sha Allahu zan mishi kashedi, ni kaina na yi tunanin ta koma wajen Saddiƙu saboda matarsa ta takura sai sun zo har su Hassana sun kawo musu ziyara, to na ce mata sai sun yi hutu da kaina zan kai su har can.”
Goge hannu Hajiya ta yi ta kama hannun Andizo ta ce “Ya dai fi maka dan Wallahi ba ƙaramin aikina ba ne na maka rashin mutumci a gidan nan matsawar bai daina cin zalin ta ba.”
To Abba ya ce ita kuma ta janyo Andizo suka dawo palo, tissue ta sa ta goge mata ƙafar sai sababi take tana zagin Ahmad ta sa mai aikin gidan ta ɗauko mata roof ta shafa mata ƙafa, godiya Andizo ta mata ta tashi ta wuce zuwa ècole.
A harabar gidan ta ganshi tsaye ta wuce tana ɗingisa ƙasar a hankali ta nufi hanyar fita, kallon ta ya yi ya juya ya koma ciki.

Tana fitowa sai ga su Amira sun iso yau ba muso ta shiga motar saboda yadda ƙafarta ke mata zugi, sunkuyar da kai ta yi ta ce “Good morning Daddy.”
Lumshe ido ya yi bai amsa gaisuwar ba sai ce mata ya yi “Daga yau na hana daddy ɗin nan ki kira ni da kowanni suna na masoya.”
Turo baki gaba ta yi ta ce “Yo to ba mahaifin ƙawata ba ne kai meye a ciki dan na ce maka daddy? Thank you na ga waya Allah ya ƙara arziƙi.”
Wani Sanyin daɗi ne ya ratsa zuciyar Sultan yadda ta sakar masa da murmushi mai ƙayatarwa ya san wayar ta birge ta, ajiyar zuciya sauke ya ce “Ai ni da ke babu godiya a tsakanin mu tun nine mijinki ma gobe in sha Allahu. Amma ba ki ga saƙona ba?”
Kawar da kai ta yi gefe tana kumbura baki ta ce “Na gani mana.”
Chapter 48 · 0% Book details