Sashe 36
Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ahmad ya shigo fito shi da Mamma suka taro su, a palo suka zauna aka kawo musu ruwa da lemo suka sha, Mom ta gaishe su tare da musu gaisuwa sannan ta ce “Ina Khadija da abokiyar zaman nata?”
Hajiya Babba ta sa aka kira su, ba ta lura da su ba dan ba ta san za su zo ba shi ya sa ko kallon wajen ba ta yi ba kanta a ƙasa, sai da ta iso kusa da su Farrah ta miƙe hawaye sun cika mata ido ganin yadda ta rame ga cikin ya kere ta yanzu sun shiga watan haihuwa, a hankali ta kama hannunta ta ce “Khadija.”
Saurin juyowa ta yi suka haɗa ido, da hanzari ta iso gaban Mom ta kama hannunta ta ce “Mom kece nake gani da Farrah ko gizo ne kuke mini irin na mai hankali?”
“Ba gizo ba ne Khadija ni ce da Farrah muka zo miki ta'aziyya, ba mu san Salim ya rasu ba sai yau da asuba na kira Maigari muam gaisawa y sanar da ni, shi ne na sa aka cira mana ticket muka ci sa'a jirgin safe ya ɗauko mu, sannu kin ji Khadija Allah ya jiƙan Salim da rahama, ku kuma Allah y ba ku haƙurin rashin shi.”
“Amin Mom Allah ya saka da alheri na gode sosai, kina da kirki Mom kin ɗauke ni kamar Farrah duk wani abin da ya shafe ni sai kin shiga ciki, Allah ya bar zumunci..” Ta faɗa tana zama kusan Farrah
“Babu komai Khadija ga Farrah nan an musu hutu ta ce za ta taya ki zama har sai kin haihu.”
Guntun murmushi Andizo ta yi ta ce “Ke ɗin ƙawar kwarai ce Farrah Allah ya barmu tare, kuma ko ba komai kin sa naji farin cikin da rabona da shi tun ranar da zai rasu.”
Murmushi Farrah ta yi ta kama ta suka koma ciki.
Mom ta musu Sallama ta tafi suka mata rakiya har bakin mota suna mata godiya.
Ƙarfe biyar daidai na asuba Aminatou ta tashi da naƙuda, hankali a tashe Farrah ta fita ta buga wa Mamma kofa, dama ba bacci take ba kwanakin nan saboda halin da su Andizo ke ciki. Da sauri ta zura Hijabi ta fito ganin Farrah ya sa ta nufi ɗakin da hanzari, hankali tashe ta kama ta suka fito palo ta je ta bugawa hajiya babba kofa ta fito. Mota suka fito da ita Hassana ta ja su zuwa asibiti, suna isa aka amshe suka, shigar da ita ɗakin haihuwa.
Suna nan tsaye har Ahmad ya zo ɗaya daga cikin likitocin ta fito da baby tana murmushi ta ce “Alhamdu Lillah ta sauka lafiya ga ƴarta mace ta haifa.”
Mamma ta amshi Jaririyar tana kallon ta sak Salim, miƙa wa Ahmad ta yi ya amsa ya zauna yana kallon ɗiyar ba ko kiftawa. Sai da aka gyara ta tukun su Ummi suka iso asibitin kowa sai ɗaukan Jaririyar yake ana ta murnar game da lahini. Ita kanta Aminatou da ta ga jaririyarta sai da ta yi kuka sosai, da aka yi Sallar Azuhar aka sallamo su suka yo gida, Ummi ta so su tafi gida amma Mamma ta ce sam ta bari ta ƙarasa ladan ta, ba yadda ta iya ta haƙura suka nufi gidan..
Andizo da ga ta yarinyar ta ɗauka tana kallon ta ta kalli Aminatou tana murmushi ta ce “Dama na faɗa miki za ki haifo mini takwara to G shi dai addu'ata ta karbu dan haka a cika alƙawari..”
Murmushi ta yi ta ce “, Ai ba zan manta ba Khadija tun a asibiti Ahmad ya rada mata suna da Nana Khadija kin samu takwara.”
Zama ta yi ta murmushi hawaye suak cika mata kwarmin ido ta ce “Na gode Adda haƙiƙa ke abokiyar zama ce ta gari, kin kasance mace mai kirki mai son abin da mijinta yake so, Allah ya saka da alheri da wannan takwarar ta kika mini naji daɗi sosai ba zan taɓa manta halakcin ki a gareni ba..”
Murmushi Aminatou ta yi ta ce “Karki damu Khadija ai ke kika fi dacewa da a kira ki da abokiyar zama ta gari, tun da nake da ke ba ki taɓa nuna mini kishi ba a duk wasu lamuran mu, kin sha sadaukar mini da kwananki yayin da ba ni da lafiya, kin sha min wa'azi da dora ni kan hanya madaidaiciya, duk da a lokacin kina, yarinya ƙarama amma duk wasu ɗabi'unki na manyan mutane ne, dan haka karki ji komai zan miki abin da ya fi haka ma in dai ina raye a duniyar nan.” Ta ƙarashe maganar tana dafa ta..
Kallon su su Ummi suka yi suna yaba hali irin nasu, sai da ta ji bacci na ɗaukan ta ta ba da ɗiyar ta tafi ta kwanta.
Jaririya na ta kuka aka ce Aminatou ta shayar da ita ta amshe ta, aka nun Mata yadda za ta yi ta rungume ta doam shayar da ita.
Kwana biyu har ruwan nono ya zo kamar almara ya ɗauke, ranar jaririyar ta wuni tana kuka sai madara aka ba ta ta sha.
Washegri ranar itama ta tashi da daƙuda, kafin ma a yi ƙoƙarin kaita asibiti daga za tw yi fitsari sai jin kuka suak yi a banɗaki, da sauri Ummi ta shiga ta ta haihu, janye babyn ta yi ganin tana wata naƙudar ta kalli Mamma ta ce “Ta saura fa.”
Kamar minti goma ta sake haifo namiji, murna a gidan ba a magana aka gyara ta ita da yaran suka kaita asibiti aka duba ta duka ce ba matsalar komai..
Yaran da aka zo rada musu suna Andizo ta ce namijin a sa mishi sunan mahaifin Aminatou macen kuma a sa sunan Mamma, hka kuwa Ahmad ya sa rada musu suna. Ranar Aminatou ta dinga wa Andizo godiya ta ce ba komai ai za ta mata fiye da haka ma..
Washegari da kukan ɗiyar Aminatou ya yi yawa Andizo ta tashi ta ɗauke ta ta soma shayar da ita, tuni ta kama tana sha Aminatou ta yi tagumi tana kallon ta, ta rasa da wani irin alkhairi za ta saka wa Andizo, su kansu su Mamma sun ji daɗin abin da ta yi bayan ta gama shayar da ita yarinyar ta yi bacci har da dogon numfashi take ja..
Hajja ta ce tun da har ta sha nonon Andizo ita za ta ci gaba da shayar da su duka ukun, Ummi ta ce da an ba ta madara Andizo ta sa kuka ta ce“Haba Ummi ina nan a raye za a ba wa takwara ta madara? Ki barni na, shayar da su ai duka yarana ne.”
Albarka ta dinga sa mata tana amsawa da amin..
_Maman Nusaiba ce_
[6/14, 1:31 AM] Ummu Amjad: _*AREWABOOKS@SARATALKASUM88*_
35
Taron suna aka haɗa shi rana ɗaya tun da kwana biyu ne tsakanin su, hakan ya sa aka shirya walima duk da wannan haihuwa ta zo musu a baibaiye ne, sosai Salim ya ci buri a kan wannan haihuwar sai ga shi an yi haihuwa shi kuma ba ya duniyar..
Ana gobe suna 'yan ƙauye suka diro Niamey har da su Salame su Hajaru duk wasu ƙawayen da suka yi wasa tare Andizo cewa ta yi kowa ba ta ɗauke mishi ba sai ya zo wajen bikin yaranta za ta biya masa kuɗin mota da suturar da za su suka kala bibiyu, sosai hakan ya yi wa ƙawayen nata daɗi kowacce ta sha wanka aka turo mota huɗu ta zo har kofar Maigari aka kwashe su.
Su Salame sai ƙauyenci ake nunawa har da shafa bangon ɗakin Andizo ta ce “Jakka uban nan! Yanzu Andizo a nan kike rayuwa? Kai mutuwa mai yankan ƙauna Allah ya jiƙan Salim ɗan gayu mai fara'a.”
Fara'ar kan fuskar Andizo ce ta rage ta yi ƙasa da kai tana amsawa da amin tana kallon yaran nata musamman ma namiji tafi ganin kamannin shi da Salim, tana gama shayar da su ta miƙa wa Inna aka kwantar da su a kan gadonsu mai kyau, nan ma Salame ta ce “Kenan yara ma suna da gado kamar na manya?”
Wannan karon dariya ta ba wa Andizo ta yi murmushi ta ce “Salame kenan, ke komai kika gani sai kin yi magana? Ni kuwa ina jikar Iya take? Ko Iyar ta hana ta zuwa?”
Gyara zama Salame ta yi tana dariya ta ce “Gaskiya na yarda yanzu Andizo kin soma manta mutane, jikar Iyar da ga ta nan a gefen ki amma kike tambayar ina take.”
Saurin kallon gefen ta ta yi jiyar Iya ta yi dariya ta sha kwalliya bakin nan sai maiko yake, dariya Andizo ta yi ta ce “Alƙur'an kin haɗu jikar Iya mai koko da ƙosai.”
Su duka suka sa dariya Farrah ta riƙe ƙugu tana kallon su, turo baki ta yi ta ce “Khadija shi ne dan kin ga ƙawayenki kika manta da ni ko? To bari na tafi wajen Anty Aminatou wajen ta zan kwana.”
Fuskar tausayi Andizo ta yi ta ce “Haba my friend am so sorry kin ji.”
Juyawa ta yi tana faɗin “To bari dai ina zuwa dama Daddy ya ce zai miki barka zan kira shi ku gaisa.
To kawai Andizo ta ce tana kallon ta har ta bar ɗakin.
Hajaru ta kalli kofar ɗaki ta ce “Andizo wannan kamar dai na santa a wani waje.”
“Wai ba ki gane ta ba? Farrah ce fa ƙawata da na yi lokacin da aka sace ni mamanta ta ceci rayuwata.”
“Haba ni fa kamar na santa ashe ita ce har ta girma haka, Allah mai iko.”
Suna ta hira sai ga wata daga cikin dangin Aminatou ta shigo ɗakin da sallama hannunta riƙe baby tana ta kuka, amsa mata suka yi ta iso tsaya ta miƙa wa Andizo ta ce “Ɗiyar albarka kinga yarinyar nan taki kuka take yi ko yunwa ce take damunta”
Bakin gado ta matso ta amshi shi tana murmushi ta ce “Allah sarki yarinyata ai dole ta ji yunwa, rabon da na shayar da ita fa tun da La'asar ai ta yi ƙoƙari ma.” Ta rungume shi ta soma shayar da shi.
Murmushi matar ta yi ta ce “Bari to na zauna ta gama sha sai na koma da ita ko?”