← Book details Andizo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 75

Sashe 34

Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da Salim ya yi kwana uku sannan ya farfaɗo, ranar har sun haƙura za su koma gida wata nurse ta fito ta tsayar da su duk suka dawo, kallon su ta yo ta ce “Ya farka yana kira wasu mutane amma dai za ku iya shiga..”
Su duka suka shiga ciki kowa so yake ya ganshi, zaune suka same shi ya jingina da gadon an tallabo kansa da pilo idanunsa a kan kofar yana murmushi, suna shigowa ya hango su ya lumshe idanu yana godiya ga Allah da ya ba shi ikon ganin su, sannu suka dinga mishi yana masawa.
Andizo ta zauna a kusa da shi ta riƙe hannnunsa tana faɗin “Alhamdu Lillah mun gode wa Allah da ya farkar da farin cikinmu.”
Kallon su yake yana murmushi a hankali ya ce “Nana Khadijana kenan ai na faɗa miki zan dawo in sha Allah, gashi kuma kin gani na dawo ɗin.” Ya faɗa yana kallon ɗayan gefen da Aminatou take zaune itama ta riƙe hannnunsa.
A hankali ya ce “Matar Salim ya yarana suke? Fatan dai duk ba ku ɗaga hankalinku ba kuka yi ta wahalar mini da yara ko? Dan nasan ita wannan rigimammiyar ko shakka babu ta sha kuka.”
Murmushin jin daɗi Aminatou ta yi ta ce “Kuka ai ya zama dole mijin Aminatou da Khadija, musamman ma ita ai ba a magana amma tun da ka tashi Alhamdu Lillah mun gode Allah.”
Jinjina kai ya yi Mamma ta kalle shi tana goge hawaye ya ce “Haba dai Mamma meye na kuka ba gashi na tashi ba? Ka da ki yi tunanin abin da ya faru shekeru goma ne zai sake faruwa yanzu, in sha Allah ba komai ba na so ma kike tuna wannan lokacin..”

Girgiza kai ta yi ta ce “Haba yarona ai ba zan taɓa manta wannan baƙar ranar ba mai ɗauke da baƙin dare, naji daɗi matuƙa da ka farka Allah ya ba ka lafiya.”

Amin ya ce yana kallon su Hassana suma ya ce su daina kuka suka ce to, Hajiya Babba ta ce “To yanzu ku tashi mu tafi gida dare ya yi sai mu dawo gobe tun da ga Ahmad nan da Abdoul suna tare da shi.”
Duk tashi suka yi amma Andizo ta ce ita sam ba ta san ba zancen tafiya gida, da suka takura mata ma kuka ta sa ta riƙe hannun Salim ta ce “Ni ba inda zan je muna nan ni da Adda za mu kula da shi ai.”

Ganin yadda ta kafe sai Aminatou ta ce “Khadija ki yi shuru ba wanda zai mayar da ke gida kin ji, ki zauna a nan ni zan tafi idan kika yi kwana biyu nima sai na zo na yi kwana biyu.”
Goge hawaye ta yi tana dariya ta ce “To Adda sai da safe.”
Kallon Salim Aminatou ta yi ya ɗaga mata gira ɗaya, juyowa ta yi ta ga duk sun fita Andizo ma ta shiga banɗaki, matsowa ta yi ta manna masa kiss a ƙoshi da kumatu ji take itama ta tsaya ɗin amma ta ɗaure saboda ganin yadda Andizo ke kuka gara ita ta zauna da farko.
Yadda ta tsura mishi ido sai da ya hura mata iska ta rufe tana dariya ta mike tsaye ta ce “To sai da safe ko.”
Hannu ya ɗaga mata ta fita da hanzari..

Tana fitowa Sallah ta yi ya kallon ta, bayan ta gama ta ɗaga hannu a bayyane take jero mishi addu'oʼi yana amsawa da amin har ta gama ta shafa, cire hijabin ta yi ta dawo ta zauna tana faɗin “Sannu mai hankali, yanzu ma kana jin ciwo ko?” Ta faɗa tana riƙe hannnunsa.

Girgiza mata kai ya yi ya dafe cikinta ya yi masa addu'a sannan ya ɗauke ya ce “To tashi ki je ɗayan gadon can ki kwanta na ga kin fara hamma.”
Babu muso ta tashi ta isa gadon ta hau ta kwanta ta yi facing ɗin Shi, ƴar dariya ya yi ganin yadda take kallon shi, itama dariyar ta yi zuciyarta na ƙara sanyi ta tashi ta haɗe yatsu ta masa alamar zuciya, ta nuna mishi yana cikin ranta tana sonshi sosai ba kaɗan ba.
Dariya ya yi shima ya nuna mata yana matuƙar ƙaunar ta ita da babyn da ke cikinta, alamar godiya ta mishi tana rufe ido.
Gyaran murya ya yi ya ce “Allah sauke ku lafiya Nana Khadija, ina so ki haifa mini yara dozin shida su yo kamar ki shida su yo kama da ni, zan sa sunan su Mama da su Hajiya Babba.”
Buɗe ido ta yi ta ce “Kai haba dozin kuma kamar wata kaza?”
Dariya yi ya ce “To ai ba yanzu ba, da ɗaiɗai za ki haifo mini su.”

“To Allah ya kaimu lokacin.” Amin ya ce daga nan ba ta sake cewa komai ba.
Ganin haka ya sa shima ya rufe ido ba dan yana jin bacci ba..

Sai da ya ji ta yi bacci ya buɗe ido yana kallon ta ba ba ko ƙiftawa har shi ma bacci ya ɗauke shi.

Kiran Sallah ne ya tayar da shi ya kalli gadon ta ya ga ba ta nan, can ya hango ta tana zaune tana jn carbi ya lumshe ido. An gama Salla sai ga Ahmad ya shigo suak gaisa ya dube shi ya ce “Ahmad Sallah nake son na yi, tun da dai kafata lafiya take riƙe ni na shiga banɗaki.”

“To shi kenan bari na kira likita ta cire maka wannan abin.”

Fita ya yi ya je ya zo likita ya cire mishi ƙarin ruwan da ake mishi, kama shi ya yi a hankali suka tafiya har suka shiga banɗaki, ruwan alwala ya diba mishi sannan ya fito waje. Ledar da ya zo da ita ya ɗauko ya fito da wando ya kai mishi, Andizo na zaune tana kallon su. Bayan ya gama ya fito ta shinfida mishi abin sallah ya zauna ya yi Sallah. Bayan ya gama likitan ya dawo ya mayar mishi da ƙarin ruwan, kallon Ahmad ya yi ya ce “Idan Abdoul ya zo ka ce mishi ya ba ka abin da na ba shi ya aje maka.”
To ya ce ya fita ya zo da kayan abinci ya haɗa mishi shayi mai kauri da soyayyan kwai da doya ya miƙa mishi, itama ya tura mata Kwandon kayan abincin ya ce “Matar yaya ki samu ki ci abinci.”

Godiya ta mishi ta ɗauki kamar yadda ta ga Salim yana ɗan ci, sai da ta dan ci mai yawa ta aje Salim ya kalle ta ya ce “Ba dai har kika ƙoshi ba ?”
Turo baki gaba ta yi ta ce “Ba zan iya ci ba na ƙoshi.”
Bai takura mata ba ya dan shima bai ci sosai ba ya aje. Yana gama ci ta ɗauko mishi ruwa ya wanke hannu Ahmad ya ba su waje ya fita ta zauna a kusa da shi, hannunta ya riƙe ya ce “Khadija kin san kuwa irin son da nake miki?”
Girgiza kai ta yi ta ce “Ni kuwa na sani sosai kamar yadda nake sonka.”
Murmushi ya yi ya lumshe ido ya ce “Alhamdu Lillah.”
Baki ya buɗe zai yi magana sai ta ga ya yi shuru yana kallon ta fuska ɗauke da murmushi, itama sai ta yi tagumi ta zuba mishi ido.

Zabura ta ga ya yi ta yi saurin riko shi tana faɗin “Subhanallahi lafiya dai?”
Girgiza mata kai ya yi ya ce “Khadija Allah ya muku albarka.”
Amin ta ce tana murza hannnunsa, salati ta ji yana yi yana sauke ajiyar ajiyar zuciya hakan ya sa ta zauna tana riƙe da hannnunsa, can dai ta ji shuru ta ɗago kai ta kalle shi ta ga yana kallon gefe, taɓa shi ta yi ta ce “Juyo mana.” Ta ji shuru ta taɓa shi ta ji bai motsa ba, a rude ta kwaɗa wa Ahmad kira sai ga shi ya shigo afijajan.

Nuna mishi ta yi ta ce “Na yi ta mishi magana ya yi shuru.” taɓa shi ya yi ya ji jikinsa ya saki, nan take jiri ya ɗauke shi kamar zai fadi ya daure ya kai hannu ya sa a saitin wiyanshi, idanuwansa ya rufe mishi ya fita da sauri yana ce mata bari na kira likita..

A tare suka dawo lokacin su su Abba sun ƙaraso suma suka shigo, auna shi ya yi da ya gama sai gani suka yi ya cire duk wata na'ura da ke jikinsa ya janye gefe ya ja zanin gadon ya rufe mishi fuska. Kallon shi suka yi suna tambayar me ke faruwa, girgiza kai ya yi ya ce “Ku yi haƙuri wanda ya fi mu son shi ya karɓi abinsa.”
Wani dum Andizo ta ji kunnenta ya yi kamar jinta ya ɗauke, kallon su kawai take sai ta ta ji Abba na faɗi “Inna lillahi wa inna laihin raji'un! Allah ya jiƙan ka Salim..”

Wani irin ƙara ta fasa ta yi lu za ta faɗi Mamma ta yi saurin taro ta ta sume a hannunta, itama Aminatou a jikin Hassana ta suma. Hankali tashi aka kira likita aka zo aka ɗauke su zuwa ɗakin taimakon gaggawa..

Gabaɗaya kuka suke sun rasa da wanne za su ji da mutuwar Salim ko da matansa da suka sume, gawar aka fito da ita aka sa ta mota har za su tafi su bar su Hassana su kula da su Andizo sai ga Aminatou ta fito a firgice, riƙe ta suka yi ta dinga rusa kuka tana faɗin “Ina mijina yake? Don Allah karku ce mini ya mutu waiyo Allah na gode maka, ina Khadija takeda?”
Da kyar suka rarrashe ta suka sa ta a mota kamar haɗin baki itama Andizo ta farka ta tsige ƙarin ruwan da ake mata ta fito. Kamo ta Hajiya Babba ta yi ta sa ta mota suka nufi gida..
Chapter 34 · 0% Book details